A Jerin wasikunmu daga 'yan jaridar Afirka, wata marubuciya 'yar kasar Ghana Elizabeth Ohene ta yi amfani da damar da ta samu a lokacin barkewar annobar cutar korona wajen fito da wani yayi na kwalliya.
Ban dade da yanke shawara ba game da kamannina.
A'a, ban je likitan fida ya yi min tiyatar gyara tamojin fuskata ba, ban kuma yi yunkurin a yi min kwaskwarimar kwankwasona ba.
A maimakon haka, na rika yawo da gashina - mai cike da furfura a bude.
A shekara 76 ba wani abin bayar da labari ba ne cewa ina da furfura ko farin gashi, amma a gaskiya, ya kasance wani mataki na ban mamaki.
Lokacin da za ka iya gane shekarun macen kasar Ghana shi ne ta yadda ta mayar da gashin kanta.
Ya zuwa shekara 16 zuwa 17, budurwa kan rika barin gashin a gajarce. Daga nan ne za ta iya yin kitso ko kuma ta yi adon gashinta irin yadda take so.
Karshen furfura ko farin gashi
Matasa da magidanta kan saisaye gashin kansu, ko shakka babu, lokacin yayin tara suma da aka fi sani da "Afro" ya zama tsohon yayi.
Idan ana batun launi kuwa, gashin kan kowa kan kasance baki ne tun daga ranar haihuwa har ya zuwa tsufa.
Amma ya zuwa wani lokaci wannan al'ada ta sauya.
Bani da tabbaci kan lokacin da aka fara shigo da amfani da shuni a gashi a tsakanin al'ummar kasar Ghana - a wani lokaci cikin shekarar 1950, haka na ji ana fada.
An yi masa lakabi da "yoomo b3 Ga", ko a gajarce zuwa "yoomo", wanda wata kalma ce da ke nufin dattijuwa a harshen Ga na kasar Ghana.
Cikakken sunan shunin ana fassara shi ne da ''babu tsohuwa a birnin Accra''.
Hakan na nuni da yadda bakin shuni ya shiga cikin rayuwa da al'amuran ado da kwalliya da al'adar kasar Ghana.
Babban abin da aka fi gane wanda ya tsufa dai ita ce furfura ko farin gashi, amma a yanzu, saboda bakin shunin, babu tsohuwa ko tsoho a birnin Accra babban birnin kasar Ghana.
Daga nan ne bakin shunin ya samu shiga a kowane lungu da sako na kasar, kuma rububin sha'awar da ake yi wa "yoomo" babban abin mamaki ne.
Launin gashin matan kasar Ghana ya kasance baki tun daga ranar haihuwa har ya zuwa karshen rayuwa.
'Hanya mafi sauki' ta nuna tsufa
Dole a fadi cewa batun sha'awar kasancewa babu furfura ko farin gashi ba wai a mata kadai ya tsaya ba.
Sannu a hankali maza suka rungumi wannan al'ada wadda ta hakan ne aka wayi gari ba za ka iya ganin kowane mutum da farin gashi ba, mace ko namiji ko da kuwa shekarunsu nawa ne.
Sauyin da aka samu ta bangaren yadda mazan kasar Ghana ke mayar da gashinsu ya fi ban mamaki.
Ba dukkaninsu ne ke amfani da bakin shunin gashi ba, suna da hanya mafi sauki ta kauce wa nuna tsufansu.
A saukake, su kan ki barin ko da silin gashi daya a kansu - kwaryar molo ne ya zama adon yayi.
Don haka askin kwal-kwabo ko kuma kwaryar-molo ya warware matsalar zubewar gashi.
Makonni biyu da suka gabata, n afara fita waje da farin gashi na a bude.
Ba ni da tabbaci ko n afara fitar da sabon yayi ne, amma hakan na nufin yanzu za ka iya ganin tsohuwa guda daya - yoomo - ia birnin Accra.