Menu

Yadda aka kitsa yunƙurin kashe Sarauniya Elizabeth II a Amurka

Sarauniya Elizabeth II ta Birtaniya

Wed, 31 May 2023 Source: BBC

Wasu takardu da hukumar bincike ta FBI a Amurka ta fitar sun ce Sarauniya Elizabeth II ta Birtaniya ta fuskanci barazanar kashe ta sa’ilin ziyarar da ta kai ƙasar Amurka a shekarar 1983.

A bara, bayan rasuwarta ne hukumar ta FBI ta fitar da wasu jerin takardu masu ƙunshe da bayanan tafiye-tafiyen sarauniyar zuwa Amurka.

Takardun sun nuna yadda FBI ta damu matuƙa game da kare lafiyar Sarauniyar saboda barazanar hari daga ƙungiyar ƴan tawayen yankin Northern Ireland, wato IRA.

An bayyana barazanar kai wa Sarauniyar hari ne ga wani jami’in ɗan sanda a birnin San Francisco.

Takardun sun ce wani jami’in ɗan sanda da ke yawan zuwa wani wurin hutawa na mutanen Ireland a garin na San Francisco ya shaida wa jami’in hukumar tsaron ta FBI game da wata tattaunawa da ya yi da wani mutum da ya haɗu da shi a wurin.

Ɗan sandan ya ce mutumin ya faɗa masa cewa yana son ya ɗauki fansa a kan abin da ya faru kan ƴarsa “wadda aka kashe a Arewacin Ireland lokacin da aka harbe ta da harsashin roba.”

Barazanar ta faru ne a ranar 4 ga watan Fabarairun 1983 – kimanin wata guda gabanin ziyarar Sarauniya Elizabeth II da mijinta Yarima Philip zuwa jihar California.

Bayanin takardun ya nuna cewa “Zai yi ƙoƙarin cutar da Sarauniyar ne ko dai ta hanyar jefa wani abu kan Jirgin ruwan shaƙatawa na masarauta daga kan gadar ‘Golden Gate Bridge’ a lokacin da jirgin ke wucewa ta ƙarƙashin gadar, ko kuma ya yi ƙoƙarin kashe ta a lokacin ziyarar da za ta kai gandun daji na ‘Yosemite National Park.’

A ƙoƙarin kare yiwuwar hakan jami’an hukumar tsaron sirri sun shirya rufe hanyar tafiya da ƙafa a kan gadar a lokacin da jirgin ruwan Sarauniyar ya kusa kai wa gadar.

Sai dai babu cikakken bayani kan matakin da aka ɗauka a gandun dajin Yosemite National Park.

Source: BBC