BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yadda aka kashe mutum bakwai a hari kan jami'an jakadancin Amurka

58529780 Hoton alama

Fri, 19 May 2023 Source: BBC

Hari kan ayarin Jami'an Ofishin Jakadancin Amurka a Anambra a ranar Talata 16 ga watan Maris ɗin 2023, ya tabbatar da yadda rashin tsaro ya yi kama-guri-zauna a jihar da kuma kudancin Najeriya.

Kwamishinan Yan Sandan Jihar ta Anambra, Echeng Echeng, ya bayyana cewar mutane bakwai da suka haɗa da ƴan sanda huɗu da ma'aikatan ofishin Jakadancin uku sun mutu lokacin da aka kai wa kwambar hari a hanyar Atani zuwa Osamala da ke ƙaramar hukumar Ogbaru.

Babu ɗaya daga cikin al'ummar Amurka ma'aikatan Ofishin Jakadancin da ya rasa ransa, amma biyu daga cikin jami'an ofishin sun ɓace, ƴan sanda sun ce ƴan bindigar sun yi awon gaba da su.

Mr Echeng ya ɗora alhakin harin kan ƴan awaren Ipob. Kodayake bai bayar da shaidar da za ta tabbatar da zargin ba.

Amma ya bayyana yadda jami'an tsaro suka yi wa wani sansani da ake zargin na ƴan awaren ne a Ugwuaneocha da ke ƙaramar hukumar Ogbaru ƙawanya amma kuma aka samu sun bar gurin.

Kwamishinan ƴan sandan ya ƙara da cewa sun yi nasarar kama wasu mutane biyu waɗanda a yanzu su ke taimakawa wurin bincike.

Ma'aikatan Ofishin Jakadancin sun taso daga Legas don gane wa idonsu illar da zaizayar ƙasa ta yi a ƙaramar hukumar Ogbaru, yankin da yake fama da matsalar ambaliyar ruwa saboda maƙotaka da River Niger.

Yadda Harin Ya Faru

Wannan ba shi ne karo na farko da ƴan bindiga ko mutanen da ake zargi da ayyukan aware a ƙaramar hukumar ke kai wa ayarin jami'an Ofishin Jakadancin Amurka hari ba.

Shugaban Karamar Hukumar Ogbaru Pascal Aniegbuna, ya shaida wa BBC cewa mazauna garin da abin ya faru sun ce sun fahimci ƴan bindiga sun shiga garin kwanaki biyu kafin harin.

Mista Aniegbuna, ya ƙara da cewar harin ya faru a hanyar da ta ke tsakanin garuruwan Ogbakuba da Umunankwo waɗanda ke kusa da Ofia Umuoga. Ayarin ya haɗa da motoci ƙirar SUV biyu tare da rakiyar motar ƴan sanda.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce yana zargin kwambar ta yi taho mu gama da ƴan bindigar ne ko kuma sun wuce su a hanya abin da ya sa ƴan bindigar su ka biyo bayansu tare da harbin waɗanda su ke cikin motar bayan kunna wa motar wuta duk da gawawwakin da suke cikinta waɗanda za su yi wuyar ganewa.

''Sun kuma tsoratar da mutane da harbe-harbe bayan harin. Mun sanar da kwamandan sojojin ruwa da ke yankin kuma nan take ya aike da sojoji zuwa wurin. Ƴan bindigar sun tsere cikin daji da ganin jami’an tsaro.''

Mista Aniegbua yana zaton ganin jami'an tsaro a tawagar ne ya haifar da harin.

Ya kuma shaida wa BBC cewa ya yi mamakin harin sakamakon an jima ba a fuskanci hari a Ogbaru ba.

To amma sakamakon binciken BBC ya gano wannan shi ne hari na biyu da aka kai wa jami'an Ofishin Jakadancin Amurka a ƙaramar hukumar ta Ogbaru a bana.

Hare-hare a Ogbaru

A ranar 4 ga Maris na shekara ta 2023, an kashe wani ɗan sanda a yankin Atani na ƙaramar hukumar lokacin da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka kai hari wani shingen bincike na jami'an tsaro.

Wani hari da aka kai hedikwatar ƴan sanda a Atani a ranar 13 ga watan Afrilun shekara ta 2022 ya yi sanadin mutuwar ƴan sanda huɗu.

Haka kuma akwai wasu hare-hare da suka faru tsakanin mahara da Jami`an Tsaro tun a shekata ta 2020.

A ranar 29 ga watan Yunin shekara ta 2022, jami’an tsaron Najeriya sun kashe mutane da dama a Ogbaru. Kashe-kashen ya haifar da wani gangami a shafukan sada zumunta mai taken #OgbaruMassacre da aka ɗauki kwanaki ana yi.

Jami’an tsaron Najeriya sun musanta cewa suna da hannu a wani kisan kiyashi da aka yi a yankin, inda suka bayyana cewar mutanen da aka kashe yan bindiga ne da suka yi sansani a cikin babban dajin da ya tashi daga Ogbaru zuwa Ihiala.

A ranar 25 ga watan Mayun shekara ta 2021, Sojojin Ruwan Najeriya sun yi musayar wuta da ƴan bindiga a ƙaramar hukumar Ochuche kodayake ba wanda ya rasa ransa.

Haka ma a ranar 16 ga watan Fabrairun 2022 , sojojin ruwan Najeriya sun kashe wani mutum tare da kama wasu huɗu waɗanda aka zarga da yaɗa manufofin ƴan aware a tashar Uga cikin ƙaramar hukumar Ogbaru, sojojin sun samu bindigogi da wukake a hannun mutanen.

Ranar 31 ga watan Disamban 2021, Jami`an Kar-ta-Kwana na Rundunar Sojojin Ruwan Najeriya suka kai samame wani sansani a dajin Ochan inda suka kashe mutane 10 da ake zargi da kama mutum biyar, dajin na Ochan yana kan iyakar Ogbaru da Ihiala.

Ranar 15 ga watan Nuwamban 2021, ƴan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Ogwaniocha a ƙaramar hukumar Ogbaru bayan sun ƙone gidansa.

Za a hukunta waɗanda suka aikata laifin - Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana takaici game da harin na Ogbaru, inda ya ce gwamnati ta ɗauki alwashin zaƙulo waɗanda suka aikata laifin domin su fuskanci hukunci.

Ministan Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken ya ce ba su san dalilin wannan hari ba. Ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da aka raba wa kafafen yaɗa labarai a ranar 18 ga watan Mayun bana.

''Ba mu da wata alama a halin yanzu da ke nuni da cewar an shirya harin ne domin aikinmu''

Wata sanarwa da Sakataren Yada Labaran Gwamnatin Anambra Christian Aburimeya ya fitar ta bayyana cewar akwai yiwuwar ganin ƴan sanda a ayarin, shi ne ya haifar da harin don haka akwai buƙatar aiki tare don magance faruwar irin haka a gaba.

Ƙaramar Hukumar Ogbaru ɗaya ce daga cikin ƙananan hukumomi takwas a jihar Anambra. Gwamnati ta sanya dokar hana fita a ranar 25 ga watan Mayu.

Sauran ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Aguata da Ihiala da Ekwusigo da Nnewi ta Arewa da Nnewi ta Kudu da Orumba ta Arewa da kuma Orumba ta Kudu.

Gwamnati ta ƙara da cewa yawaitar hare-hare a ƙananan hukumomin shi ne ya sa aka sanya dokar hana fitar, kuma har yanzu tana aiki.

Source: BBC