Menu

Yadda lamarin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a jihar Zamfara

63886219 Hoton alama

Tue, 2 Jan 2024 Source: BBC

Kimanin al'ummomin garuruwa goma ne da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, suke gudun hijira zuwa wasu wurare sakamakon kwazzabar da 'yan bindiga da ke yi masu ta hanyar hare-hare, da aikata kisan gilla, da kuma sace mutane don neman kudin fansa da sauran miyagun laifuka.

Jama'ar da matsalar ta addaba a yankin yammcin yankin tsafe sun shiga tsaka mai-wuya inda lamarin yake ta ƙara tsananta.

Wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya yi wa BBC bayanin cewa lamarin ya shafi kusan garuruwa goma a yankin inda ya ce a baya bayan nan 'yan bindiga sun kai hari a ƙauyen Rakyabu a yankin inda suka fatattaki al'ummar ƙauyen baki ɗaya wanda haka ya yi sanadiyyar mutuwar mutane biyu.

'A yanzu haka babu ko kaza a garin, kowa ya gudun sun dawo cikin garin Tsafe suna kwana cikin tasha da bakin titi. Duk sun zama 'yan gudun hijira'. in ji shi

Ya ƙara da cewa aksarin garuruwan da ke yankin sun shiga irin wannan halin inda mafi yawan mutanen yankin suka yi gudun hijira zuwa cikin garin tsafe.

Ya ce 'An shekara guda ana yi mana wannan abin amma yanzu lamarin ya ƙara tsananta. Mun kai kukar mu ga gwamnati amma har yanzu babu wani mataki da aka ɗauka, kuma mu yanzu ba mu ma san makomarmu ba'.

Amma ita gwamnatin Jihar ta Zamfara ta yi ikirarin cewa matsalar rashin tsaro ta yi sauki kan yadda ta kasance a shekarun baya.

Mai magana da yawun gwamnatin jihar Zamfara, Suleiman Bala Idris ya ce gwamnati mai ci a yanzu ta ɗauki ƙwararan matakai domin shawo kan matsalar, tare da duba halin da 'yan gudun hijiran ke ciki.

A cewarsa 'Gwamnati za ta duba ta ga irin agjin gaggawan da za ta kai wa wadanda suka yi gudun hijira a yankin, kafin lokacin da za a fi ƙarfin matsalar har su sami komawa ƙauyukansu'.

Bayanen da aka samu sun ce wanna yankin na yammacin Tsafe ya na kusa da dajin 'mun haye' wanda ya zama mafaka ga 'yan bindigan da kan fito daga yankiunan Birnin Gwari da Faskari da Sabuwa da sauran garuruwan da ke makwabtaka da yankin.

Source: BBC