Masana tattalin aziki a Najeriya sun fara tsokaci kan yadda farashin kayayyakin amfanin yau da kullum za su tashi, idan har aka cire tallafin man fetur da gwamnatin kasar ta sanar za ta yi.
A baya dai gwamnatin ta ce ba ta da niyyar cire tallafin man, amma daga bisani ta ce dole ta dauki matakin saboda fatan da ake da shi na kwalliya za ta biya kudin sabulu ya gagara samuwa.
Shugaban kamfanin mai na ƙasa, NNPC, Mele Kyari ya ce gwamnatin na biyan naira biliyan 120 a kowanne wata a matsayin tallafin man fetur.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Kyari ya ce, a maimakon ƴan ƙasar su dinga sayen mai kan yadda farashin kuɗaɗen shigo da adana shi suke na naira 234 kan kowace lita guda, gwamnati na sayar da man a kan naira 162, don haka ita ke ɗaukar nauyin cikon kuɗin.
Sai dai ya ƙara da cewa, NNPC ba zai iya ci gaba da asarar waɗannan kuɗaɗe ba, don hakan ƴan Najeriya nan ba da jimawa ba za su koma sayen man a kan yadda aka samo shi.
Ya kuma shaida cewa dole ne a bar kasuwa ta ƙayyade yadda farashin mai zai kasance a ƙasar.
Shin mene ne ma tallafin mai?
Kamar yadda Dakta Muhammad Daneji, mai sharhi kan sha'anin tattalin arziki, kuma babban malami a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria ya shaida wa BBC, tallafin mai shi ne wani kaso da gwamnati take biyawa 'yan kasa, a duk lokacin suka je sayan man fetur da suke amfani da shi a motoci ko amfanin yau da kullum.
"Kasashen da suke da man fetur ne suke biya wa 'yan kasar tasu, amma a halin yanzu wasu kasashe da dama sun cire tallafin man fetur saboda dalilai na tattalin arziki da faduwar farashin man.
"Sai dai kasashen da suka cire tallafin mai musamman na Turai su na biya wa 'yan kasashensu manyan buƙatu yau da kullum, misali inganta fannin lafiya, da tsaro da ilimi, da ayyukan ababen more rayuwa da sauransu."
Ta yaya cire tallafin mai zai shafi 'yan Najeriya?
Dakta Daneji ya kara da cewa: "Cire tallafin mai zai shafi duk wani dan Najeriya da wanda yake amfani da mai, ko dai a abin hawa, ko injin janareto na gida, ko masu amfani da shi a wuraren sana'a, da ma wanda baya amfani da dukkan abubwuan da na zayyana.
"Saboda a duk lokacin da wani aiki da kake so a yi maka ya taso, da ake bukatar amfani da abubuwan da su ma suke bukatar man fetur kudin aikin zai karu.
Kasancewar ba mu da wadatacciyar wutar lantarki a Najeriya, a zamanin nan kuma kusan komai an dogara ne a kan hasken lantarkin nan, don haka komai da ake saya zai yi tsada, ciki har da abubuwan da ba ma a amfani da man fetur wajen samar da su.
"Misali dauko amfanin gona, za a yi amfani da motar da aka zuba wa man fetur don haka farashin kudin dakon kaya zai sauya kenan," in ji shi.
Wane alfanu cire tallafin mai zai yi wa gwamnati?
Dakta Daneji ya ce gwamnati za ta samu karin kudaden shiga, tun da dama kaso mai tsoka na kudaden shigar gwamnatin Najeriya sun dogara ne ga abin da take samu daga man fetur.
Saboda haka a duk lokacin da gwamnati ba ta biya tallafin mai ga 'yan Najeriya ba za ta samu kudade.
A takaice matukar an yi amfani da kudin yadda ya dace, gwamnati za ta samu kudaden gudanar da ayyukan more rayuwa da ci gaban al'umma.