Menu

Yadda ragunan Sallah ke tsada a Najeriya

Hoton alama

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Yayin da ƙasa da mako guda ya rage a gudanar da bikin Babbar Sallah a faɗin duniya, a Najeriya al'ummar Musulmin ƙasar sun fara kokawa kan tashin farashin ragunan layya.

Yayin wata ziyara da BBC ta kai wata kasuwar dabbobi da ke Kubwa a Abuja, mun tarar matsakaicin rago na kaiwa Naira dubu dari uku zuwa dubu dari hudu.

Wasu masu saya da suka je kasuwar don sayan ragunan sun bayyana cewa a yanzu, tashin farashin ya sa suna tunanin anya ma kuwa za su yi layyar.

''Gaskiya sun yi tsada sosai idan aka kwatanta da bara, na dauka ba zai wuce dubu dari da hamsin ba haka babba, amma yanzu su suna maganar cewa dubu dari uku, gaskiya bana jin zan yi layyar nan bana'' inji wani Kwastoma.

Sai dai a nasu bangaren masu sayar da ragunan na cewa laifin ba daga wajensu yake ba, domin shi kansa abincin ragon ya yi tsada, kana farashin jigilar ragunan daga inda suke sayowa ma ya tashi, duba da karin man fetur.

A cewar wani mai sayar da raguna a kasuwar Malam Lamin Kano, ya ce ''Yanzu duk rago daya daga Kano zuwa Abuja a kan Naira dubu goma aka kawo mana su, haka kuma ko a can kauyen inda muke sayo su sun tashi, wanda muke saya Naira dubu dari biyu yanzu sai dai dari biyu da hamsin''.

Muhimmancin yin layya ga Musulmai

Layya, sunna ce mai karfi a wurin mafi yawancin malamai na Musulunci. Sunnah ce ta Annabi Muhammad, kuma tana da asali tun daga Annabi Ibrahim Alaihi salam.

Annabi ya kwadaitar da a yi ta, shi kansa ya yi, ya kuma yi kira ga al’umma su yi.

Ana yin layya da dabbobi nau’in Rakumi da nau’in shanu da nau’in Awaki, wato Tunkiya da Akuya da Rago.

Sai dai duk da muhimmancin layya a addinin Musulunci, a kowacce shekara a kan samu tashin farashin dabbobin da ake yin ta da su

Source: BBC