Menu

Wanne sauyi sabbin shugabannin riƙo 13 za su kawo wa Kano Pillars?

Kano Pillars ta samu sabbin mambobin da za su ja ragamar kungiyar

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Gwamnatin jihar Kano ta naɗa shugabannin riƙo na Kano Pillars da za su ja ragamar ƙungiyar.

Babangida Little ne zai ja ragamar shugabancin Pillars da taimakon mambobi 12, don mayar da ƙungiyar gasar Firimiya ta ƙasa.

Pillars wadda ake yi wa taken "Sai Masu Gida" na buga ƙaramar gasar tamaula ta Najeriya, bayan faɗuwar ta daga Firimiya a bara.

Ranar Laraba za a gabatar da shugabannin, daga nan su karɓi ragamar aiki da nufin ciyar da ƙungiyar gaba.

Jerin mambobin da za su ja ragamar Kano Pillars.

1. Babangida Little, Chairman

2. Garba Umar, Member

3. Naziru Aminu Abubakar, member

4. Bashir Chilla, member

5. Ali Nayara Mai Samba, member

6. Shuaibu Ibrahim Doguwa, member

7. Rabiu Pele, member

8. Muhammed Danjuma, member

9. Sabo Chokalinka, member

10. Abba Haruna (Dala FM), member

11. Engr. Usman Kofar Na'isa

12. Yakubu Pele, member

13. Comrade Sani Ibrahim Coach, Secretary

Kano Pillars tana buga gasar Super Eight, wadda za ta ba ta damar samun gurbin komawa babbar gasar tamaula ta Najeriya.

An kafa ƙungiyar Kano Pillars ne a 1990, kuma ta lashe Firimiya lik huɗu, sannan ta zo ta biyu a 2009/10, ta kuma dauki FA Cup biyu da kuma Nigerian super cup a 2008.

Source: BBC