BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yadda ‘yan siyasa ke biyan maƙudan daloli don yaɗa labaran karya

15450091 Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar plus Peter Obi (middle)

Fri, 20 Jan 2023 Source: BBC

Wani binciken BBC ya gano cewa jam'iyyun siyasa a Najeriya na ba wa masu fada a ji a shafukan sada zumunta kudi a boye domin su yada bayanan karya a kan abokan takararsu gabanin zabukan da ke tafe.

Tawagar sashen yada bayanan karya na BBC ta tattauna da masu kwarmata bayanai da ke yi wa wasu jam'iyyun siyasa biyu aiki da kuma masu fada a ji a kafafen sada zumunta.

Masu kwarmata bayanan sun ce jam'iyyun siyasar na ba su kudi da kyautuka da kwangilolin da kuma wani lokaci mukamin siyasa don su yi musu aiki.BBC ta sakaya sunan wadannan mutane saboda dalilai na tsaro.



Source: BBC