A Najeriya, yayin da gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi ke kokarin samar da tallafin abinci ga al'ummar kasar bayan cire tallafin man fetur, masu sharhi na ganin matakin na wucin-gadi ya dace amma matakin din-din-din zai fi dorewa.
Barista Bello Galadi, tsohon shugaban reshen kungiyar lauyoyi ta Najeriya (wato NBA) a jihar Zamfara, ya shaida wa BBC cewar tunanin bayar da tallafin abin a yabawa gwamnatin tarayya ne idan aka yi la`akari da halin da talaka ya shiga na yunwa da fargaba da tashin hankali.
Barista Bello Galadi ya ce ''Na fahimci wannan mataki ne na wucin gadi, shi ko al`amari irin wannan ya kamata ya zamo mataki ne na din-din-din''.
Ya ce, ''Matsalolin da suka jefa talaka cikin wannan yanayi, sun hada da rashin tsaro wanda ya haifar da tabarbarewar harkokin noma, akwai kuma rufe iyakokin kasa wanda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kaddamar da nufin samar da tsarin wadata kasa da abincin cikin gida tsarin da ya dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen waje''.
Barista Bello ya kara da cewar ''Daga wannan lokacin aka shiga wahala a Najeriya, na yar da cewar tsari ne mai kyau a samar da abinci ingantacce to amma tsarin da aka bi wajen kaddamar da shirin shi ya jefa talaka cikin kunci''