BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

'Yan Barca da suka je Getafe buga La Liga ranar Lahadi

Yan wasan Barcelona a cikin murna

Mon, 17 Apr 2023 Source: BBC

Getafe za ta kara da Barcelona a wasan mako na 29 a gasar La Liga ranar Lahadi a filin wasa na Coliseum Alfonso Perez.

Barcelona ta ci Getafe 1-0 ranar 22 ga watan Janairu a wasan farko a kakar bana a La Liga, inda Pedri ya ci mata kwallon saura minti 10 su je hutun rabin lokaci.

Barcelona tana matakin farko da maki 72 a teburin babbar gasar tamaula ta Sifaniya, Real Madrid ce ta biyu mai maki 62.

Ranar Asabar Real Madrid ta je ta doke Cadiz 2-0 a wasan mako na 29 da suka kece raini a La Liga.

Wadanda suka ci wa Real kwallayen sun hada da Nacho Fernandez da kuma Marco Asensio.

Getafe mai maki 30 bayan wasa 28 tana ta 16 a kasan teburin La Liga na kakar nan.

'Yan wasan Barca sun hada da Ter Stegen, R. Araujo, Sergio, Lewandowski, Ansu Fati, Ferran, Iñaki Peña, Marcos A da kuma Jordi Alba

Sauran sun hada da Kessie, S. Roberto, Raphinha, Kounde, Eric, Balde, Gavi, Pablo Torre, Arnau Tenas, A. Alarcón da kuma Aleix Garrido

Source: BBC