BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Wasa shida da ke gaban Man United a Premier League

Kocin Manchester United Ten Hag

Wed, 6 Sep 2023 Source: BBC

Kungiyar Manchester United tana mataki na 11 a teburin Premier League bayan kammala wasa hudu da fara kakar bana 2023/24.

Maki shida take da shi bayan nasara a kan Wolverhampton da Nottingham Forest, yayin da Tottenham da Arsenal suka doke ta.

Kungiyar na fama da 'yan wasan da ke jinya, amma yanzu da akwai maki 100 nan gaba da za ta yi kokarin samu, domin taka rawar gani a kakar nan.

Wannan makon ana hutu, bayan da kasashe za su buga wasannin neman shiga gasar kofin Afirka ko nahiyar Turai ko kofin duniya ko kuma na sada zumunta.

United tana cikin rukunin farko a Champions League da ya hada da Bayern Munich da FC Kobenhavn da kuma Galatasaray.

Haka kuma a kakar nan kungiyar ta Old Trafford za ta kare kofinta na Carabao da ta lashe a bara, bayan cin Newcastle United.

United za ta buga wasan Premier da Brighton ranar 16 ga watan Satumba a Old Trafford, sannan ta ziyarci Bayern Munich ranar 20 ga watan Satumba a karawar Champions League.

Wasa shida da ke gaban Manchester United a Premier League:

Asabar, Satumba 16 da Brighton a Old Trafoord

Asabar, Satumba 23 da Burnley a Turf Moor

Asabar, Satumba 30 da Crystal Palace a Old Trafford

Asabar, Oktoba 7 da Brentford a Old Trafford

Asabar, Oktoba 21 da Sheffield United a Bramall Lane

Lahadi, Oktoba 29 da October vs Man City a Old Trafford

Source: BBC