Ranar Laraba Arsenal za ta karbi bakuncin Manchester City a kwantan wasan Premier League karawar mako na 12.
Arsenal mai maki 51 tana ta daya a kan teburi da tazarar uku tsakaninta da City ta biyu mai 48.
Sai dai watakila Erling Haaland ba zai buga wasan ba, bayan da ya ji rauni a fafatawar da City ta doke Aston Villa 3-1 a Etihad ranar Lahadi a Premier League.
Haaland wanda ya ci kwallo 25 a babbar gasar tamaula ta Ingila a bana, an sauya shi a wasan Lahadin lokacin da City ke cin 3-0.
Kociyan City Pep Guardiola ya fada cewar ''Erling ya samu buguwa, bai jin kazar-kazar.''
Kungiyar Etihad za ta koma kan teburi idan har ta doke Arsenal a Emirates ranar Laraba.
Arsenal ta ci karo da cikas a Premier, wadda Everton ta doke ta 1-0 a Goodison Park, sannan ta tashi 1-1 da Brentford ranar Asabar a Emirates.
To sai dai City ba za ta yi rashin Haaland ba koda bai buga mata wasan ba, domin bai ci kwallo ba a karawa hudu baya a waje a dukkan fafatawa.
A wasan Premier League da Tottenham ta ci City 1-0, Haaland bai buga kwallo ya nufi raga ba ko sau daya, kenan baya yin kokari sosai.
Rabon da Haaland ya ci kwallo tun ukun da ya zura a ragar Wolves ta City ta ci 3-0 ranar 22 ga watan janairun 2023.
City ta doke Arsenal 1-0 a FA Cup ranar 27 ga watan Janairun 2023 a Etihad.