Kamar kowane mako, wannan maƙala na ɗauke da wasu daga cikin abubuwan da suka faru a Najeriya a makon da muke ban kwana da shi.
Ba mu tattauna da NNPP da PDP don kafa jam’iyyar haɗaka ba - LP
Jami’iyyar Labour a Najeriya ta musanta cewa ta na tattaunawa da takwarorinta na NNPP da PDP don kafa jam’iyyar haɗaka domin tunkarar jam’iyya mai mulki ta APC a zaɓe mai zuwa.
Jam’iyyar faɗi haka ne bayan da wasu daga cikin jaridun Najeriya suka ruwaito cewa ana wata ganawa tsakanin ‘yan takarar shugabancin ƙasar na PDP Atiku Abubakar, da na NNPP Rabi’u Kwankwaso, da kuma Peter Obi don haɗewa waje guda.
Mai magana da yawun LP na ƙasa Dakta Tanko Yunusa, ya ce abun da suka sani shi ne, akwai tattaunawa ta fahimta da ake yi tsakani ɗan takararsu da na NNPP da kuma na PDP, wanda kuma ba shi da alaƙa da batun haɗewa ko wani abu makamancinsa ba.
Haka kuma Dr. Tanko Yunusa ya ce ko da za a haɗe ma to sai dai a ba su jan ragamar ta fi da komai, kuma a sa su gaba.
Tinubu ya rantsar da ministoci 46
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce ministocin da aka rantsar a ranar Litinin an zaɓo su ne bisa cancanta domin su taimaka wajen tafiyar da lamurran ƙasar.
Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da ya yi jawabi bayan rantsar da sabbin ministoci a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
"Ƴan Najeriya na sa ran za ku yi aiki mai inganci kuma za ku sauke nauyin da aka ɗora muku." - In ji Tinubu
Ya ƙara da cewa "Dole ne ku yi aikin da zai sanya ƴan Najeriya su sake amincewa da gwamnati."
Ya bayyana cewa akwai babban nauyi a kan sabbin ministoci ganin irin manyan alƙawurran da gwamnatinsa ta ɗauka.
Shugaban ya kuma buƙaci sabbin ministocin da su yi aiki ba tare da nuna banbanci ba, inda ya ce: ”An ba ku wannan matsayi ne ba domin ɓangaren da kuka fito ku jihonhinku ba, sai dai domin ƙasa baki ɗaya.”
Mun zaɓo ministoci ne bisa cancanta - Tinubu
Tinubu ya nemi malamai su koma Nijar a karo na uku
Shugaba Bola Tinubu ya umarci ayarin malaman addinin Musulunci da ke shiga tsakani a rikicin Jamhuriyar Nijar su koma wajen shugabannin mulkin sojin ƙasar don samo wani ƙwaƙƙwaran alƙawari.
Bayan wani taron sirri da malaman, jagoran tafiyar, Ustaz Abdullahi Bala-Lau ya ce Tinubu na neman a kauce wa amfani da ƙarfi don warware rikicin, kuma a tabbatar an mayar da Nijar kan tafarkin tsarin mulki.
Ya ce Tinubu ya karɓi shawarwarinsu na a kauce wa amfani da ƙarfin soja wajen kawo ƙarshen duk wata taƙaddama, musamman ma a tsakanin maƙwabta da manyan ƙawaye na tsawon lokaci.
A ranar Laraba ne malaman addinin Musuluncin suka koma Nijar a karo na biyu, inda suka gana da Shugaba Abdurahamane Tchiani da Firaminista Ali Lamine Zeine, kafin su dawo Abuja don yi wa Shugaba Tinubu bayani a kan matsayar da suka cimma.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ya ruwaito Sheikh Bala-Lau ya ce: "Wannan ce ta sa ya sake cewa mu koma Nijar don mu ci gaba da tattaunawa a ƙoƙarin ganin an mayar da ƙasar kan tsarin dimokraɗiyya.
Ya kuma umarci mu sake tuna wa shugabannin sojin Nijar cewa akwai fa shawarar da Ecowas ta yanke game da juyin mulki".
An dawo da 'yan Najeriya baƙin haure daga Libya
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayar da rahoton cewa, an mayar da wasu 'yan Najeriya 161 daga kasar Libya zuwa gida, a wani shirin sa-kai da Majalisar Dinkin Duniya ke tallafawa.
Sun isa ne a wani jirgi daga Tripoli zuwa babban filin jirgin saman Legas ranar Litinin.
Daga cikin wadanda aka mayar da su ɗin akwai mata 75 da ƙananan yara shida wadanda aka tsare a wuraren tsare mutane a ƙasar Libya.
Ministan cikin gidan ƙasar ya bayyana cewa, an dakatar da mutum 102 daga cikin waɗanda aka mayar da su gida a kan iyakar Libya da Tunisia.
