BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Wace nasara shugabannin Afirka suka cimma a ziyarar sasanta Ukraine da Rasha?

Shugaban Rasha, Vladimir Putin da ta Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa

Wed, 21 Jun 2023 Source: BBC

Shugaban kasar Afirka ta kudu Cyril Ramaphosa ya sha yabo bayan da ya jagoranci ayarin shugabannin kasashen Afirka a wata ziyara mai cike da tarihi da shugabannin suka gudanar a makon jiya a kasashen Ukraine da Rasha.

Ziyarar ita ce irinta ta farko da shugabannin Afrika suka shirya a wajen nahiyar da nufin shiga tsakani don yayyafa ruwa a wutar yakin da ake gwabzawa tsakanin kasashen Rasha da Ukraine.

Sai dai, duk da bijirewar da aka samu na kin amincewar bangarorin wadanda ba su jituwa su hau teburn sulhu, shin ko ziyarar ta yi wani tasiri, ko kuma wani yunkuri ne kawai da Ramaphosa ya yi na neman jan hankalin kasashen duniya, a yayin da kasar Afrika ta kudun ke fama da tarin matsaloli?

Tawagar daga Afrika wadda ta kunshi shugabanni da wakilai daga kasashe bakwai sun gana da shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky da na Rasha Vladimir Putin a karshen makon jiya.

Ana fatan ziyarar, wadda shugaba Ramaphosa ya jagoranta, za ta taka rawa wajen kawo karshen yakin, wanda ya yi mummunnan tasiri ga yanayin rayuwar alummar Afrika.

Wakilan daga kasashen Afrika ta kudu, da Masar, da Senegal, da Kwango -Brazzaville, da Komoros, da Zambia, da Uganda, sun gabatar da muhimman kudirori 10, da suka hada da neman amincewar bangarorin kasashen Rasha da Ukraine, kan su amince da cigaba da bude kofa don fitar da hatsi zuwa kasashen ketare.

Sun kuma bukaci a ajiye makamai a yakin da ake gwabzawa kuma a gaggauta komawa kan teburin sulhu, don hanzarta sakin fursunonin yaki da kuma samar da gagarumin tallafin jin-kai.

A cewar shugaban na Afrika ta kudu dukkan bangarorin na Rasha da Ukraine sun amince a cigaba da lalubo matakan da suka dace, sai dai a ranar Asabar shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi watsi da kaso mafi yawa na kudirorin da aka tsara.

Ukraine ma ba ta nuna wata cikakkiyar ƙwarin gwiwa ba kan shirin.

Yakin ya haddasa karancin hatsi da takin zamani a kasashen Afirka da dama, wadanda suke shigo da kayan daga kasashen na Ukraine da Rasha.

Lamarin dai ya haddasa tsadar farashin abinci a sassan duniya, musamman Afrika.

Bankin raya cigaban Afirka ya ce yakin ya yi sanadin karancin abinci da ya kai tan miliyan 30 a nahiyar.

Shugaba Putin ya sha yin barazanar ƙin sabunta yarjejeniyar sakar wa Ukraine mara ta fitar da hatsi ta jiragen ruwa zuwa Afirka ta mashigar tekun Baharul-aswad wanda Rshar ke riƙe da ikonsa.

Wannan ba shi ne karo na farko da Mista Putin yake barazanar bijirewa ba, sai dai a wannan karo muddin shugaban ya cigaba da nuna tirjiya, matsalar ƙarancin abinci a nahiyar za ta kara ta'azzara, wanda shi ne abun da shugabannin suke kokarin ganin an kauce wa.

Sai dai akwai yiwuwar Mista Putin zai iya bayar da kai bori ya hau saboda yana bukatar goyon bayan kasashen Afirka domin gudun kada a mayar da kasarsa saniyar ware ta fuskar diflomasiyya.

Mene ne mataki na gaba?

Baya ga karuwar fadakarwar da ake samu a duniya game da tasirin da yakin ke haifarwa ga tattalin arziki nahiyar, an sha yin kiraye-kiraye ga shugabannin Afirka da su fito fili su yi Allah wadai da mamayar.

Shugaban Ukraine ya nanata cewa yin Allah wadai da gwamnatin Moscow zai isar da wani bayyanannen sako ga mutanen Rasha cewa mayar da su saniyar ware a harkokin duniya ya faru ne sakamakon matakin da shugabansu ya dauka na kaddamar da yaki kan Ukraine.

Dukka kasashen Uganda da Afrika ta kudu, wadanda wani bangare ne na tawagar wakilan Afrika, ana kallon suna da matsaya guda da Rasha.

A makon jiya jakadan Amurka ya zargi Afirka ta kudu da saɓa ra'ayin tsayawa a matsayin 'yar ba ruwanmu kuma ta samar da makamai ga Rasha, ta saba matsayinta na nuna kin goyon bayan matsayar Rasha, sai dai Afirka ta kudun ta sha musanta zargn.

Sai dai har yanzu babu tabbas ko Afirka ta kudu za ta iya mika Mista Putin ga kotun hukunta laifukan yaki ta duniya, wanda ake sa ran zai ziyarci Afirka ta kudu a taron kasashen Brics da za a gudanar a watan Agusta.

Babban makasudin ziyarar shi ne domin ƙarfafa gwiwar amfani da tattaunawar diflomasiyya wajen kawo karshen yakin Ukraine, kuma daga wannan da alama kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.

Ukraine da Rasha sun jaddada tuntuni da kuma bayan ziyarar tawagar shugabannin na Afirka cewar ba za su hau teburin sulhu, ba tare da gabatar da muhimman sharruda ba.

Ukraine, tana bukatar a kyale kan iyakoki su kasance kamar yadda suke a 1991. Hakan na nufin Rasha ta janye daga dukkan yankunan da ta kwace daga hannun Ukraine a shekaru goma da suka gabata, ciki har da wani ɓangaren yankin Crimea.

Wannan wani batu ne da fadar Kremlin take matukar adawa da shi, tana ikirarin cewa a maimakon shiga yarjejeniyar, kamata ya yi Kyiv ta amince da sabon tsarin mallakar iko da yankuna na hakika.

Kakakin fadar Kremlin Dmitry Peskov, ya sanar a ranar Litinin cewa tattaunawa da wakilan Afirka za ta ci gaba.

Duk da gazawar da aka yi na rashin tattaro shugabannin bangarorin biyu da ke yaki da juna, Mista Ramaphosa ya yi ikirarin cewa kofa a bude take domin ci gaba da tattaunawa a nan gaba.

Source: BBC