BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Wace ce Stormy Daniels - matar da ta zame wa Trump karfen-kafa?

Ana zargin Trump da biyan Stormy kudi kafin zaben 2016 don rufe bakinta

Fri, 31 Mar 2023 Source: BBC

Kotu a birnin New York na Amurka ta samu tsohon shugaban ƙasar Donald Trump da laifi a zargin da ake masa na biyan kuɗi domin ɓoye alaƙar da ke tsakaninsa da wata ƴar fim ɗin batsa.

Ana zargin Trump ne da biyan matar mai suna Stormy Daniels kuɗi gabanin zaɓen 2016 domin ta rufe bakinta kan alaƙar da ta wanzu tsakaninsu.

Ita dai Stormy Daniels ta ce sun samu alaƙa ta lalata tsakaninta da Trump a 2006, shekar ɗaya bayan ya auri mai dakinsa Melania Trump.

Kuma hakan ya faru ne kimanin shekaru 10 kafin Donald Trump wanda ɗan kasuwa ne ya hau kan shugabancin Amurka.

Trump dai ya musanta zarge-zargen da ake yi masa, kuma ya ce an biya ta kuɗi ne domin hana ta yi masa ƙazafi da nufin tatsar kuɗi daga gare shi.

Wace ce Stormy?

Sunan Stormy Daniels na ainahi shi ne Stephanie Clifford. Tana da shekara 44 a duniya, kuma ta fito ne daga birnin Baton Rouge na jihar Louisiana da ke ƙasar Amurka.

Daniels ta shahara a tsawon kimanin shekara 20, saboda sana’arta ta fina-finan baɗala.

Takan taka rawa a wasu fina-finan, sannan ta bayar da umurni a wasu.

Ta ce an haɗa ta da Trump ne a watan Yulin 2006 a lokacin wata gasar kwallon sanda ta golf.

A ranar 28 ga watan Oktoban 2016, jim kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa da Trump ya yi nasara, Daniels ta sanya hannu kan wata yarjejeniyar cewa za ta yi gum da bakinta game da alaƙar da ta wanzu tsakaninta da Donald Trump.

Inda aka biya ta kuɗi dalar Amurka 130,000, kamar yadda takardun da aka gabatar wa kotu suka nuna.

Lauyan Stormy a wancan lokacin, Keith Davidson da lauyan Trump, Michael Cohen ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

Akwai wurin da aka ware a jikin takardar inda Trump zai sanya hannu, sai dai bai sa hannun ba.

Yadda rikicin ya fara

A 2018 ne Stormy Daniels ta shigar da ƙara tana zargin Donald Trump da laifin ɓata mata suna bayan ya sanya wani bayani a shafinsa na tuwita, inda ya zarge ta da damfara saboda ta ce ana mata barazana game da yiwuwar za ta fallasa aikin baɗala da ya faru tsakaninta da shi.

Daga baya kotu ta wanke Trump, inda ta ce kalaman Trump a kan Daniels ba na ɓata suna ba ne, kuma sun yi daidai da tanadin kundin tsarin mulkin ƙasar na faɗin albarkacin baki.

Daniels ta ce wani mutum ne ya tunkare ta lokacin da take tare da ɗiyarta a wurin ajiye motoci a Las Vegas, cikin shekarar 2011, inda ya yi mata barzana, bayan da ta amince za ta bayyana alaƙarta da Trump a wata tattaunawa ta talabijin.

Source: BBC