0
MenuAfrica
BBC

Waiwaye: Neman da ICPC ke yi wa surukin Buhari da ƙwato $153 da EFCC ta yi

 118520272 899b7dcf 684a 499c Afe9 F0e380d87f13 1 Tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke

Sun, 16 May 2021 Source: www.bbc.com

Ga wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a makon da ya gabata a Najeriya, daga Lahadi 9 ga Mayu zuwa Asabar 15 ga watan.

EFCC ta kwato karin $153m daga wurin Diezani

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya ta'annati, EFCC, ta sanar da kwato $153m daga hannun tsohuwar ministar man fetur Diezani Alison Madueke wadda ta tsere daga kasar zuwa Birtaniya a 2015.

Jaridar Vanguard ta ambato shugaban hukumar Abdulrasheed Bawa yana cewa sun kwace akalla kadarori 80 da kudinsu ya kai $80m.

"Muna fatan ganin lokacin da, watakila, za ta shigo kasar nan, kuma tabbas za mu yi nazari kan abubuwan da ta yi, sannan mu san matakin da za mu dauka nan gaba. Tabbas ba mu yi watsi da batunta ba," a cewar Abdulrasheed Bawa.

Ya shaida wa manema labarai cewa a shirye yake ya sauka daga kan mukaminsa na shugabancin hukumar EFCC "idan wani ya sa na yi abin da bai dace ba".

Ms Alison-Madueke ita ce ministar man fetur daga2010 zuwa 2015.

Lalacewar rumbun samar da wutar lantarki a Najeriya

Rumbun samar da wutar lantarki a Najeriya ya sake lalacewa, abin da zai sake ta'azzara ƙarancin wutar a jihohin ƙasar.

Lalacewar ta faru ne ranar Larabar da ta gabata, kamar yadda kamfanin rarraba lantarki na Transmission Company of Nigeria (TCN) ya tabbatar cikin wata sanarwa.

"Transmission Company of Nigeria na bayyana cewa da misalin ƙarfe 11:01 na safiyar Laraba, 12 ga watan Mayu, an samu lalacewar layin lantarki gaba ɗaya sakamakon lalacewar wani rumbu daga cikin layukan," a cewar TCN.

Su ma kamfanonin dillancin wutar na KEDCO da Kaduna Electric sun tabbatar da faruwar matsalar, inda suka bai wa kwastomominsu haƙuri.

Ceto mutum 52 da aka yi yunkurin garkuwa da su

Hukumar yaƙi da masu safarar mutane a Najeriya NAPTIP ta ce ta ceto mutum 52 a jihohin Kano da Jigawa da Katsina da ke arewacin ƙasar, waɗanda aka yi yunƙurin safararsu.

Kazalika ta kama mutum huɗu da ake zargi da aikata laifin, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Libya sannan su ƙarasa Turai daga jihohin Imo da Delta da Edo da Ondo da Ogun.

Daga cikin 52, 48 mata ne da kuma maza huɗu, dukkansu 'yan shekara 16 zuwa 34.

Shugaban hukumar na Kano, Abdullahi Babale, ya ce za su tabbatar sun tsaurara sa ido domin ci gaba da kama masu safarar mutane a arewacin ƙasar.

Sakin firsunoni 123 da Ganduje ya yi a Kano

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya yi wa ɗaurarru 123 afuwa albarkacin Idin Ƙaramar Sallah.

Gwamnan wanda ya jagoranci sakin 'yan gidan yarin na Goron Dutse a ranar Alhamis, ya ce an zaɓi waɗanda aka yi wa afuwar ne bisa irin girman laifinsu da kuma alamun sauya hali da suka nuna.

Ganduje ya ce ya kai ziyarar ce domin ya nuna wa ɗaurarrun cewa "gwamnatin Kano ta san da zamansu sannan kuma tana kallonsu a matsayin 'yan jihar".

Gwamnan ya shawarce su da su sauya hali domin komawa cikin al'umma sannan su yi wa ƙasa addu'ar zaman lafiya.

Ziyarar Shugaban Chadi

A ranar Juma'a ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin takwaransa na ƙasar Chadi Laftanar Janar Mahamat Idriss Deby a Abuja, inda suka tattauna game da ci gaban ƙasashensu.

Wannan ne karon farko da Janar Mahamat mai shekara 37 ke ziyara a Najeriya tun bayan da ya gaji mahaifinsa Idris Deby Itno a matsayin shugaban gwamnatin riƙon ƙwarya ta Chadi a watan Afrilu.

A farkon watan Mayu ne Janar Mahamat ya kai irin wannan ziyara Jamhuriyar Nijar. Muhimmancin ziyarar na da girman gaske ganin yadda ƙasashen uku ke fama da hare-haren 'yan bindiga masu iƙirarin jihadi baya ga iyakoki da suka haɗa.

Shugaba Buhari ya faɗa wa Janar Mahamat cewa Najeriya za ta tallafa wajen daidaita Chadi da kuma tabbatar da komawarta kan tsarin mulkin dimokuraɗiyya.

"Najeriya ta san irin rawar da Chadi ta taka wajen taimaka mata a yaƙi da ta'addanci kuma muna godiya sannan za mu ci gaba da wannan alaƙar", in ji Buhari.

Neman surukin Buhari da ICPC ke yi

Masu binciken laifukan cin hanci d rashawa a Najeriya na neman surukin Shugaban kasar mai suna Gimba Yau Kumo ruwa a jallo.

Hukuma Mai zaman kanta da ke yaki da miyagun halaye ta Najeriya ICPC ce ta wallafa sakon neman shi kan wata badakkalar kudaden mallakar gidaje da aka wawushe da darajarsu ta zarce dala miliyan 65.

Kumo shi ne tsohon shugaban gudanarwa na bankin Federal Mortgage Bank of Nigeria mai samar wa al'umomin kasar basusukan mallakar muhallai na cikin jerin mutane biyun da hukumar ICPC ta wallafa sunayensu da hotunansu a shafinta na intanet.

Sakon da aka wallafa tare da hotuna, wanda kakakin hukumar Azuka Ogugua ya sanya wa hannu a shafin hukumar na intanet ta ICPC na cewa:

"Mutanen da hotunansu mu ka wallafa a sama, Mista Tarry Ruffus, Mista Gimba Yau Kumo da Mista Bola Ogunsola sun kasance na wadanda mu ke NEMA...kan wata badakkala da ta shafi wawushe asusun ajiya na kasa kan mallakar muhallai da kuma karkatar da$65m"

Source: www.bbc.com
Related Articles: