Wannan maƙala ta yi waiwaye kan wasu daga cikin manyan abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata daga 25 zuwa 30 ga watan Disamba.
'Yan bindiga sun kashe sama da mutum 140 a Filato
Mataimakin Shugaban Najeriya Kashim Shettima ya kai ziyara jihar Filato don jajantawa game da hare-haren da 'yan bindiga suka kai wasu ƙauyuka da dama.
Mazauna yankunan sun tabbatar da cewa hare-haren sun halaka sama da mutum 140, waɗanda aka fara kaiwa tun ranar Asabar har zuwa Talata.
Gidan Talabijin na Channels ya wallafa wani bidiyo da ke nuna wasu manyan muƙarraban gwamnati da gwamnan jihar ta Filato zaune suna dakon isowar mataimakin shugaban Najeriyar a filin jirgin sama na Yakubu Gowon.
Fadar gwamnati ta yi tir da harin da kuma bai wa jami'an tsaro umarnin zaƙulo maharan don a hukunta su.
Daga cikin tawagar gwamnatin akwai mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, da Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Musa.
Kotu ta ce a ci gaba da tsare Hafsat 'Chuchu' kan zargin Kashe Nafi'u a Kano
Hukumomi a Kano sun gurfanar da matashiyar matar aure, Hafsat Surajo, wadda ake yi wa laƙabi da Chuchu, a gaban kotu, bisa zargin kashe matashi Nafi'u Hafiz da kuma yunƙurin kashe kanta.
Rundunar 'yan sandan jihar ta ce an gurfanar da Hafsat Surajo ne tare da ƙarin mutum biyu a gaban babbar kotun majistare da ke unguwar 'Yankaba a cikin ƙwaryar birnin.
Ɗaya daga cikin lauyoyin waɗanda ake tuhuma, Barrista Rabi'u Sidi, da yake jawabi ga manema labarai bayan fitowa daga kotun, ya ce takardun ƙara, sun nuna cewa ana kuma tuhumar mijin Hafsat da wani malami da kuma ƙarin wani mutum, a kan haɗa baki da ɓoye laifi da kuma bayar da bayanan ƙarya.
Sai dai, Barista Sidi ya ce da aka karanta mata tuhume-tuhumen guda biyu a gaban kotu, Hafsat Surajo ta amsa laifi kan tuhumar farko, amma ta musanta tuhuma ta biyu.
Shi ma wani, Barista I.S Abdullahi, lauyan malamin da 'yan sanda suka kama bisa zargin yi wa mamacin wanka, ya ce wanda yake karewa ya musanta tuhume-tuhumen da aka yi masa.
Ya ce sun nemi kotu ta bayar da belin waɗanda ake ƙara, amma masu gabatar da ƙara sun nemi kotu ta ba su dama su yi nazarin wannan buƙata, kafin bayar da matsayinsu.
To amma, mai magana da yawun 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, ya ce waɗanda ake zargin sun amsa dukkan tuhume-tuhumen da aka yi musu.
Kotun dai daga bisani, ta ɗage zamanta zuwa ranar 8 ga watan Janairu don yanke hukunci a kan buƙatar ba da belin.
Sanarwar da SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano ya fitar daga baya, na cewa a ranar Alhamis ne jami’ansu suka kama Hafsat Surajo ‘yar shekara 24 da ke Unguwa Uku bisa zargin kashe Nafi'u Hafiz, ɗan shekara 38 a gidanta na aure.
Haka zalika binciken ‘yan sandan a cewar sanarwar, ya kai su ga kama mijin matashiyar, Dayyabu Abdullahi mai shekara 38, sai kuma Mallam Adamu mai shekara 65.
An yi jana'izar mutum takwas da ƴan bindiga suka kashe a Katsina
An yi jana'izar mutum takwas da ƴan bindiga suka kashe a wani hari da suka kai karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa mutum huɗu sun jikkata, sannan ba a ga wasu biyu ba a harin da aka kai a ranar Lahadi da dare.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa ƴan bindigar sun zo da yawa inda suka far wa mutanen waɗanda ke kan hanyarsu ta komawa gida daga kauyen Kukar Babangida zuwa Ƴan Gayya.
Mutumin ya bayyana cewa waɗanda aka kashe ba su haura shekaru 22 zuwa 47 kuma dukkansu ‘yan kauyen Yan Gayya ne.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jibia dai na kan iyakar Najeriya da Nijar. Karamar hukumar ta kuma yi iyaka da kananan hukumomin Batsari, Kaita, Katsina, Batagarawa da kuma Zurmi.
Tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Ghali Na'Abba ya rasu
A ranar Laraba tsohon shugaban Majalisar Wakilan Najeriya Ghali Umar Na'Abba ya rasu.
Ya rasu ne a wani asibiti da ke Abuja babban birnin ƙasar, inda ya kwanta don jinya.
An yi jana'izarsa da yammacin Larabar a Kofar Kudu da ke fadar Sarkin Kano Aminu Ado Bayero, inda aka binne shi a makabartar Dan Dolo da ke Goron Dutse.
Haifafen jihar Kano, Na'Abba ya riƙe muƙamin kakakin majalisar ne daga 1999 zuwa 2003 a ƙarƙshin jam'iyyar PDP mai mulki a lokacin.
Ondo ta yi sabon gwamna bayan mutuwar Gwamna Akeredolu
A ranar Laraba, an rantsar da Lucky Aiyedatiwa a matsayin gwamnan jihar, sa'o'i bayan mutuwar Rotimi Akeredolu sanadin cutar kansa a ƙasar Jamus.
