BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Wasu jiga-jigan APC sun motso domin samun shugabancin jam'iyyar

 118089150 Mediaitem118089149 Hoton wasu manyan APC a wani taro da shugaba Buhari a Abuja

Sat, 17 Apr 2021 Source: BBC

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya sun fara wasa wukakensu, don neman shugabancin jam'iyyar.

APC ta shafe tsawon lokaci tana fama da rikicin cikin gida, har ta kaii ga sauke tsohon shubabanta Adams Oshiomhole, kana aka kafa kwamitin riko karkashin jagorancin gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

A watan Yuni mai zuwa ne ake san ran jam'iyyar za ta yi babban taronta na kasa, domin zabar sabbin shugabanni.

Alhaji Mustapha Salihu wanda tsohon matamakin shugaban jam'iyyar CPC na kasa ta shugaba Buhari ne, shine mutum na baya bayan nan da ya bayyana sha'awarsa ta neman shugabancin jam'iyyar.

Ya bayyanawa BBC cewa lokaci ya yi, da ya kamata dattawan da suka kankane jagorancin jam'iyyar su matsa su bawa matasa dama domin ciccibata ga turbar sake samun nasara a zabukan 2023.

Ko da yake har yanzu APC bata yanke hukunci a kan shiyyar da za ta mikawa jagorancinta ba, tuni 'ya'yanta daga kowanne yanki suka fara fitowa sun nuna sha'awarsu, musamman ma tsofaffin gwamnoni.

Tsohon gwamnan jihar Zamfara Abdul'aziz Yari, daga arewa maso yammacin Najeriya na kan gaba wajen neman shugabancin jam'iyyar, kuma yayin wata tattaunawa da BBC Hausa a baya bayan nan, ya ce ya riga ya fito neman shugabancin, abin da ya kawo karshen rade radin da ake yi.

Daga shiyyar Arewa maso gabas Akwai kuma tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima, wanda shima ake ganin yana da sha'awar darewa shugabancin jam'iyyar, duk da cewa Sanata ne mai ci a halin da ake ciki.

A arewa ta tsakiya kuwa tsohon gwamnan jihar Nassarawa Umaru Tanko Almakura wanda shima sanata ne mai ci a halin da ake ciki, na daga cikin wadanda aka rawaito cewa suna hankoron kujerar shugabancin jam'iyyar APCn ta kasa.

A halin da ake ciki dai gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni ne ke jagorantar kwamitin riko na jam'iyyar da zai gudanar da babban taronta na kasa, inda za a zabi sabbin shugabanni.

Source: BBC