BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yaƙin Gaza : Afirka ta Kudu ta kai ƙarar Isra'ila Kotun Duniya

87144139 Cyril Ramaphosa, shugaban Afrika ta kudu

Mon, 1 Jan 2024 Source: BBC

Afirka ta Kudu ta shigar da ƙara a gaban Kotun Duniya (ICJ) kan zargin Isra'ila da aikata laifukan kisan-kiyashi a Gaza.

Sai dai Isra'ila ta yi watsi da zargin da cewa ba shi da tushe kuma tsabagen raini ne ga kotun.

Bayan shigar da ƙarar a wata sanarwa da ta fitar fadar gwamnatin Afirka ta Kudun ta ce ta yi hakan ne domin alhaki ya rataya a wuyanta na ta dakatar da faruwar kisan-kiyashi.

Kuma ta ce ƙarar da ta shigar ta nemi Kotun ta Majalisar Dinkin Duniya da ta ayyana cewa Isra’ila ta saɓa dokokin kisan-kiyashi na majalisar.

A takardar mai shafi 84 da Afirka ta Kudun ta shigar da ƙarar ta nemi da kotun ta zauna zaman sauraren ƙarar a mako mai zuwa tare da buƙatar kotun ta ayyana wasu matakai da suka haɗa da sanya Isra’ila ta dakatar da duk wasu ayyuka na soji a Gaza.

Afirka ta Kudu na sukar lamirin Isra'ila sosai inda a watan da ya gabata shugaban ƙasar Cyril Ramaphosa ya ce Isra'ila na aikata laifukan yaki a Gaza.

A farkon watan Nuwamba Afirka ta Kudun ta janye dukkanin jami’anta na diflomasiyya daga Isra’ila, abin da ita ma Isra’ilar ta mayar da martani da janye jakadanta daga Pretoria.

Bugu da ƙari majalisar dokokin Afirka ta Kudun ta kaɗa ƙuriar ƙasar ta dakatar da duk wata hulɗar diflomasiyya da Isra’ila to amma har zuwa yanzu gwamnatin ba ta yi hakan ba.

Sannan a baya ma Afirka ta Kudun ta shigar da ƙara a gaban kotun hukunta manyan laifuka ta duniya, ICC a kan laifukan da take zargin Isra'ila da aikatawa na yaƙi a Gaza. Sai dai Isra’ila ba ta yarda da kasancewar kotun ba.

A martanin Isra’ilar kan ƙarar ta kotun duniya, kakakin ma’aikatarta ta harkokin waje Lior Haiat ya ce iƙirarin na Afirka ta Kudu tsabar raini ne ga kotun.

Ya kuma ce Afirka ta Kudu na haɗa kai ne da ƙungiyar ta’addanci da ke kira da a kawo ƙarshen ƙasar Isra’ila.

Sannan ya ce Hamas ce ke da alhakin mawuyacin halin da Falasdinawa ke ciki a Gaza ta hanyar amfani da su a matsayin kariya da sace kayan tallafin da ake kai musu.

Zuwa yanzu dai hare-haren Isra'ila a Gaza sun yi sanadiyyar mutuwar sama da mutum 21,500 a Gaza yawancinsu yara da mata a tsawon makonnin, yakin kamar yadda ma’aikatar lafiya ta Gaza ta bayyana.

Harin da Hamas ta kai wa Israila ranar 7 ga watan Oktoba, inda ta kashe mutum 1,200 tare da garkuwa da wasu 240 shi ne ya buɗe babin hare-haren na Israila a kan Gaza.

Kotun ta Duniya wadda ke zaune a birnin Hague na Netherlands aikinta shi ne sasantawa ko shiga tsakani a rikicin ƙasashe tare da bayar da shawara a kan batutuwan da suka jiɓanci shari'a ta duniya.

Source: BBC