Menu

Yadda mata masu juna biyu daga Rasha ke zuwa Argentina domin 'ya'yansu su samu takardun zama 'yan kasar

Hoton alama

Mon, 13 Feb 2023 Source: BBC

Fiye da mata 5,000 'yan kasar Rasha sun shiga kasar Argentina cikin 'yan watannin da suka gabata, cikinsu har da wasu mata masu juna biyu 33 da suka isa can ranar Alhamis a jirgin sama daya, kamar yadda jami'ai suka sanar.

Wadannan matan duka sun kusa haihuwa, inji hukumar da ke kula da batutuwan zama dan kasa ta Argentina.

Ana hasashen matan na son su haifi 'ya'yan nasu a Argentina ne saboda su sami takardun zaman 'yan kasar.

An sami karuwar masu zuwa Argentinar daga Rasha, abin da yasa wasu ke alakanta batun da yakin Ukraine.

Sai dai cikin mata 33 da suka sauka a babban birnin kasar a ranar Alhamis, an tsare uku saboda "matsalolin da aka gano a takardunsu na shiga kasar", kuma an hada su da wasu matan guda uku da suka isa kasar kwana daya kafin isar wadannan, inji Florencia Carignano, shugabar hukumar shige da fice ta kasar yayin wata hira da jaridar La Nacion.

Ta ce "Mun gano cewa wasu matan na zuwa ne da wani dalilin na daban a maimakon na yawon bude idanu. Su da kansu sun amince da dalilin zuwansu nan."

Ta kuma ce matan 'yan kasar Rasha na son 'ya'yan da suka haifa su sami takardun zama 'yan Argentina, saboda fasfon Argentina yafi na Rasha daraja.

"Matsalar da suke fuskanta shi ne sun zo Argentina, sun yi wa 'ya'yansu rajista a matsayin 'yan wannan kasar, sai su yi tafiyarsu kawai. Fasfunanmu na da karfi sosai a duniya, domin su kan ba 'yan kasarmu damar ziyartar kasashe fie da 171 ba tare da biza ba.

Wasu kasashen tarayyar Turai sun daina ba 'yan asalin kasar Rasha bizar ziyartar kasashensu, ciki har da mambobin kungiyar tarayyar Turai da ke da iyaka da Rashar.

An dai saki wadancan matan guda shida bayan da lauyansu ya koka cewa ana tsare da su "ba tare da sun aikata wani laifi ba".

'Babu ingantaccen tsarin kiwon lafiya a Rasha'

Jaridar La Nacion ta bayyana dalilin da yasa ake samun karuwar shiga Argentina da mata masu ciki daga Rasha ke yi.

Ta ce, "Baya ga yakin Ukraine da ya sa suna tserewa da rashin ingantaccen kiwon lafiya a kasarsu, matan na son yadda za su iya shiga Argentina ba tare da takardun izini ba, da kuma asibitoci masu nagarta a fadin kasar."

Wannan halayyar ta haihuwar yara a Argentina da mata daga Rasha ke yi ba sabon abu ne ba.

Wasu shafin intanet da BBC ta gani yana tallata wa mata masu juja biyu da ke sha'awa tikitin zuwa Argentina domin su haihu a can.

Akwai tikiti maii rangwame da ake sayar da shi kan dalar Amurka 5,000, akwai kuma na masu hannu da shuni da ya fara daga dalar Amurka 15,000 zuwa sama.

Ranar Asabar da ta gabata, jaridar La Nacion ta wallafa wan rahoto da ke cewa 'yan sanda a Argentina na gudanar da wani bincike kan yadda ake badakkalar ba mata masu juna biyu 'yan kasar Rasha tare da mazajensu takardun zama 'yan kasa na bogi cikin hanzari domin su sami damar zama a kasar ta Argentina.

'Yan sanda sun ce wata kungiyar masu aikata laifuka kan caje su kusan dalar Amurka 35,000 domin su sami komawa Argentina da zama.

Kawo yanzu babu wanda aka kama, sai dai 'yan sandan sun kwace wasu komfutoci da na'urori masu kwakwalwa, da takardun shige da fice, har ma da tarin kudaden kasar waje.

Source: BBC