Libya dai ta kasance wata babbar hanya da bakin haure 'yan Afirka ke bi a ƙoƙarinsu na tsallakawa Turai ta tekun Bahar Aswad ba bisa ƙa'ida ba.
Wani jami'i a ofishin jakadancin Najeriya a Libya, ya tabbatar wa kamfanin dilancin labaran AFP cewa baƙin hauren sun zaɓi koma wa gida ne da son ransu, ba tare da an tilasta musu ba.
Ya kuma bayyana cewa waɗanda suka koma ɗin sun gamsu su koma Najeriya, domin “babu wani wurin zama kamar gida.
Hare-haren ƴan bingida na neman durƙusar da yankin Gumau a jihar Bauchi
Duk da cewa lamarin rashin tsaro ba baƙon abu ba ne a Najeriya, amma a yankin Gumau da ke Jihar Bauchi zai iya zama baƙo.
Mazauna garin Gumau da ke Ƙaramar Hukumar Toro a jihar ta Bauchi sun ce wani gungun ‘yan bindiga na kai hare-hare kan jama’ar wasu kauyuka tare da kashe su da kuma tafiya da dukiyoyinsu.
A baya-bayan nan wasu rugage da wasu ƙauyukan Gumau ɗin sun fuskanci hare-hare da suka yi sanadin mutuwar mazauna yankin.
Wani mutum da BBC ta tattauna da shi, wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya ce "A sati biyu da suka gabata an zo garin Gumau an sace mutane har da wata mata mai ciki wata bakwai."
"An ɗauke ta tare da maigidanta da kuma wani makwabcinsu, su uku aka tafi da su. Sai da suka biya kuɗin fansa sama da miliyan biyar sannan aka sake su," in ji mutumin.
Ga cikakken labarin a nan: Hare-haren ƴan bingida na neman durƙusar da yankin Gumau a Jihar Bauchi
Emefile bai bayyana a gaban kotu ba
An sake fuskantar wani tsaiko a shirin gurfanar da gwamnan babban bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele a gaban kotu, dangane da zargin karkatar da naira biliyan 6.9.
Babbar Kotun tarayya da ke Abuja ba ta lissafa shari'ar da ake yi wa Emefiele cikin shari'un da za ta saurara ranar Laraba ba.
Lauyoyin Emefiele da hukumar tsaro ta farin kaya (DSS), wadanda su ne masu gabatar da kara, ba su halarci zaman kotun ba,
Ba a dai bayar da dalilin da ya sa shari’ar ba ta cikin jerin shari'un da za a saurara a kotun ba.
Hukumar DSS dai ba ta mayar da martani ga tambayoyin da BBC ta yi ba game da wannan lamari.
A ranar Alhamis din da ta gabata, Emefiele ya bayyana a kotun amma kotun ta ɗage ƙarar saboda Sa’adatu Yaro, wata ma’aikaciyar babban bankin kasar, kuma wadda ke fuskantar tuhuma tare da Emefiele ba ta bayyana a kotun ba.
Wannan ne ya sa mai shari’a Hamza Mu'azu, ya dage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga watan Agusta.
Sabon ministan Abuja ya yi alƙawarin inganta tsaro a babban birnin
Sabon ministan babban birnin tarayyar Najeriya - Abuja, Nyesom Wike, ya yi barazanar fara rusa gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba.
Wike ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan rantsar da shi domin soma aiki a ranar Litinin.
"Idan kun gina gidajenku a wuraren da aka saba ka'ida, sai an rusa su," in ji Wike.
Tsohon gwamnan Ribas din yana cikin ministoci 45 da shugaban Najeriya Bola Tinubu ya rantsar da su a fadarsa da ke Abuja.
Wike ya sha alwashin yin tir da tsarin da ke kawo cikas ga taswirar babban birnin tarayyar.
Gwamna Uba Sani ya rage kuɗin manyan makarantu a jihar Kaduna
Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya amince da rage kuɗin makaranta a manyan makarantu na jihar.
A cikin wata sanarwa da ya fitar yau Litinin, gwamnan ya ce ya yi hakan ne domin rage irin wahalhalun da tsadar kuɗin makaranta ke haifarwa ga al'ummar jihar.
Sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari na kuɗin makaranta da ɗalibai ke biya a jami'ar jihar Kaduna, wato KASU.
Haka nan an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari na kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli da ke Zaria.
Bugu da ƙari sanarwar ta ce an yi ragin kashi hamsin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a Kwalejin ilimi ta jihar da ke Gidan Waya.
Yayin da aka yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai masu karatun babban difiloma ke biya a Kwalejin koyar da harkokin lafiya ta Shehu Idris da ke Makarfi, inda su ma masu karatun difiloma za su samu ragin kashi talatin cikin ɗari.
A ƙarshe sanarwar ta ce an yi ragin kashi talatin cikin ɗari a kan kuɗin da ɗalibai ke biya a kwalejin koyon jinya ta jihar.