BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Wakilin BBC a Gaza: ‘Na sare, rayuwa ta tarwatse akan idona’

Hoton wani hari da Isra'ila ta kai a Gaza

Fri, 8 Dec 2023 Source: BBC

Rahoto daga wakilin sashen Larabci na BBC Adnan El-Bursh

A birnin Khan Younis, Gaza

Matasa maza sanye da wandon Jins da riga mai dogon hannu, sun jeru tamkar ana sallar jana'za a gaban asibitin Nasser da ke Khan Younus.

Daruruwan mutane ne suka mutu, tun bayan da Isra'ila ta zafafa kai hare-haren bama-bama kudancin Gaza a ranar 1 ga watan Disamba.

Wata mummunar rana mai cike da tashin hankali ce a gaban kofar shiga sashen gaggawa da hadari a asibitin.

Ma'ikata sanye da kayan asibiti, su na kai komo, muryoyi na tashi ya yin da maza sukai dandazo wuri guda.

Duk wani umarni da ake ba dawa ba ya tasiri, mutane na cikin rudu da kidima, wasu a gajie matuka.

Wata mota ce ta tsaya a wurin, an kuma danna odarta da kunna fitilunta, cikin gaggawa aka fito da wani matashi aka dora kan makarar daukar marassa lafiya aka yi gaggawar shiga da shi cikin asibitin.

Ba a jima ba, wata motar ta shigo a sukwane, ta yi budu-budu da kura, akai gaggawar fito da wani yaro da kafafunsa ya taka, zai kai akalla shekara 4 zuwa 5.

Washegari, a can wata unguwa, wata uwar 'ya'ya shida mai suna Samah Ilwan ce ke neman taimako.

"Ina son aika sako ga duk duniya, da kasashen Larabawa," in ji ta.

"Ina son shaidawa duniya babu abin da muka yi, ba mu aikata laifi ba."

Sai ta daga gorar ruwa guda biyu da ba komai a ciki, ta ce 'ya'yanta mata biyar da namiji daya su na tsananin bukatar ruwan sha.

"Mun zama tamkar maguna da karnuka. Kai karnuka da maguna sun fi mu gata tun da suna da wurin zama. Amma mu ba mu da komai. Gararanba kawai mu ke yi a kan tituna."

Tun ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kaddamar da hare-hare kan Isra'ila, rayuwa ta tsananta.

Kungiyar Tarayyar Turai da Amirka da Birtaniya sun ayyana Hamas da kungiyar 'yan ta'adda, wadda ta kashe Isra'ilawa akalla 1,200 , tare da yin garkuwa da sama da mutum 240, tare da tsare su a Gaza.

Daga nan Isra'ila ta fara kai munanan hare-haren bama-bamai da makamai masu linzami babu kakkatawa.

Ma'aikatar lafiya da Hamas ke jagoranta, ta ce sama da Falasdinawa 15,800 aka kashe daga fara yakin, kuma yawancinsu mata da kananan yara.

An amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki 7, wadda anan akai musayar Isra'ilawan da Hamas ke tsare da su da kuma Falasdinawan da Isra'ila ke tsarewa a gidajen kasonsa yawancinsu tun kafin fara yakin na baya-bayan nan.

Wannan ne wuri mai aminci musamman ga babbar motar tauraron dan adam, ana samun layin intanet mai kyau, amma kwanaki kadan da suka wuce komai ya kacame.

A koda yaushe burina da alfahari na shi ne zama dan Jarida, amma yanzu lamuran na neman fin karfina. Rayuwa na neman karewa kan idona.

Lokaci zuwa lokaci, na kan samu damar yin balaguro zuwa tsakiyar Gaza domin ziyartar iyalina. Amma yanzu da Isra'ila ta rufe wata hanya, dayar da ke bude na da hatsari, ina ji ina gani na hakura da zuwa.

Asalinmu 'yan arewacin Gaza ne, amma sai muka tsero kudanci tare da iyalina da 'yanuwana, bayan umarnin da sojin Isra'ila suka bai wa mazauna yankin inda suka ce Kudancin Gaza ya fi aminci da tsaro.

A yanzu su na gargadin mu tattara inamu-inamu mu bar yankin, saboda su na shirin kai farmaki ta kasa a Khan Younus, sun shaida mana mo koma Rafah da ke iyaka da Masar wanda nan ma a wani bangaren kudancin ne.

Duk da irin abubuwan da suka same ni da iyalina da 'yan uwana tun fara wannan yakin, wanna ne karon farko da na ji na sare, na rasa yadda zan yi, ba ni da wani karfi ko iko, komai ya kubuce daga hannuna.

Na saba bai wa iyalai da 'yan uwana kariya da tabbatar da tsaronsu, kullum da shirin da na ke yi don tabbatar da hakan. Amma yanzu na rasa tudun dafawa, ban san wane matakin zan dauka ba.

Shin na tafi Rafah, na ci gaba da aiki, in yi fatan iyali da 'yan uwana za su kasance cikin aminci? Ko dai na yi kokarin komawa inda suke, na daina dauka da aiko rahoto, idan kuma mai aukuwa ta kasance, ko ba komai za mu mutu tare?

Ba na fatan wani mahaluki ya samu kan shi cikin hali irin wannan, wanda abu ne mai sauki ba.

Source: BBC