Menu

Ya aka yi jiragen ƙasa uku suka yi hatsari a Indiya?

Hoton jirgin da ya samu hatsari

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

Mummunan hatsarin da ya faru a Jihar Odisha ta Indiya ya kashe aƙalla mutum 275 tare da jikkata wasu fiye da 1,000, bayan ya ritsa da jiragen ƙasa uku.

Har yanzu ba a san musabbabin hatsarin ba, wanda aka ce shi ne mafi muni a Indiya a cikin wannan ƙarnin.

A tsarin titin dogo, layin lantarkin da ya haɗe ilahirin ƙarafan ne ke yi wa jiragen jagora don tabbatar da cewa jirgi zai iya gudu a kan kowane layinsa ba tare da wata matsala ba.

Wani jami'i ya ce kwamashinan kula da harkokin jiragen ƙasa na yankin kudu maso gabas ne zai jagoranci binciken abin da ya faru - yankin ya ƙunshi gundumar Balasore inda tsautsayin ya faru.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton babu cikakken bayanin yadda lamarin ya faru, amma ma'aikatar sufurin jiragen ƙasa ta ce hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 6:55 na yamma a Indiya (ƙarfe 2:55 agogon Najeriya) na ranar Juma'a a kusa da Tashar Bahanga Bazar - kusan kilomita 270 daga kudancin Kolkata.

Hatsarin ya ritsa da jirgin ƙasa uku:

  • Coromandel Express, wanda ya taso daga Shalimar 'yan awanni kafin hatsarin daga jihar Bengal kuma ya nufi garin Chnnai da ke kudancin ƙasar


  • Howrah Superfast Express, wanda ya taso daga tashar Yesvantpur da ke Bengaluru kuma ake jiran ya ƙarasa Howrah


  • Sai kuma wani jirgin dakon kaya da ke tsaye, wanda yake jira a tashar Bahanga
  • An samu rahotanni daban-daban game da wane jirgin ne ya fara gocewa da kuma yadda lamarin ya faru. Amma mai magana da yawun ma'aikatar sufurin jiragen ƙasa Amitabh Sharma ya ce Coromandel Express ne ya fara gocewa daga titinsa.

    Wani jami'in ma'aikatar ya faɗa wa BBC cewa tashar Bahanaga Bazar na da layin dogo huɗu.

    "Akwai jirage a kan layi na 1 da 4 da ke tsaye a kansu. Su kuma layuka na 2 da na 3 akwai jiragen fasinja da ke gudu a kansu a lokaci guda. Bincike ne kawai zai nuna yadda aka yi Coromandel Express ya goce kuma ya afka wa jiragen kayan," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa taragon jirgin da ya goce sun faɗa kan bayan jirgin Howrah Superfast kuma suka gotar da shi.

    Wata sanarwa daga gwamnatin Odisha ta fitar ta ce jimillar tarago-tarago 17 ne suka goce kuma suka lalace.

    Mazauna ƙauyen da kuma waɗanda suka shaida lamarin na cewa jirage uku ne lamarin ya shafa.

    Hatsarin na ranar Juma'a na cikin biyar mafiya muni da suka faru a tarihin layin dogo na Indiya.

    Atul Karwal, shugaban Rundunar Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NDRF), ya ce ƙarfin taho-mu-gama da jiragen suka yi ta sa sai da masu ba da agaji suka yanka taragon kafin su isa ga fasinjoji.

    An tura ɗaruruwa motocin agaji, da likitoci, da malaman jinya zuwa wurin kuma sun shafe awa 18 suna aikin ceto fasinjojin.

    Indiya na cikin ƙasashen da suka fi girman layin dogo a duniya.

    Jirgin fasinja fiye da 12,000 ne ke jigila a kullum, inda dubban mutane ke hawa zuwa sassa daban-daban na ƙasar - sai dai kuma da yawa daga cikin titunan na buƙatar gyara.

    Source: BBC