Menu

Ya kamata a binciki shugaban EFCC — Matawalle

Shugaban EFCC Abdurrashid Bawa da tsohon gwamnan Zamfara, Bello Matawalle

Fri, 19 May 2023 Source: BBC

Bayan da hukumar EFCC a Najeriya ta fitar da sanarwa cewa tana binciken gwamnan jihar Zamfara Mohammed Bello Matawalle, kan zargin wawure kudin jihar fiye da Naira biliyan 70, gwamnan ya zargi shugaban hukumar Abdurrashid Bawa da tafka almundahana iri-iri.

A cikin wata hira da BBC, gwamnan ya kalubalanci Bawa da ya sauka daga kan kujerarsa ya ba da damar a bincike shi ya ga irin abubuwan da za a bankado.

Gwamna Matawalle, “ Bincike gaskiya ne, ba a hana ayi bincike ba, amma kuma yakamata binciken ya zamo na kowa da kowa, don bai kamata ace komai sai dai a a ambaci gwamna ba, ai ba gwamna ne kadai ke da asusun ajiya ba.”

Ya ce, “ Kamar yadda shugaban EFCC ya ce ya tanadi takardu na gwamnoni, to muna so ya nunawa duniya takardu na wadanda yake aiki tare da su, sannan shi kansa yakamata ya rubutawa kansa takarda don a bincike shi saboda akwai zarge zarge masu dumbin yawa a kansa.”

Gwamnan ya Zamfara, ya ce “Akwai shaidu da dama wadanda idan ya sauka za a fito da su a gwadawa duniya cewa shi bam ai gaskiya bane.”

Ya ce ‘’ Ya sauka ya gani duk wadanda ke da wata shaida a kansa za su kawo a cikin lokaci kalilan.”

Gwamna Matawalle, ya ce ‘’ Akwai abin da shi shugaban EFCC ya sanya ya yi tsakaninsa da ni, ya san abin da ya roka ban bashi ba a kan haka ya sani gaba.”

To itama hukumar ta EFCC ta kalubalanci gwamnan jihar Zamfarar, Bello Matawalle kan cewa idan yana da hujja a kan cewar shugabanta, Abdulrasheed Bawa na da hannu a ayyukan rashawa to ya kai kara wajen ‘yan sanda.

Koda BBC ta tuntubi shugaban hukumar Malam Abdulrasheed Bawa, ya ce ai babu wani dan Adama da yake 100 bisa 100 a duniya.

Ya ce, ‘’ Amma dai gwargwadon hali wadannan maganganu da gwamna Matawalle ya ke wane ya yi kaza ai sai ya fadi.”

Shugaban na EFCC ya ce, ‘’ Idan ya san da wani gwamna ko minista da ya yi wani abu ya zo ya kawo, idan kuma ya ga cewa ni na yi wani abu ai akwai ‘yan sanda da wuraren da zai iya rubuta kara sai ya kai idan ya so sai a bincike ni, in ya so sai a gano wanda ke da gaskiya.”

An dai shiga takun saka tsakanin gwamnan da EFCC ne bayan da hukumar ta ce ta aike da goron gayyata ga wasu gwamnoni da za su sauka a karshen watannan domin ta bincike su.

Daga cikin gwamnonin har da gwamnan na Zamfara Mohammed Bello Matawalle, inda ake zarginsa da wawure kudin jihar fiye da Naira biliyan 70.

Source: BBC