Wadanda aka bai wa jan kati da yalo a Premier League ta bana
Hoton alama
Tue, 30 May 2023
Source: BBC
Ranar Lahadi aka kammala gasar Premier League ta kakar 2022/23, wanda Manchester City ta lashe.
Tuni aka samu wadanda suka bar premier league a kakar da aka karkare, za su koma buga Championship a badi.
Sai dai kuma an bai wa 'yan wasa da yawa jan kati da kuma mai ruwan dorawa a wasannin bana.
Hakan ne ya sa muka hada muku wasu jerin 'yan kwallon Premier League da suka karbi katin gargadi da yawa da wadanda aka bai wa jan kati a kakar nan.
Jerin goman farko a 'yan wasan da suka karbi kati mai ruwan dorawa:
Kungiya Yawan katin Yawan laifi Kungiya
- Joao Palhinha 14 48 Fulham
- Joelinton 12 65 Newcastle
- Rúben Neves 12 38 Wolves
- Nelson Semedo 11 47 Wolves
- Fabinho 11 53 Liverpool
- Adam Smith 11 29 Bournemouth
- James Maddison 10 31 Leicester
- Moisés Caicedo 10 65 Brighton
- Conor Gallagher 9 23 Chelsea
- Boubakary Soumaré 9 33 Leicester
Jerin goman farko da aka bai wa jan kati a gasar Premier League:
Kungiya Yawan kati Yawan laifi Kungiya
Casemiro 2 48 Man Utd Nathaniel Chalobah 1 2 Fulham Lucas Moura 1 3 Tottenham James Tomkins 1 3 Crystal Palace Mason Holgate 1 9 Everton Shandon Baptiste 1 11 Brentford Luis Sinisterra 1 14 Leeds João Félix 1 15 Chelsea Diego Costa 1 29 Wolves Jonny 1 13 Wolves
Kungiyoyin da suka karbi katin gargadi da yawa guda 84:
Leeds UnitedNottingham ForestWolverhampton Wanderers
Kungiyoyin da ke da karancin karbar katin gargadi 44:
Manchester CityWest Ham United
Kungiyar da ta karbi jan kati da yawa guda shida a bana:
Wolverhampton Wanderers