Menu

Yadda matasan Najeriya ke nuna wa ƴan takarar shugaban ƙasa goyon baya

32316072 Some of di major presidential aspirants

Thu, 20 Oct 2022 Source: BBC

A ranar 25 ga watan Fabrairun 2023 ne za a zaɓi sabon shugaban Najeriya, kuma matasan ƙasar sun dage wajen yi wa ƴan takarar da suke goyon baya kamfe a fili da kuma ta shafukan intanet. Ba a taɓa ganin matasan ƙasar sun shiga ana damawa da su a harkar yaƙin neman zaɓen ba kamar wannan karo. Kuma hakan na nuna cewar suna da shauƙin taka muhimmiyar rawa wajen zaɓen wanda zai gaji Shugaba Muhammadu Buhari. Babu yadda za a yi ƴan siyasa su ci nasara a zaɓe matuƙar ba su samu haɗin kan mata da matasa ba a ƙasar, kasancewar su ne suka fi yawa a masu kaɗa ƙuri’a, kamar yadda alƙaluman hukumar zaɓen ƙasar mai zaman kanta suka bayyana. Da alama matasan sun gane irin tasirin da suke da shi a batun zaɓe na ƙasar, kuma suna son amfani da wannan damar wajen nemar wa ƴan takarar da suke so goyon baya. Matasan na nuna goyon bayan nasu ne ta hanyar shirya gangami, ko bi gida-gida domin tattaunawa da mutane, ko kuma tattaunawa ta shafukan sada zumunta. Ƴan takara 18 ne ke neman kujerar shugaban ƙasa a Najeriya a zaɓen na shekara ta 2023, BBC ta duba yadda magoya bayan ƴan takarar ke nuna goyon baya ga ƴan takaran nasu. Gangamin mutum miliyan ɗaya domin Peter Obi Magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) Peter Obi, sun gudanar da gangamin mutum miliyan ɗaya domin nuna goyon bayansu gare shi da mataimakinsa Datti Baba Ahmed. Magoya bayan, waɗanda ke yi wa kansu laƙabi da ‘Obidients’, sun gudanar da gangamin ne a garin Lafia na Jihar Nasarawa a cikin watan Agusta. Bayan haka, sun gudanar da wani gangamin a garin Yenagoa na Jihar Bayelsa a cikin watan Satumba. Haka nan, sun gudanar da wani gangamin a ranar ɗaya ga watan Oktoba a Legas, yayin da ake murnar zagayowar ranar da Najeriya ta samu ƴancin-kai. Gangamin mutum miliyan biyar domin Bola Ahmed Tinubu Magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar All Progressive Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, sun yi gangami a cikin watan Oktoba, wanda suka yi wa laƙabi da gangamin mutum miliyan biyar. Magoya bayan waɗanda kan yi wa kan su laƙabi da ‘Batist’ sun yi amfani da gangamin wajen nuna goyon bayansu ga gwamnan Jihar Legas Babjide Sanwo-Olu da mataimakinsa Femi Hamzat, waɗanda ke neman a sake zaɓen su a shekara mai zuwa. Shugaban kwamitin kula da tashoshin mota na jihar Legas, Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo ne ya jagoranci gangamin na goyon bayan Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima. Gangamin mutum miliyan ɗaya domin Atiku Abubakar

The energy is electrifying! -AA #AtikuInBauchi pic.twitter.com/g4pVtcEWDT — Atiku Abubakar (@atiku) October 5, 2022 Mata da maza magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Niger sun fita kan tituna domin nuna goyon bayansu ga ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da mataimakinsa Ifeanyi Okowa. Gangamin na mutum miliyan ɗaya ya fara ne daga ƙofar shiga birnin Minna, zuwa shataletalen Bahago. Mutanen, waɗanda suka yi wa kansu laƙabi da ‘Atikulaes’ sun kuma yi amfani da damar wajen yi wa ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, Liman Kantigi da mataimakinsa Samuel Gwomna, kamfe. Masu goyon bayan Rabi’u Musa Kwankwaso Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabiu Musa Kwankwaso, ya ga yadda magoya bayansa suka nuna masa ƙauna, lokacin da ya je garin Maiduguri na Jihar Borno domin buɗe ofishin jam’iyyar a cikin watan Agusta. Dubun-dubatar mutane ne suka fito domin nuna masa goyon baya a garin na Maiduguri, inda ya ce matuƙar dukkanin mutanen da suka fito a wannan ranar suka goya masa baya, suka fito a ranar kaɗa ƙuri’a suka zaɓe shi, to kuwa babu shakka shi ne zai lashe zaɓen shugaban ƙasa. Masu goyon bayan Omoyele Sowore

#SoworeLiveInLagos Returned to Lagos after 3 years of city arrest, detention, torture false trial, attempted assassinations by the @mbuhari regime #WeCantContinueLike pic.twitter.com/sdFkvnKzwy — Omoyele Sowore (@YeleSowore) September 5, 2022 Magoya bayan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Africa Action Congress (AAC) sun yi gangami domin nuna masa goyon baya, tare da mataimakinsa Magashi Garba, a zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa. Haka nan magoya bayan ɗan takaran na ci gaba da nuna masa goyon baya a shafukan sada zumunta.

Sowore is the most relevant 2023 Presidential Candidate and the old System are scared knowing he's going to win as the President of Nigeria by 2023. So they exclude him in debates and other things and counts him out as a top running contestant. The fear of Sowore

Source: BBC