BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

'Yan Real da suka je Valencia buga La Liga ranar Lahadi

Yan wasan Real Madrid

Sun, 21 May 2023 Source: BBC

Valencia za ta karbi bakuncin Real Madrid a wasan mako na 35 a La Liga ranar Lahadi a Mestalla.

Kungiyar da Carlo Ancelotti ke jan ragama na fatan cin wasa na 23 a kakar bana, wadda tuni Barcelona ta lashe La Liga na kakar nan.

Wasa biyu suka fuskanci juna a kakar 2022/23.

Sifanish La Liga Alhamis 2 ga watan Fabrairun 2023

  • Real Madrid 2 - 0 Valencia


  • Sifanish Super Cup Laraba 11 ga watan Janairun 2023

  • Real Madrid 1 - 1 Valencia


  • Real wadda saura wasa hudu suka rage mata tana ta biyu a teburin La Liga da maki 71, Valencia mai maki 37 tana ta 16 a kasan teburin kakar bana.

    Wannan shine wasa na shida da Real za ta fafata a watan Mayu daga takwas da za ta yi, daga shi za ta fuskanci Rayo ranar Laraba da ziyartar Sevilla ranar Asabar.

    Real din za ta buga wasan karshe a La Liga ta bana da Athletic Club a makon farko da za a shiga watan Yuni.

    Valencia za ta yi karawar da tazarar maki uku tsakaninta da 'yan ukun karshen teburin La Liga.

    Sai dai kungiyar ba a doke ta ba wasa biyu bayan nan, wadda ta ci daya da canjaras daya, kuma guda daya ta rasa daga shida da ta kara a gida a bayan nan.

    Cikin fafatawar shidan da ta yi a Mestalla ta yi nasara uku da canjaras biyu daga ciki.

    Tuni Ancelotti ya sanar da 'yan wasan da ya je Valencia da su, domin buga fafatawar.

    'Yan wasan Real Madrid:

    Masu tsaron raga: Courtois, Lunin da kuma Luis López.

    Masu tsaron baya: Carvajal, Militão, Alaba, Vallejo, Nacho, Odriozola, Lucas V., Rüdiger da kuma Mendy.

    Masu buga tsakiya: Kroos, Modrić, Camavinga, Valverde, Tchouameni da kuma D. Ceballos.

    Masu cin kwallaye: Benzema, Asensio, Vini Jr. da kuma Rodrygo.

    Source: BBC