Wannan maƙala na ɗauke da wasu daga cikin muhimman abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da ya gabata.
Tasirin yajin aikin da 'yan ƙwadago ya yi a Najeriya
Ƙungiyoyin kwadago na Nigeria Labour Congress (NLC) da ta Trade Union Congress (TUC) sun dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar Talata 14 ga watan Nuwamba.
Hakan ya biyo bayan wani taro da suka yi da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
A ranar Litinin ne NLC ta yanke hukuncin tsunduma yajin aikin sakamakon dukan da aka yi wa shugabanta Joe Ajaero.
A ranar 1 gawatan Nuwamba ne Ajaero tare da rakiyar wasu mambobin NLC suka shirya wata zanga-zangar a Owerri babban birnin Jihar Imo kan zargin take haƙƙin ma’aikata da gwamnatin jihar ke yi.
Gabanin zanga-zangar ta kankama ne kuma ‘yan sanda suka cafke shugaban kungiyar kwadagon kuma aka lakaɗa masa duka, wani abu da aka zargi gwamnan jihar Hope Uzodinma da kitsawa.
Za ku iya karanta ƙungiyoyin da suka shiga yajin aikin da kuma irin tasirin da ya yi idan kuka latsa nan:
An tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasdinawa a Kaduna
'Yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar goyon bayan Falasɗinawa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ranar Alhamis.
Rahotonni sun ce masu zanga-zangar sun fara tattaki ne daga kan babban titin Ahmadu Bello, inda suka ratsa ta titin Muhammadu Buhari a tsakiyar birnin Kaduna, kafin daga bisani 'yan sanda suka tsarwatsa su.
A tattaunawarsa da BBC, ɗaya daga cikin jagororin ƙungiyar IMN, Aliyu Umar Tirmidhi, ya ce sun fito ne kawai domin nuna adawa da rikicin da ke faruwa a yankin Gaza.
Ya kuma ce a lokacin arangamar tasu da ƴan sanda an raunata mutane da dama, kuma "mutum ɗaya ya rasa ransa."
Tun bayan fara yaƙin Isra'ila da Hamas, an gudanar da irin waɗannan zanga-zanga na nuna goyon baya ga Falasɗinawa a manyan biranen duniya.
Kotu ta ce zaɓen gwamnan Zamfara bai kammala ba
Kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta ayyana zaɓen gwamnan jihar Zamfara, a matsayin wanda bai kammala ba.
A hukuncin da ɗaukacin alƙalanta uku ƙarƙashin Mai shari'a Sybil Nwaka suka amince da shi, kotun ta soke halascin zaben Gwamna Dauda Lawal Dare na ranar 18 ga watan Maris din 2023.
Kotun da yammacin ranar Alhamis a Abuja, ta kuma bayar da umarnin sake gudanar da zaɓe a ƙananan hukumomin Zamfara uku, da suka haɗa da Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.
Ta ce kotun sauraron ƙararrakin zaɓe ta jihar Zamfara, ba ta yi la’akari da hujjojin da masu ƙara suka gabatar ba – wato jam'iyyar APC .
Kotun ta kuma yi watsi da sakamakon da jam’iyyar APC da hukumar zaɓe ta ƙasa INEC suka bayar na ƙaramar hukumar Maradun.
Don haka ta umarci hukumar zabe (INEC) ta gudanar da sabon zabe a ƙananan hukumomin uku, inda ba a gudanar da zabe ba a baya, ko kuma ba a ƙidaya sakamakon wasu tashoshin zabe ba.
Dan takarar jam'iyyar APC a zaben watan Maris, Bello Matawalle ne sake kalubalantar hukuncin da karamar kotun zaben jihar Zamfara ta yanke, wanda ta kori shari'arsa bisa hujjar cewa ya gaza gabatar da gamsassun hujjoji.
Tsohon gwamnan na Zamfara, wanda a yanzu yake rike da mukamin karamin ministan tsaro, yana neman wa'adin mulki na biyu ne bayan karewar mulkinsa na tsawon shekara hudu.