Alƙalin alƙalan jihar Mai shari'a Olusegun Odusola ne ya rantsar da shi a ofishin gwamnan Ondo cikin birnin Akure.
Mataimakin gwamnan, ya karɓi ragamar mulkin jihar a matakin riƙo, bayan Gwamna Rotimi Akeredolu ya aika wasiƙa ga majalisar dokokin jihar don sanar da ita game da ƙudurinsa na tafiya jinya da kuma miƙa ragamar mulkin jihar ga Lucky Aiyedatiwa.
Tun farko, an yi ta dambarwa a fagen siyasar jihar, lokacin da majalisar dokokin Ondo ta fara yunƙurin tsige Lucky Aiyetadiwa daga kan kujerar mataimakin gwamna.
Sakataren gwamnan jihar da kwamishinonin Ondo da shugaban jam'iyyar APC da alƙalan jihar na cikin manyan jami'an da suka halarci taron rantsuwar.
Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yari a Ogun
Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan yarin Ijebu Ode da ke jihar Ogun a kudancin Najeriya.
Hukumomin gidan yarin sun tabbatar da tserewar fursunoni uku.
Sanarwar da jami’in hulɗa da jama’a na hukumar kula da gidajen gyara hali reshen jihar Ogun Victor Oyeleke ya fitar, ta ce fursunonin sun tsere ne ranar Asabar da tsakar dare.
Fursunonin sun tsere ne ta hanyar tsallaka katanga.
A cewar sanarwar, tuni aka shiga farautar fursunonin - hukumomin sun ce suna da bayanansu da kuma iyalansu, suna kuma aiki da sauran hukumomi domin dawo da su cikin gaggawa.
Har ila yau, sanarwar ta ce ɗaya daga cikin fursunonin da suka tsere yana zaman gidan yarin ne kan hukuncin fashi da makami da aka yanke masa, ɗayan kuma an ɗaure shi a gidan yarin ne kan aikata kisa.
Yadda ta kasance a taro tsakanin Tinubu da gwamnonin Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya nemi hadin kai tsakanin gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci gaban kasa baki daya.
Shugaban ya yi wannan kiran ne a ziyarar da gwamnonin jihohin Najeriya suka kai masa a gidansa da ke Legas ranar Talata, inda suka tattauna halin da kasar take ciki musamman kashe-kashe da matsin tattalin arziki.
Wannan na zuwa yayin da wasu yan bindiga suka kashe mutum sama da 100 a jihar Filato
Gwamnan Zamfara Dr Dauda Lawan Dare wanda na daga cikin gwamnonin da suka gana da shugaba Tinubun ya ce gwamnoni sama da 20 ne suka kai wannan ziyara.
Gwamnan ya ce: ''Mun tattauna kan batutuwa da dama da suka hadar da batun hada kai da gwamnatin tarayya da kuma na jihohi, sannan ya yi jaje a kan abun da ya faru a jihar Plateau na kashe-kashen da aka yi."
Yadda ta kasance a taro tsakanin Tinubu da gwamnonin Najeriya
Ƙazafi ake min, ban buɗe asusun banki 593 a ƙasashen waje ba - Godwin Emefiele
Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Godwin Emefiele, ya musanta zarge-zargen satar dukiyar ƙasa da ake yi masa a wani rahoton Mai Bincike na Musamman kan harkokin bankin CBN da aka fitar a baya-bayan nan.
Ya bayyana matsayin nasa ne a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Re: Emefiele, others stole billions, illegally kept Nigeria’s funds in foreign banks’ da ya fitar ranar Lahadi.
Idan za ku iya tunawa a cikin makon jiya ne, Mai Bincike na Musamman kan harkokin Babban Bankin Najeriya, Jim Obaze, ya bankaɗo cewa tsohon gwamnan bankin ya jibge fam miliyan 543, 482,213 ba tare da izini ba a bankunan Birtaniya kawai.
Wani ɓangare na rahoton Jim Obaze a cewar jaridar Daily Post ta intanet, “Tsohon gwamnan babban bankin, Godwin Emefiele ya jibge kuɗaɗen Najeriya ba tare da izini ba a asusun ajiya 593 na bankunan ƙasashen waje a Amurka da China da Birtaniya, lokacin da yake mulki.
Sai dai Godwin Emefiele a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ya ce, bayan sakin sa a matakin beli daga gidan yarin Kuje, hankalinsa ya kai kan wasu labarai masu alaƙa da rahoton Jim Obaze.
“Na karanta labaran, kuma da ƙarfin murya ina cewa abin da suka ƙunsa, ƙarairayi ne da karkatar da hankali da kuma maƙarƙashiya don a ɓata min suna, a ci mini zarafi sannan da biyan muradin mai binciken.”
Ya kuma ce ba shi da hannu a buɗe asusun ajiya 593 a sassan duniya, kuma bai ma san an buɗe su ba.
Sai dai ya ce akwai sashe-sashe na babban bankin da ke da iko su aiwatar da irin waɗannan harkoki kamar yadda doka ta amince musu bisa tanade-tanaden aikin CBN.
Don haka, a cewar Emefiele "Ni ma kamar sauran 'yan Najeriya masu kyakkyawar niyya da suka yi magana kan wannan batu, ina neman a gudanar da cikakken bincike kuma a fayyace komai a faifai game da waɗannan zarge-zarge na almundahana".
Ya kuma ce ya umarci lauyoyinsa, su hanzarta ɗaukan matakan shari'a don wanke sunansa daga kalaman ɓata-suna da ke ƙunshe a cikin rahoton da kuma labaran da suka wallafa shi.