Menu

Yadda Shugaba Biden ya yi tuntuɓe sannan ya faɗi a bainar jama'a

Shugaba Biden bayan ya fadi

Fri, 2 Jun 2023 Source: BBC

Shugaba Joe Biden ya yi tuntuɓe sannan ya faɗi a lokacin da yake bada takardar shaidar kammala karatu a makarantar horar da sojojin sama ta Amurka da ke Colorado.

Mista Biden, wanda shi ne shugaban ƙasar da ya fi tsufa a kan karagar mulki na ƙasar yana da shekara 80, an ga jami'an sojin sama sun taimaka masa a lokacin da ya tashi amma da kafarsa ya taka ya koma kan kujerarsa.

Shugaban ya kwashe kusan sa'a ɗaya da rabi a tsaye yana gaisawa da kowanne daga cikin ɗaliban da suka kammala karatu, su 921.

Daraktan sadarwa a fadar White House ya ce "shugaban yana nan cikin koshin lafiya".

"Akwai jakar yashi kan dandamalin a lokacin da ya ke gaisuwa", a cewar Ben Labolt a shafin Tuwita bayan faɗuwar da ya yi a ranar Alhamis.

'Wannan ba farau ba'

Hotunan faruwar al'amarin sun nuna Mista Biden yana nuna jakar yashin a lokacin da aka taimaka masa tashi daga kasa.

An gan shi yana gudu a lokacin da zai koma ayarin motocinsa, kuma babu wata alamar ya ji rauni ba, a lokacin da aka kammala bikin, jim kadan bayan faruwar al'amarin.

Wani ɗan jarida da ke cikin tawagar ta shugaba Biden ya ce shugaban bai amsa tambayoyi ba a lokacin da ya koma jirginsa.

Sakatariyar yaɗa labaran fadar White House, Karine Jean Pierre ta ce Mista Biden na cikin "koshin lafiya" kuma ya shiga cikin jirgin yana kyalkyali da "murmushi".

Masu suka sun ce Mista Biden ya tsufa ya tsaya takarar shugaban kasa a wa'adi na biyu.

Kuri'ar jin ra'ayoyin jama'a ta baya-baya nan ta nuna cewa akasarin masu kaɗa kuri'a a Amurka sun damu da yawan shekarunsa.

Zai kasance mai shekaru 82 a farkon wa'adinsa na biyu idan ya yi nasara a zaɓen.

Wannan faɗuwar da tuntuɓe da ya yi a baya da suka haɗa da na kekensa da kuma hawa kan matakalar jirgin saman shugaban ƙasar Amurka wato 'Airforce one', watakila suna cikin abubuwan da ke janyo damuwa.

Tsohon shugaban kasa, Donald Trump wanda shi ne ɗan takarar jamiyyar Republican da zai kalubalanci shugaba Biden a zaɓen 2024, ya yi magana a kan a'lamarin a wani taron yaƙin neman zaɓe a Iowa.

"Ina fatan bai ji rauni ba", inji Mista Trump, mai shekara 76, wanda ya sha yin ba'a akan shekarun Mista Biden. "Wannan ba abin burgewa bane".

Mista Trump ya kara da cewa: "Akwai ruɗani a cikin al'amarin... ko da ya ya kamata a ce ka taka ne sannu a hankali," da alama yana magana ne akan irin tafiyar da ya yi a lokacin da zai sauka kan dandamali abinda a gidajen jarida suka wallafa a kanun labarai a 2020.

Ya ce a wancan lokaci kasan ɗakin taron Kwalejin horar da sojoji Amurka da ke West Point a New York ya yi tsantsi kuma ya yi watsi da tambayoyin da kafafen yaɗa labarai ke yi gameda lafiyarsa a matsayin labaran karya.

A watan fabrairu ne aka yi wa Mista Biden gwajin lafiyarsa.

Likitan fadar White house Dr Kevin O’Connor ya rubuta a wancan lokaci cewa: shugaban ya na cikin koshin lafiya kuma zai iya aiwatar da ayyukansu.



Source: BBC