BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yadda za a gwangwanje makafi da sanduna zamani a Najeriya

 118105282 B2404aeb 0d8a 427f B23c 5c2ee6ed0df6 Taimakon zai je ga masu gani garara-garara da kuma marasa gani

Tue, 20 Apr 2021 Source: BBC

Wata ƙungiya da ke taimakawa nakasasu a Najeriya ta shaida aniyarta na raba sanduna jagora ga masu fama da larurar gani su 10,000 a wasu sassan ƙasar.

Ƙungiyar mai suna 'Disability Resource Foundation of Nigeria' ta ce za ta raba sandunan jagora ne ga masu gani garara-garara da kuma marasa gani.

A cewarta ta bijiro da wannan tsarin ne da nufin rage musu haɗuran da sukan fuskanta a yayin zirga-zirga da kuma sanya su zama masu dogaro da kansu.

Shugaban ƙungiyar Salisu Ibrahim ya shaida wa BBC cewa ɗaya daga cikin abin da ya ja hankalinsu wajen ƙaddamar da wannan shiri shi ne burinsu na tabbatar da cewa kowanne mai larura ido ya kasance yana da ƴanci fita ba tare da fargaba ba.

Hikimar raba sandunan

Ya ce, wasu za suyi mamakin hikimar raba sandunan, sai dai yawancin sandunan da ake amfani da su ba waɗanɗa suka kamata ba ne a yi amfani da su.

"Sannan basu da ƙwarewa ko fahimtar yada ake amfani da sandar kuma wanda za a raba musu yanzu na musamman ce da aka ƙirƙira domin ta taimakawa makafi ko waɗanɗa basa gani sosai wajen tafiya."

Salisu Ibrahim yana mai cewa, kafin a fitar da wannan shirin sai da suka yi bincike tare da gano manyan matsaloli kamar uku da masu larurar gani ke fama da shi.

"Na farko akasari ba sa iya amfani da sandunan zamani saboda tsadar su, sannan abu na biyu basu da ilimin sanin yadda ake sarafata ko amfani da sandar, na uku kuma shi ne jin kunyar amfani da sandar."

Wadanan dalilai ya sanya aka ƙirƙiro shirin wayar da kawuna ta hanyar haɗa-kai da hukumomin kula da hanyoyi da ƙungiyoyin direbobi da malaman makarantu da ke koyar da amfani da sanduna da daliban makarantu da iyaye, sannan aka tsara littafin koyar da amfani da sanduna, in ji Salisu.

A cewarsa, sandunan kala biyu ne akwai na rukunni wanɗanda ba sa gani baki ɗaya, akwai kuma na masu gani garara-garara.

Sannan ya ce ana iya naɗeta ko lanƙwasa sandar a jefa ta a cikin jaka ko aljihu duk lokacin da ba a bukatarta, sanduna ne na musamman da aka yi su domin daɗin tafiye-tafiye.

Yaushe za a soma rabon sanduna

Salisu ya ce sun soma rabon sanduna a makarantu makafi da makarantu da ke da makafi cikin ɗalibansu a Kaduna.

Amma dai nan da wata biyu za a ƙaddamar da gagrumin shirin raba sanduna a wasu jihohin Najeriya

Rukunin mutanen da za su ci gajiyar sanduna sun haɗa da wadanda basa gani da marasa hali da kuma malamai da ke koyar da amfani da sanduna kuma a kyauta za a raba musu.

Source: BBC