Gudun hijira domin tsira da rayukansu daga mayaka ba sabon abu ba ne ga ƴan kasar Sudan waɗanda ke ƙetarawa zuwa kasar Chadi- gajiyan da ke fuskokinsu na nuni da irin mawuyacin halin da suka kwashe shekaru da dama a ciki.
Mahmud Adam Hamad ya shaida wa BBC cewa ba su daɗe da dawowa gida ba domin fara rayuwasu kafin wannan sabon rikicin ya sa su ka sake yin hijira.
Rikicin da ya ɓarke a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin manyan hafsoshin soji na Sudan guda biyu, ya sake haddasa bullowar wani rikicin ƙabilanci a yammacin yankin Darfur.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙiyasta cewa fiye da mutum 100,000 ne suka yi gudun hijira sakamakon rikicin, inda mafi yawan su ke ƙetarawa zuwa ƙasar Chadi da ke da iyaka da Darfur.
Dama an kwashe shekaru ana fuskantar tarzoma a yankin Darfur sakamakon rikici tsakanin wasu ƙabilu da ke yankin da Larabawa.
A lokacin da sauran ƙabilu suka yi wa gwamnati bore a shekarar 2003, sakamakon zargin da suka yi wa gwamnati na nuna musu wariya, gwamnatin ƙasar ta mayar da martani ta hanyar amfani da mayaƙan Larabawa da a ka fi sani da Janjaweed, wadanda ake zargi da aikata munanan ayyuka.
Da dama daga cikin mayaƙan na Janjaweed ne suka rikiɗa zuwa ƙungiyar ‘Rapid Support Forces’ wani rukunin jami’an tsaro da ke yaƙar gwamnati a halin yanzu.
Mutane kamar Mr Hamad da iyalansu, sun ƙare a sansanin ƴan gudun hijira na wucin-gadi da ke yankin Koufroune da ke kasar Chadi.
Akwai kimanin mutane 8,000 a sansanin, waɗanda suka samu tsira da ɗan abubuwan da suka mallaka da kuma dabbobi, wanda za su iya amfani da su wurin neman sauƙin mawuyacin halin da suke ciki.
Mr Hamad ya yi tafiye-tafiye masu haɗari guda biyu, ya ƙetara iyaka domin ya samu ceto tare da matansa biyu da ƴaƴa takwas daga Darfur.
‘Mafi yawanci da daddare nake tafiya. Na samu ƙetarowa da su, ina tafiya daga wuri zuwa wuri tare da iyalina har sai da muka iso.’
"An kusa a yi min fashi a tafiyata ta biyu” yake bayani a yayin da yake tsaye a kusa da matsuguninsa da aka yi da itatuwa da ledoji.
An taɓa kai farmaki a ƙauyensu da ke Darfur a inda ya rasa gonarsa da dabbobi kuma waɗansu ‘yan uwansa suka rasa rayukansu.
“Sun yi mana duka da bulala. Mun roƙe su su sake mu”
Mr Hamad ya yi bayani kan yadda ya tsere daga ƙauye zuwa ƙauye har ya ƙetara zuwa ƙasar Chadi.
Daga baya ya koma Darfur tare da iyalinsa yana tunanin cewa komai ya lafa, amma yanzu ga shi ya sake dawowa.
Yanzu yana dakon kaya ne a sansanin domin ya samu kuɗin da zai iya sayen abinci.
Ibrahim Bashar Ebra, mai shekara 83 da matarsa, Maka Naseem Tabeer mai shekara 70 na zaune a inwar da aka yi da leda inda suke samun sauƙi daga zafin rana.
Suna kewaye da abubuwan da suka mallaka waɗanda suka rufe da barguna domin kare su daga ƙura.
Sun rasa abubuwan da suka mallaka a rikicin Darfur lokacin da aka kai farmaki a gonarsu, aka kwashe musu dabbobi.
A wani farmakin da aka sake kaiwa kuma aka sace musu ƴaƴansu uku waɗanda har yanzu ba su san inda suke ba.
"Na zame ba ni da wurin zama kuma na dogara kan waɗansu,” a cewar Mr Ebra.
Abin da ya tursasa shi yin gudun hijira makonni biyu da suka wuce shi ne wani farmaki da aka kai ƙauyensu inda aka kashe mutane da dama.
"An ƙona ƙauyen baki ɗaya . A amalanke aka ɗauko ni zuwa nan,” yake bayani a yayin da yake nuni da cewa ciwon ƙafa ba zai bar shi ya yi tafiya da kansa ba.
Matarsa ta yi masa tambaya "Ya kake ganin rayuwarmu za ta kasance nan gaba?”
"Babu gwamnati a Darfur, sai dai mayaƙan ƴan sa-kai, wanda babu abin da suke yi sai kisa, da fyade, da kuma sace mutane. Allah kaɗai ya san abin da za mu fuskanta” in ji Mr Ebra.
Ya ce ba zai taɓa komawa ba.
"Ina zaune lafiya a nan, ba ni da matsala da samun ruwan sha daga wannan kwarin. Meye zan samu idan na koma? Shekara na 83, ba ni da ƙarfin jiki amma ina da taurin zuciya.”
A halin yanzu hukumonin Majalisar Ɗinkin Duniya ke kula da su, wanda suka haɗa da shirin samar da abinci na duniya (WFP).
Ana tsammanin dubban ƴan gudun hijira a sansanin, a inda ake tunanin rikicin na Darfur na iya ƙara taɓarɓarewa.
Akwai fiye da mutum miliyan ɗaya da ke gudun hijira a ƙasar Chadi kuma kusan 400,000 daga cikin su ƴan ƙasar Sudan ne daga Darfur.
A cewar shugaban Shirin Samar da Abinci na duniya na ƙasar, Pierre Honnorat, yanzu ana ƙoƙarin kai tallafi ne kafin damina ta faɗi.
"Ana matuƙar buƙatar haka domin cikin ƴan makonni kaɗan, za a samu damuwa wurin hanyar da za a bi domin kawo masu agaji. Babban matsalar ke nan, muna buƙatar abubuwan da za mu yi amfani da su domin mu taimaka musu.” Ya bayyana wa BBC.
Masu gudun hijira a Koufroune sun tsira yanzu, amma da su da sauran ƴan Sudan rayuwarsu na hannun hafsoshin soji guda biyu da ke rikici kan ƙasarsu.
Akwai matsin lamba daga ƙasashen duniya kan a kawo ƙarshen wannan rikicin, idan ba haka ba yana iya haddasa yaƙin basasa a Sudan da zai fi na Libiya da Syria muni.