Ranar Lahadi Arsenal ta bar Ingila zuwa Amurka domin buga wasannin sada zumunta, a shirye-shiryen tunkarar kakar wasa 2023/24.
Tun kan Gunners ta ziyarci Amurka ta buga wasan sada zumunta biyu, domin gwada 'yan wasanta, wadda ta fafata da Watford da kuma FC Nurnberg.
Arsenal wadda ta yi ta biyu a gasar Premier League ta bara, za ta fara wasa a Amurka ranar 19 ga watan Yuli da fitattun 'yan wasan kwallon kafar gasar Amurka wato MLS All Stars.
Za a buga wasan a Audi Field da ke Washington, inda Wayne Rooney ne zai ja ragamar MLS All Stars.
Daga nan ne Arsenal za ta ziyarci New Jersey, domin fuskantar Manchester United a filin MetLife, inda za su kara ranar Asabar 22 ga watan Yuli.
Wasa na uku da Arsenal za ta yi shine da Barcelona a Los Angeles ranar 26 ga watan Yuli a filin wasa na kungiyar LA Rams.
'Yan kwallon da Arsenal ta je da su Amurka buga wasannin sada zumunta
1 Aaron Ramsdale
2 William Saliba
3 Kieran Tierney
4 Ben White
6 Gabriel Magalhaes
7 Bukayo Saka
8 Martin Odegaard
9 Gabriel Jesus
11 Gabriel Martinelli
12 Jurrien Timber
13 Alex Runarsson
14 Eddie Nketiah
15 Jakub Kiwior
16 Rob Holding
18 Takehiro Tomiyasu
19 Leandro Trossard
20 Jorginho
21 Fabio Vieira
25 Mohamed Elneny
26 Folarin Balogun
27 Marquinhos
29 Kai Havertz
31 Karl Hein
32 Auston Trusty
35 Oleksandr Zinchenko
41 Declan Rice
45 Amario Cozier-Duberry
Haka kuma Arsenal tana sa ran Emile Smith Rowe da Thomas Partey za su je Amurkan domin a buga wasannin.