BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yadda rikicin kabilanci ya tarwatsa dubban mutane a Indiya

Hoton alama

Mon, 8 May 2023 Source: BBC

Mutane da dama sun rasu, sanadin barkewar rikicin kabilanci a jihar Manipur da ke arewa maso gabashin Indiya.

Cincirindon mutane ne suka rika kai hare-hare a kan gidaje, da motoci da coci-coci da kuma sauran wuraren ibada, a cewar jami’ai.

Rikicin dai ya faro ne a makon jiya, bayan kabilu 'yan gargajiyar yankin sun yi zanga-zangar nuna adawa da bukatar babbar kabilar jihar da ke neman a ba ta matsayin kabila da ke fama da koma-baya.

Al'ummomin Meitei, wadanda ke da kashi 53% na yawan jama'ar jihar, sun shafe tsawon shekaru suna neman a shigar da su cikin jerin kabilu masu koma-bayan ci gaba a Manipur, abin da zai ba su damar samun filaye da tabbatar musu da wani kaso na ayyukan gwamnati da gurabe a manyan makarantu.

Al'ummomin da aka riga aka shigar jerin al'ummomi masu raunin ci gaba, kamar al’ummar Kuki da suke zaune a yankunan kan tsaunuka, sun damu game da yiwuwar rasa filayensu na gado da ke dokar dajin, idan al’ummar Meitei ta cimma burinta.

A ranar Litinin, ministan cikin gidan Indiya, Amit Shah ya bayyana wa wani gidan talbijin cewa, an shawo kan tarzomar da ta tashi a Manipur tare da yin kira ga mutane su rungumi zaman lafiya.

A cewarsa gwamnatin Manipur za ta tattauna da dukkan bangarori kafin ta yanke hukunci kan batun.

An aika dubban sojoji zuwa jihar domin tabbatar da zaman lafiya, an kuma kafa dokar hana fita a mafi yawan yankunan jihar tare da katse layukan internet.

A makon jiya gwamnan jihar ya bada dokar a harbe duk wanda aka gani yana neman tayar da tarzoma.

An ceto Sama da mutane 23,000 tare da kai su muhallai na wucin gadi, a cewar hukumomin soji ranar Lahadi.

Mutanen da rikici ya raba da gidajensu sun hadar mata da yara masu tarin yawa.

Mazauna yankin sun ce hankalinsu a tashe yake game da yanayin yadda rayuwarsu za ta kasance.

"Ba mu da kwanciyar hankali a yanzu” L Sanglun Simte wanda ke zama a garin Imphal, babban birnin jihar, ya fada wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP.

Dan shekara 29 daga al'ummar Kuki ya yi kwanaki yana kwana a kusa da filin jirgin sama na Imphal tare da mutanen gidansu 11.

A ranar Lahadi, sojoji sun yi bayanin cewa, rikicin ya dan lafa bayan sun yi aiki tukuru cikin sa’a 96, inda suka ceto mutanen da ke zaune a yankin tare da kwantar da tarzoma da kuma tabbatar da zaman lafiya.

Amma har yanzu ana zaman dar-dar a yankunan jihar da dama.

Dumbin al'ummar jihar 'yan gargajiya ne ke zaune a sansanonin ‘yan gudun hijira da sojoji suka kafa, wadansu jihohi sun aika da masu aikin ceto jama'arsu da rikicin ya ritsa da su a Manipur.

Jihohi kamar Maharashtra da Andhra Pradesh, sun nemi jirage na musamman domin kwashe mutanensu.

Rikici ya barke ne ranar Larabar da ta gabata. Inda aka lalata motoci, tare da kona gidaje da shaguna a garin Imphal, da sauran yankuna.

Hotuna sun nuna gidaje na ci da wuta, inda hayaki ya turnuke ko'ina.

Sojoji sun ce suna shawo kan lamarin.

A ranar Litinin, mutane sun fito sayen abinci da magunguna bayan an sassauta dokar hana fita ta tsawon ‘yan sa’o’i a yankunan da rikicin ya shafa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na PTI ya ruwaito.

Source: BBC