Yadda masana suka auna zaɓen gwamnan Kogi da Imo da kuma Bayelsa
A Najeriya, masana da masu sa ido a kan zabe na cigaba da tofa albarkacin bakinsu dangane da yadda hukumar zabe ta gudanar da zaben gwamna a jihohin Imo da Bayelsa da kuma Kogi a karshen makon jiya.
Wasu dai na ganin hukumar ta yi abin a yaba, musamman wajen tabbatar da tsaro ga masu zabe. Sai dai sun ce akwai kurakuren da aka tabka, wadanda ke bukatar gyara, matukar ana so a kayautata zabuka a nan gaba.
Saɓanin yadda aka saba da yi wa hukumar zaɓe caccaka da suka a kan yadda take gudanar da zabe a Najeriya, a wannan karon, da dama daga cikin masu sa ido a kan zaɓe a kasar na ganin cewa hukumar ta yi abin a yaba ta fuskar shiri.
Ya ce ‘‘An buɗe runfunan zaɓe a kan lokaci, ta kawo kayayyakin zaɓe a kan lokaci, ta tabbatar da amfani da na’urarar BVAS kuma sun taimaka wajen samar da ingancin zaɓen’’
Karanta cikakkiyar maƙalar a nan:
Zaɓen Kogi: Ba zan je kotu ba saboda ɓata lokaci ne - Ɗan takarar SDP Murtala Ajaka
Ɗan takarar jam'iyyar Social Democratic Party (SDP) a zaɓen gwamnan jihar Kogi ya yi zargin cewa an yi maguɗi a zaɓen na ranar Asabar, yana mai cewa ba zai je kotu ba "saboda ɓata lokaci ne".
Murtala Ajaka wanda ya zo na biyu a sakamakon da hukumar zaɓe Inec ta bayyana, ya faɗa wa kafar talabijin ta Channels TV cewa zuwa kotu ɓata lokaci ne "saboda hukumar zaɓen za ta je kotun kuma ta kare sakamakon da ta bayyana".
Inec ta ce Usman Ododo na jam'iyyar APC ne ya yi nasara bayan ya samu ƙuri'a 446,237, sai Ajaka da ya samu 259,052, da kuma Dino Melaye na PDP mai ƙuri'a 46,362.
"Na shafe shekara 20 ina siyasa, saboda haka na san yadda lamarin yake. Me zan je kotu na yi bayan Inec ɗin da suka yi wannan abin za su je kotun a matsayin waɗanda ake ƙara kuma su kare abin da suka aikata?" in ji Ajaka.
"Wannan ɓata lokaci ne kawai, sai dai jam'iyya [ta kai ƙara] amma ni kam raina ya ɓaci sosai."
Tun kafin a kammala tattara sakamakon zaɓen, ɗan takarar PDP Sanata Dino Melaye ya yi watsi da shi, yana mai neman Inec ta soke shi gaba ɗaya.
Douye Diri na PDP ya lashe zaɓen gwamnan jihar Bayelsa
Gwamnan Bayelsa kuma ɗan takarar jam'iyyar PDP, Douye Diri, ya lashe zaɓen gwamnan jihar da aka gudanar ranar Asabar da ta gabata.
Mista Diri ya samu wa'adi na biyu ne bayan Baturen Zaɓe Farfesa Faruq Kuta ya bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara da ƙuri'a 175,196.
Ɗan takarar adawa na APC, Timipre Sylva, shi ne ya zo na biyu da ƙuri'a 110,108, sai kuma Udengs Eradiri na jam'iyyar LP a mataki na uku da ƙuri'u 905.
Sakamakon ƙaramar hukuma biyu na Kudancin Ijaw da Brass ne suka jawo ɗage tattara sakamakon har zuwa Litinin bayan an bayyana na ƙananan hukumomi shida cikin takwas a ranar Lahadi.
