Menu

'Ya’yan yayana suna maƙale ni amma dole na tafi na bar su a Sudan

A ranakun Laraba da Alhamis ne jirgin saman RAF ya kai ‘yan kasar Burtaniya da ke Sudan zuwa Cyprus

Thu, 4 May 2023 Source: BBC

Wata ‘yar Burtaniya da ta tsere wa rikicin Sudan ta bayyana yadda aka ɗauketa daga ƙasar lokacin da take tsakiyar ‘ya’yan yayyenta da suke kuka suna riketa domin kar ta tafi.

Waafa Salim ta tattauna da BBC a filin jirgin Larnaca da ke Cyprus, inda jiragen Burtaniya ke sauka idan suka tashi daga Sudan gabanin su ƙarasa ƙasarsu.

Ba a amince mata ta tafi da yaran ba saboda dokokin da Burtaniyan ta shimfiɗa na kwaso mutanen.

“Dolena na miƙa su ga mahaifinsu. Wani mummunan lokaci da ba zan manta ba,” in ji ta.

‘‘Ƙananan yara ne da ba su da kariya kamata ya yi a ce an kyale ni na tafi da su cikin jirgi.

‘‘Sun shaida min ba zan iya ɗaukarsu ba saboda ƙa’idar da aka sanya, sai mai fasfo ɗin Burtaniya ne kawai za a ɗauka. Na roƙe su na ce 'ya'yana ne, amma suka ce hakan ba zai yiwu ba.”

Fadar mulki ta Downing Street ta zayyana wasu sharuɗa waɗanda ta ce ba za a sauya su ba, amma an ba su wuƙa da nama na yanke shawara kan abin da suke gani a zahiri a can Sudan ɗin.

Ofishin harkokin wajen Burtaniya ya ce jirage takwas da suka tashi sun kwaso mutum 897 daga ƙasar da ke gabashin Afrika zuwa Cyprus a ranar Alhamis.

Amma duk da haka wannan wani adadi ne da bai taka kara ya karya ba na yawan ‘yan Burtaniya da ke Sudan.

Misis Salim wadda mai tsare-tsare ce a wani ofishi da ke Buckinghamshire, ta je arewacin Sudan, inda tace mutane ke samun taimakon Ƙungiyar ba da agajin ta Red Cross.

Ta je Sudan ne da ɗanta Hasan mai shekara 12, wata ziyara da ta kai wa ‘yan uwanta a lokacin sallah ƙarama.

Ya kamata a ce sun koma Burtaniya a makon da ya gabata, amma yaƙin da aka soma ya haifar da tsaiko gare su.

‘Abin firgici ne da tashin hankali’

Ta samu damar tsallake shingen duba ababan hawa da yawa da ɗanta da ɗan uwanta, tare da 'ya'yansa da suke tsakanin shekara 3 -10.

Amma bayan ta tattauna da wakilan Burtaniya ne aka mayar da ɗan uwanta da 'ya'yan nasa.

“A dokar da suka bayar sun ce ‘ya’yan cikinmu kawai za mu iya fita da su,” in ji ta.

“Waɗannan yaran da ba su san komai ba ku kyale su tare da ni. Shi ɗan uwana ya zauna, amma suka ƙi.”

Ta ce yanzu ɗan uwan nata da iyalansa na ƙoƙarin barin ƙasar ta kan iyakar Masar, ta ƙara da cewa da babu yara da tafiyar ta fi masa sauƙi.

A yanzu haka, duk wani mai fasfo ɗin Birtaniya da iyalansa ko kuma mai shaidar zama a ƙasar zai iya samun damar a ɗauke shi.

Da yake magana tun da fari, sakataren harkokin wajen Birtaniya James Cleverly ya ce duk ɗan Sudan ɗin da ba shi da takardun zama a ƙasar kada a bari ya wuce shingen tantance mutane.

“Lokacin da aka samu ɗan Birtaniya na auren ‘yar Sudan kuma suna da ‘yaya, sai mu rasa yadda za mu yi,” in ji shi.

“Ya shawarci ‘yan Birtaniya da su gaggauta tattara nasu ya nasu su fice daga ƙasar domin ba a san mai zai faru ba da lokacin yarjejeniyar ya ƙare.

Jami’ai a Birtaniya suna ci gaba da tuntuɓar ɓangarorin biyu, kan su daure su tsawaita wannan yarjejeniya ta tsagaita wuta tsakaninsu.

Da yake magana a gaban majalisa sakataren harkokin waje David Lammy ya yi kira ga gwamnati ta kyale ‘yan Sudan da ke da shaidar zama a Burtaniya su bar ƙasar.

A tare da Misis Salim akwai ɗanta mai shekara 12 Hasan, wanda ya riƙa fama da ƙarancin barci a makon jiya sakamakon ƙarar bam da harbe-harben bindiga.

Ya ce abin takaici ne ka bar 'yan uwanka, cikin wannan matsala, kuma yana tsammanin ya tafi gida ya samu iyalansa cikin farin ciki.”

An shaida wa BBC cewa sai da aka kai Misis Salim asibiti saboda rashin lafiya da ya kamata a jirgi.

Source: BBC