Menu

Wane ne zai maye gurbin Abdullahi Adamu a shugabancin APC ?

Abdullahi Umar Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano

Thu, 20 Jul 2023 Source: BBC

Bayan ajiye aikin tsohon shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu, jagororin jam'iyyar mai mulki a Najeriya na faɗi-tashin nemo wanda zai riƙe shugabancin har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa.

APC zuwa yanzu, ba ta ayyana ranar yin wannan taro ba, bayan manyan masu riƙe da shugabancin jam'iyyar biyu a matakin ƙasa sun ajiye aiki.

A farkon makon nan ne Sanata Abdullahi Adamu ya ajiye muƙamin. An dai kwashe lokaci ana raɗe-raɗin taɓarɓarewar dangantaka tsakanin sa da shugaba Bola Tinubu.

Haka nan ma sakataren jam'iyyar na ƙasa, Iyiola Omisore.

Jim kaɗan bayan saukar Sanata Adamu ne aka naɗa mataimakin shugaban APCn na yankin Arewa, Sanata Abubakar Kyari a matsayin shugaban riƙo.

Sai dai tun daga lokacin ne hankula suka karkata wajen ɗan siyasa na gaba da za a ba shugabancin APC har zuwa lokacin da za a yi babban taronta na ƙasa.

Da yammacin ranar Laraba gwamnonin jam'iyyar ta APC suka yi wata ganawar sirri a Abuja, babban birnin ƙasar.

Bayanai sun nuna cewa an yi taron ne domin tattaunawa a kan makomar jam'iyyar bayan ajiye aikin Sanata Adamu da sakataren jam'iyyar Iyiola Omisore.

Taron gwamnonin, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC Sanata Hope Uzodinma, ya samu halartar gwamnonin jihohin Ekiti da Ebonyi da Niger da Benue da Kaduna da Legas da Yobe da Katsina da Kebbi da kuma muƙaddashin gwamnan jihar.

Su wane ne za su iya maye gurbin Sanata Adamu?

A halin yanzu, babu cikakkiyar masaniya kan wanda za a bai wa wannan muhimmin muƙami.

Sai dai wata majiya ta cikin gida ta tabbatar da cewa tabbas ana shirye-shirye na ƙarshe don ayyana ɗaya daga cikin manyan ƴaƴan jam'iyyar a matsayin wanda zai riƙe muƙamin.

Amma bayan tattaunawar da gwamnonin APC suka yi a ranar Laraba, wasu daga cikin gwamnonin sun gana da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kuma maƙasudin ganawar ita ce zaɓen ɗaya daga cikin wadanda ake ganin su ne suka fi dacewa da riƙe muƙamin.

To amma su wane ne ake ganin za su samu damar ɗarewa kan wannan muƙami?

Abdullahi Umar Ganduje

Sunan Abdullahi Umar Ganduje ya shiga jerin waɗanda ake tunanin za su maye gurbin Abdullahi Adamu ne bayan ganawar da gwamnonin APC suka yi ranar Laraba.

Bayanai sun ce a ƙarshen ganawar, sunan Abdullahi Ganduje na cikin waɗanda suka fito a gaba-gaba cikin mutanen da ake sa ran za su karɓi muƙamin.

Kuma tuni kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewar ya gana da shugaba Bola Tinubu kan batun.

Gabanin hakan dai ana ta ce-ce-ku-ce kan ko sunan tsohon gwamnan na Kano, kuma ɗaya daga cikin manyan na-hannun daman shugaban ƙasar, yana cikin waɗanda Tinubu zai bai wa muƙamin minista, musamman saboda rawar da ya taka tun farko wajen samun nasarar shugaban ƙasar a zaɓen 2023.

Ganduje na cikin jiga-jigan APC ƙalilan da suka fara kiraye-kirayen a mayar da takara kudancin Najeriya, sashen da Tinubu ya fito, kuma suka ci gaba da rajin ganin takarar Tinubu ta samu karɓuwa.

Tun bayan saukar sa daga maƙamin gwamnan jihar Kano, ana yawan ganin Ganduje tare da shugaba Tinubu, wani abu da ya rinƙa janyo muhawara a kan rawar da zai taka a majalisar zartaswar ta Tinubu.

Tanko Almakura

Almakura na cikin manyan ƙusushin APC da suka yi takarar shugabancin jam'iyyar a 2022, gabanin babban zaɓen ƙasar.

A wancan lokaci, tsohon gwamnan na Nasarawa ya shiga jerin ƴan takarar da suka janye wa Sanata Abdullahi Adamu a lokacin taron jam'iyyar na watan Maris ɗin 2022.

Kuma ya kasance cikin waɗanda ake ganin suna da ƙarfin faɗa-a-ji, sannan shi da tsohon shugaban jam'iyyar Abdullahi Adamu duk sun fito ne daga jihar Nassarawa da ke Arewa ta tsakiyar Najeriya.

Idan har za a bar muƙamin a yankin na Arewa maso tsakiya, ana ganin Tanko Almakura zai iya zama sahun gaba na 'yan siyasar da za su iya samun muƙamin.

Sanata Sani Musa

Sani Musa, wanda ya fito daga jihar Neja na cikin waɗanda suka nemi shugabancin APC a baya, yana cikin jiga-jigan 'yan siyasa a majalisar dattijan Najeriya.

Ya nemi kujerar shugaban Majalisar Dattijai a majalisa ta 10.

Rabon muƙamai tsakanin shiyyoyin ƙasa

Ɗaya daga cikin muhimman abubuwan da ke jan hankali tun bayan tsayar da Bola Tinubu da Kashim Shettima a matsayin ƴan takara kafin zaɓen 2023 shi ne yadda za a tabbatar da raba-daidai a muƙaman siyasa tsakanin yankunan ƙasar da kuma addinai.

Ɓangaranci da bambancin addini na taka muhimmiyar rawa a siyasar ƙasar.

Duk da yake, arewa maso tsakiya ba ta cikin yankuna mafi yawan al'umma a ƙasar, amma tana taka muhimmiyar rawa wajen samar da shugabanni a lokutan zaɓe.

Kafin ajiye aikin Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban APC, yankin na tutiya da manyan muƙamai guda biyu a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Wato muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya da kuma na shugaban jam'iyya.

Ɗauke muƙamin shugabancin jam'iyyar daga yankin bayan saukar Abdullahi Adamu, zai bar yankin da muƙamin Sakataren Gwamnatin Tarayya kacal.

Source: BBC