Menu

Yadda wani mutum ya caccaka wa yara wuƙa a Faransa

Ƴan sanda sun ƙoƙarin kama wanda ya kai harin, in ji Gérald Darmanin

Fri, 9 Jun 2023 Source: BBC

An caka wa wasu ƙananan yara huɗu wuƙa a wani wurin shaƙatawa da ke kusa da tafkin Annecy, a kudu maso gabashin Faransa, in ji ministan cikin gida.

Ƴan sanda sun ƙoƙarin kama wanda ya kai harin, in ji Gérald Darmanin.

Rahotanni sun bayyana cewa yaran ƙanana ne ƴan kimanin shekara uku da haihuwa kuma biyu daga cikinsu na cikin mawuyacin hali.

Mai kula da yankin Antoine Armand ya bayyana harin a matsayin mummnan abin kyama kuma firaministan Faransa Élisabeth Borne na kan hanyar zuwa wurin da harin ya afku.

Mr Armand ya ce, hukumomi na kan gudanar da bincike kuma abin da aka sani a halin yanzu ba shi da yawa, amma yana taya waɗanda abin ya shafa jimamin al'amarin.

Tun da farko, hukumomin yankin sun ce yara shida ne suka jikkata a harin, amma daga baya hukumomi sun tabbatar da cewa adadin mutane shida ne abin ya shafa ciki har da yara hudu.

Ana tunanin cewa wanda ake tuhumar ɗan gudun hijira ne daga Syria, a cewar rahotnni da aka samu daga kafofin labarai kamar su Le Parisien, BFM TV da AFP, wadanda suka samu rahotanni daga ƴan sanda.

Ya afka wa yaran ne yayin da suka ziyarci wurin shakatawan, kafin ya tsere ya kuma caka ma wani dattijo wuƙar a kusa da wurin.

'Yan sanda sun shigo cikin lamarin inda aka harbi wanda ya aikata laifin a kafa.

Majalisar dokokin Faransa ta yi shiru na minti daya, sannan kuma an rufe hanyoyi da ke kusa da inda aka kai harin.

Shugaba Emmanuel Macron ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa ɗaukacin ƙasar na cikin jimamin faruwar wannan mummunar lamari.

Tsohon ɗan wasan ƙwallon kafar ƙungiyar Liverpool Anthony le Tallec na gudu a cikin garin a lokacin da abin ya faru.

Ya ce ya ji mutane ne ihun 'A gudu! A gudu'! ya kuma ga yadda 'yan sanda suka bi wanda ake tuhumar bayan ya daɗa wa wani dattijo wuƙa. Ya ce ya ci gaba da gudunsa a kusa da tafkin, inda ya ga yaran da aka ji wa ciwo suna kwance a ƙasa.

"Abin mamaki ne wannan abin ya faru a Annecy" in ji shi.

Ya ƙara da cewa 'yan sanda sun ɗan yi jinkiri kafin su harbi mutumin da ke riƙe da wuƙa.

Wata mata mai suna Eleanor Vincent, ta shaida wa BBC cewa ta san cewa wani mummunan abu ya faru da take nufowa kusa da tafkin.

"Mutane na cikin gudanar da harkokinsu, suna shaƙatawa kamar yadda nake yi, ba ƙaramin abin tashin hankali ba ne. Ban san yadda zan bayyana lamarin ba."

Source: BBC