Turawan zaɓe na wasu ƙananan hukumomi sun bayar da rahoton soke zaɓe a rumfunan zaɓe da dama saboda hatsaniya, da garkuwa da mutane, da sace malaman zaɓe.
An samu kifewar kwale-kwale a Taraba
A ranar Litinin rahotonni suka ce hatsarin jirgin ruwa ya rutsa da mutane da dam a ƙaramar hukumar Ibbi da ke jihar Taraba a tsakiyar Najeriya.
Hukumar bayar da agajin gaggawa a Najeirya (NEMA) ta ce an gano wasu gawawwaki tare da ci gaba da neman waɗanda ake zargin haɗarin jirgin ya rutsa da su.
Darektan kula da ayyukan ceto na NEMA, Dr Bashir Garga, ya ce mutanen da haɗarin jirgin ruwan ya rutsa da su sun taso ne daga Ibbi zuwa Ɗan Anacha a cikin daren jiya.
Ya ce bayanai da suka tattaro, sun gano cewa haɗarin ya afku ne sakamakon wani abu mai ƙarfi da jirgin ya daka a tsakiyar kogin yana tsaka da tafiya.
Wannan dai na zuwa ne makonni da aka sami makamancin irin wannan haɗarin na jirgin ruwa a yankin ƙaramar hukumar Karim Lamiɗo a jihar ta Taraba da ya yi sanadiyar mutuwar 17 tare da ceto sama da mutum 20, inda har yanzu ba a kai ga gano 63 ba.
Hakan ne ma ya sa gwamnatin jihar haramta dukkan tafiye-tafiyen jiragen ruwa da daddare a faɗin jihar.
Dalilin da ya sa muka hana wasu ƴan Najeriya shiga ƙasarmu - Saudiyya
Ofishin jakadancin Saudiyya a Najeriya ya yi ƙarin haske kan rahotonnin mayar da 'yan Najeriya 264 a lokacin da suka shiga ƙasar, yana mai cewa ba da wata manufa aka yi hakan ba.
A ranar Lahadi ne gwamnatin Saudiyya ta soke bizar wasu fasinjoji da jirgin Air Peace ya ɗauka a lokacin da suka sauka a ƙasar bayan tashin su daga Kano - abin da ya sa ƙasar ta buƙaci fasinjojin su koma Najeriya.
Cikin wata sanarwar da ofishin jakadancin Saudiyyar ya fitar ranar Laraba, ya ce "fasinjojin da aka hana shiga ƙasar, ba su cika sharuɗɗa da dokokin Saudiyya ba, saboda sun gabatar da bayanan da ba na gaskiya ba domin samun bizar da ba ita ya kamata a ba su ba, inda sai bayan sun isa Saudiyya ne aka gano hakan".
Sanarwar ta ƙara da cewa ''Ba 'yan Najeriya kaɗai aka yi wa hakan ba, har da na wasu ƙasashe".
Haka kuma ita ma ma'aikatar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya cikin tata sanarwar da ta fitar ranar Talata, ta ce 'tana bincike game da lamarin, domin tabbatar da ko an saɓa wata ƙa'ida".
Mataimaki na musamman ga ministan harkokin wajen ƙasar, kan kafofin yaɗa labarai, ya ce ma'aikatar za ta tabbatar da irin wannan abu bai sake faruwa kan 'yan ƙasar ba a nan gaba.
Ofishin jakadancin na Saudiyya ya kuma fitar da gargaɗi ga mutanen kan su riƙa cika ƙa'ida wajen neman bizar shiga ƙasar.
''Haka kuma muna son jaddada muhimmancin bin ƙa'idoji da dokokin da saudiyya ta gindaya ga duka mutanen da ke da burin zuwa kasar", kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Daga ƙarshen ofishin ya buƙaci duka fasinjojin da ke muradin ziyartar ƙasar da su riƙa nazarin takardun bizarsu, domin dacewa da dokokin ƙasar kafin su fice daga ƙasashensu zuwa Saudiyya."