BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yan gudun hijirar da suka ce tsintar bola ya fi musu bara a titi

Deiri Fayyad mai shekaru 26 ya ce zai iya ciyar da iyalinsa ne kawai ta hanyar tsintar bola

Wed, 29 Mar 2023 Source: BBC

Deiri Fayyad yana ta lalube cikin kwandunan shara a Beirut, babban birnin ƙasar Lebanon don samun robobi da abubuwan da aka zubar masu sauran amfani.

Aiki ne na ƙasƙanci, amma zaɓin da mahaifin 'ya'ya ukun yake da shi, ɗan kaɗan ne, matuƙar yana son ciyar da iyalinsa.

"Ina fara aiki ne da sassafe, misalin ƙarfe 8:30 kuma nakan yi aiki fiye da tsawon sa'a 12 a rana," ya faɗa, lokacin da ya ci gaba da dube-dubensa a cikin shara.

Yana amfani da hannuwansa ne, kuma ba tare da tufafin kariya ba, Deiri yakan zura jiki a cikin kwandon shara, ya buɗe ledoji don ganin abin da zai iya samu.

A rana, yana iya samun fam 250,000, kuɗin ƙasar Lebanon kimanin naira 1,500.

Mahaifin, ɗan shekara 26 daga Raqqa yana cikin 'yan Siriya kimanin miliyan ɗaya da suka samu mafaka a Lebanon mai maƙwabtaka, shekara 12 ke nan tun bayan fara mummunan yaƙin basasa a mahaifarsa.

A lokaci guda ita ma Lebanon ɗin tana durƙushewa sanadin matsalolin tattalin arziƙi da na shugabanci kusan tsawon shekara huɗu.

Dubban al'ummar Lebanon ne a yanzu ke rayuwa cikin fatara, inda da yawansu ke faɗi-tashin neman abinci da magani.

A 2019 ne gwamnatin Lebanon ta kasa biyan bashin ƙasashen waje da ake bin ta, kuma darajar kuɗin ƙasar ta karye.

A watan Maris ɗin bana, fam ɗin Lebanon ya yi faɗuwar da bai taɓa yin irinta ba, inda ake canzar fam 110,000 a kan dalar Amurka ɗaya - a iya cewa fam ɗin ya rasa kusan duk wata daraja da yake da ita.

Sai dai a lokacin da kusan kowa yake ɗanɗana kuɗa a Lebanon, 'yan Siriya da ke zaune a can ne suka fi fama da ƙasƙantacciyar rayuwar fatara.

'Yan gudun hijira da yawa - cikinsu har da ƙananan yara 'yan kimanin shekara 11- sun shiga harkar jari-bola a ƙoƙarinsu na ganin sun samu abin kaiwa baka.

Duk da yake, akwai ƙungiyoyin sa-kai da ke ƙarfafa gwiwar sake sarrafa shara a Beirut, amma ba harka ce da aka saba da ita ba, duk da haka an kafa cibiyoyin sarrafa shara don sake gyara robobin da za a iya sarrafa su zuwa wasu kayan amfanin gona da na kasuwanci.

Deiri yana cika ƙatuwar jakarsa da robobin ruwa. Yayin da na tsaya, ina kallo daga kusa, ɗoyin da ke tashi ya sa da wuya mutum ya iya numfashi ƙwaƙƙwara, don haka na cika da mamaki a kan yadda yake ci gaba da aikinsa - fuskarsa cike da fara'a.

Duk da aikin sa'o'i masu tsawo, Deiri yana kuma samun lokacin kula da wata mage, mai suna Amber, wadda yake ciyarwa da duk wani sauran abincin da ya samo a bola.

Deiri, da matarsa Yamama, da kuma 'ya'yansu suna rayuwa ne cikin wani ɗaki a wani gida da suke zaune tare da wasu iyalai guda biyu, babu nisa daga mashahuriyar unguwar bakin teku, inda yake zuwa tsintar robobi.

Mafi yawan abin da Deiri ke samu a wata, yana tafiya ne wajen biyan haya.

Ɗaki ne ɗan ƙarami, sai 'yar fitila ɗaya, da ledar tsakar ɗaki da wasu 'yan katifu da aka jefar a gefe.

Suna da galan-galan na ruwa da suke amfani da su don yin wanka da kuma wani ƙaramin murhun gas.

Da zarar ya koma gida, Deiri yakan rungume 'ya'yansa.

"Ba ni da halin tura 'ya'yana makaranta ko kuma na samar musu da rayuwa ingantacciya.

Da ƙyar da jiɓin goshi muke iya rayuwa, amma hakan ya fi na ƙasƙantar da kaina wajen yin bara a kan titi."

Da yawa cikin abokan aikin Deiri su ma sun zo ne daga Raqqa yankin da ke arewacin Siriya.

Sun kuɓuce wa yaƙi da kuma tanade-tanaden ƙungiyar masu iƙirarin jihadi ta IS, sai dai a Lebanon rayuwa tana da tsanani, kuma a nan, wannan ne kawai aikin da za su iya samu.

A 'yan shekarun nan, matsalolin kuɗi, sun sa 'yan Siriya sun maye guraben 'yan ƙasar Bangladesh, da ke zuwa aiki ana biyansu da dalolin Amurka, saboda su 'yan Siriya abin da ake biyansu bai taka kara ya karya ba, idan sun yi irin wannan aiki.

A wata bola da ake jibge shara, inda ake sake sarrafa robobi da sauran tarkace sannan a adana su kafin a sayar, da wahala a iya kwatanta irin warin da yake tashi - yana shaƙe maƙoshi kuma da wuya a iya kwatanta yadda ma'aikata ke fuskantar hakan a kullum ba tare da wani matakin kare lafiya a zahiri ba.

Wani gini da ke saman bolar a yanzu ya zama gida ga mutane da dama dukkansu 'yan Raqqa.

Suna tsoron yin magana da 'yan jarida, suna tsoron a yi hira da su. Sun ce suna tsoron a mayar da su gida Siriya.

Source: BBC