BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Wanne tasiri mata da matasa za su yi a zaɓen shugaban Turkiyya?

Mabiyan shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdoga

Wed, 10 May 2023 Source: BBC

"Idan Recep Tayyip Erdogan ya sake yin nasara, rayuwa za ta yi masa zafi'' kamar yadda Perit ta shaida wa BBC.

Perit na ɗaya daga cikin ɗaliban fitacciyar jami'ar Bogazic ta Turkiyya da suka yi zanga-zangar nuna adawa da naɗin shugaban tsangayar karatu da ke goyon bayan gwamnati.

An tsare ɗalibin mai shekara 23 a gidan yari har na tsawon kwanaki 94. Ya kuma fuskanci kaɗaici, sannan aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya da rabi, kafin daga bi sani a jingine hukuncin.

Sau ɗaya Perit ya taɓa yin zaɓe a rayuwarsa, to sai dai abokan karatunsa Sude da Emru, wannan ne karo na farko da za su yi zaɓen a rayuwarsu, kuma dukkansu ba su san wani shugaba a Turkiyya ba, face Erdogan.

Emru ya ce rayuwa na ƙara yi wa matasa wahala a Turkiyya saboda ƙaruwar hauhawar farashi, wanda a yanzu ya kai kashi 44 cikin 100.

"Kuɗin karatu sun yi wahala, kuma dole sai ka samu aiki na dindindin kafin ka samu abin rufin asiri, maimakon aikin wucin gadi, kamar yadda ake yi a wasu ƙasashen'', in ji shi.

Sude ta yi ƙorafi kan rashin mutunta 'yancin faɗar albarkacin baki a ƙasar.

''Zan fuskanci matsala, idan na bayyana ra'ayina ko na fadi albarkarcin bakina''.

''Saboda a duk lokacin da na faɗi wani abu, to nakan fuskanci barazana'', in ji ta.

Ta ƙara da cewa a baya, an taɓa yanke mata hukuncin ɗaurin wata 12 a gidan yari, wanda daga baya kotun ta soke, saboda ta halarci wata zanga-zanga a jami'ar Bogazici.

Sun ce jam'iyyar adawa za su zaɓa a babban zaɓen ƙasar da ke tafe.

Perit ya yi amanna cewa lokacin samun sauyi a ƙasar ya zo.

"A lokacin tsawon mulkinsa na shekara 20, Mista Erdogan da jam'iyyarsa sun yi ƙoƙarin kafa kansu ta hanyar zama masu ƙarfin faɗa-a-ji,", in ji Emru.

"Tsawon shekaru 20, ina ga lokaci ya yi za a samu sauyi.

Mutane sun fahimci dimokraɗiyya da 'yancin ɗan'adam, in dai Erdogan ya sake cin zaɓe, wannan zai zama zaɓe na ƙarshe a rayuwarmu."

Turkiyya za ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisar dokokin ƙasar ranar 14 ga watan Mayun da muke ciki, kuma ana tunanin takarar shugabncin ƙasar za ta zama mai zafi.

Shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan wanda ke kan karagar mulki tun a 2003, wanda ya faro a matsayin firaminista, kafin ya zama shugaban ƙasa, zai fuskanci babban ƙalubale daga babban abokin hamayyarsa Kemal Kilicdaroglu.

Ana kallon matasa sabbin masu kaɗa ƙuri'a kusan miliyan biyar a matsayin waɗanda za su yanke hukunci kan mutumin da zai yi nasara a zaɓen.

To amma a ganin Salih mai shekara 20, Recep Tayyip Erdogan shugaba ne da yake da farin jini tsakanin al'ummar ƙasar, kuma yana ganin cewa Turkiyya na buƙatar samun shugaba kamar Erdogan.

Yana da yaƙinin cewa shugaban zai ɗora a kan ayyukan alhairin da ya faro.

"Za a ci gaba da zuba jari don bunƙasa tattalin arzikin ƙasarmu.

A baya mun fuskanci matsalolin makamashi, kuma ƙasarmu ta dogara ne kan ƙasashen waje musamman game da ayyukan soji. Amma a yanzu muna ƙera motocinmu da jiragen sama da jirage marasa matuƙa.

Erdogan ya magance mana matsalolinmu''.

Duka 'yan takarar shugaban ƙasar na ƙoƙarin samun karɓuwa a zukatan matasa.

Shugaba Erdogan na ƙara mayar da hankali kan ci gaba a fannin tsaro da fasaha, yayin da shi kuma mista Kilicdaroglu ke yi wa matasa alƙawarin samun 'yancin faɗar albarkacin baki da ayyukan yi.

Ɗaya daga cikin sauye-sauyen da Erdogan ya ɓullo da su, shi ne soke haramcin sanya ɗan kwali ga ɗalibai da ma'aikata mata a wasu sassan ƙasar.

"A yanzu malamai da likitocinmu da injiniyoyi mata suna iya ɗaura ɗankwali, wannan abin a yaba ne kan 'yancin da Erdogan ya ba mu, ba don shi ba, da har yanzu ana azabtar da mu,'' in ji Gizem says.

A shekarar da ta gabata, Mista Kilicdaroglu ya gabatar da wani ƙuduri a majalisar dokokin ƙasar wanda zai bai wa mata ma'aikata 'yancin sanya danƙwali.

Matakin da Erdogan ya sa aka kaɗa ƙuri'ar raba gardama a kansa.

Akwai ƙarin wasu 'yan takarar biyu a zaɓen, waɗanda suka haɗar da Muharrem Ince da Sinan Ogan.

Ƙuri'un jin ra'ayin jama'a na baya-bayan nan sun nuna cewa waɗannan 'yan takara na neman ƙuri'un matasa, matakin da babbar jam'iyyar adawa ke kallo kamar ƙwacen magoya baya ne.

Duk ɗan takarar da ya samu fiye da rabin ƙuri'un da aka kaɗa, shi ne za a ayyana a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasar, matuƙar ba a samu haka ba, to sai an je zagaye na biyu.

Ana kallon matakin da mata za su ɗauka wajen kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen a matsayin wani abu muhimmi, kasancewar su ne kashi 50.6 cikin 100 na masu zaɓe a ƙasar.

Masu sharhi na ganin cewa goyon bayan mata ne ya bai wa Shugaba Erdogan nasara shekaru 20 da suka gabata, to sai dai a yanzu ana ganin farin jininsa a wajen matan na ci gaba da raguwa.

Matakin da Erdogan ya ɗauka na fitar da Turkiyya daga 'Istanbul Convention' wata yarjejeniyar da ke yaƙi da cin zarafin mata, lamari ne da ya haddasa zanga-zanga a ƙasar.

A baya, ya bayyana matan da ba su taɓa haihuwa ba, da cewa ba su "cika mata ba", tare da shawartar mata su haifi a ƙalla 'ya'ya uku, sannan ya ce maza da mata ba za su taɓa zama ɗaya ba.

Ƙawancen - da ya yi da jam'iyyar masu tattsauran ra'ayin addini a zaɓen baya-bayan nan da ya ba shi nasara - ya haifar da damuwa tsakanin mata 'yan majalisar dokoki na jam'iyya mai mulki.

Source: BBC