BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yadda ambaliyar ruwa ta kashe mutum 500 a Najeriya

99082250 Hoton alama

Wed, 12 Oct 2022 Source: BBC

Hukumomi a Najeriya sun tabbatar da mutuwar akalla mutum 500 sanadin ambaliyar ruwan da take ci gaba da tafka barna a fadin kasar. Mutanen sun mutu ne a makonni kadan da suka gabata. An fitar da wadannan alkaluman ne a wurin taron da hukumomin da ke da ruwa da tsaki kan sha'anin yanayi suna gudanar ranar Talata a Abuja, babban birnin kasar. Taron, wanda Ministan harkokin noma ya jagoranta, ya kara da cewa baya ga mutuwa, ambaliyar ruwan ta kuma yi sanadin rushewar gida 45,249. Kazalika hukumomin sun ce ambaliyar ruwan ta lalata hekta 70,566 na gonaki a fadin kasar, tana mai gargadin cewa akwai yiwuwar matsalar za ta ta'azzara. 'Yan kasar dai suna ci gaba da kokawa game da yadda ambaliyar ruwan ta raba su da muhallansu inda a yanzu suke kwana a gine-ginen makarantu da sansanonin 'yan gudun hijira. Rahotanni sun tabbatar da cewa ambaliyar ruwan ta janyo yaduwar cututtuka musamman irin su amai da gudawa da zazzabin cizon sauro. Tuni dai hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar ta ce ta aike da jami'anta yankuna daban-daban domin tallafa wa jama'ar.

Source: BBC