Menu

'Yan wasa 10 da hankali zai karkata kansu a AFCON

32320090 Hagu zuwa dama - Osimhen, Mane, Salah da Aboubakar

Fri, 12 Jan 2024 Source: BBC

Nan da sa'o'i kaɗan ne, nahiyar Afrika za ta ɗau harama ta ko'ina inda za a riƙa jin sowar magoya baya sakamakon Gasar cin Kofin nahiyar ta 2023, da za a fara karo na 34 a ƙasar Cote d'ivore.

Fitattun 'yan wasan nahiyar Afrika da suka yi fice a duniya za su baje-koli, daga ranar 13 ga watan Janairu zuwa 11 ga watan Fabrairu.

Shafin CAF na intanet ya zaɓo wasu 'yan wasa 10 da ake ganin hankali mai yiwuwa zai fi karkata kansu a gasar.

Sadio Mané (Senegal, 31)

Shi ne ɗan wasan da ya lashe kyautar gwarzon ɗan kwallon Afirka na 2022. Ɗan wasan na tawagar Teranga zai sake fitowa idon duniya a wannan gasar, wadda ƙasarsa za ta yi yunƙurin kare kambunta da zimmar komawa da shi gida.

Duk da yake, ya bar nahiyar Turai zuwa ƙasar Saudiyya da kwallo, Sadio Mane bai rasa ƙwarewarsa da zafin namansa ba ko kaɗan.

Shi ne hasken tawagar Senegal, kuma ba shi da burin da ya wuce lashe gasar karo na biyu a jere.

Vincent Aboubakar (Cameroon, 31)

A wasanni gasa mai yawa shi ne yake goya tawagar Indomitable Lions a kafaɗarsa.

Vincent Aboubakar shi ne kyaftin ɗin Kamaru kuma wanda ya fi ci musu kwallo a 'yan shekarun bayan nan.

Kwarin gwiwarsa da kyakkywan fatan da ya ke da shi da kuma kwarewarsa a jagoranci su ne za su kan Kamaru ga nasarar lashe gasar karo na shida a tarihi kamar yadda suke fata.

Sehrou Guirassy (Guinea, 27)

Dan wasan gaba da yake tashe a kakar bana ta Jamus.

Yana cin kwallaye kumaya bayar da kwallo da dama an ci a gasar Bundesliga.

Ko shakka babu rashinsa a wasannin da suka gabata ya janyo koma baya ga ƙasarsa Guinea

Sébastien Haller (Côte d'Ivoire, 30)

Karo na biyu kenan da zai buga gasar Afcon, ba shi da wani buri da ya wuce buga wannan gasa a gida gaban magoya bayan da suka karbe shi hannu biyu-biyu.

Sébastien Haller mai shekara 30 ya kai wata matuƙa da ake tsammanin zai nuna kansa a wannan gasa kamar yadda yake yi a nahiyar Turai.

Mohamed Amoura (Algeria, 23)

Yayin da manyan 'yan wasan suka mamaye tawagar Algeria irinsu Mahrez Feghouli Slimani da sauransu, sabbin matasa irinsu Mohamed Amoura za su so a gabatr da su a matsayin sabbin fuskar 2023. Kuma hankali zai koma kansu.

Dan wasan tsakiyan, ya nuna kansa a ƙungiyarsa ta Belgium na tsawon kusan shekaru biyu, kuma ya taimaka wa ƙasarsa wajen kai wa ga manyan gasanni

Victor Osimhen (Nigeria, 25)

Ba zai yiwu ba ka fitar da wannan jerin sunaye babu gwarzon nahiyar Afrika na 2023.

Victor Osimhen da ya zama gwarzo na bayan nan, ya sake samun ɗaukaka a wasannin kwallo a nahiyar.

Shi ne zai ja ragamar tawagar Najeriya, kuma hankali zai karkata kansa a Cote d'Ivoire.

Azzedine Ounahi (Morocco, 24)

Yana da kykkywan tasiri a tawagar Morocco ta 2022 da ta taka rawar gani a Kofin Duniya.

Azzedine Ounahi ya nuna kansa cewa zai iya ci gaba da taka rawa a ƙungiyar ta Atlas Lions.

Mohammed Kudus (Ghana, 23)

Daya daga cikin waɗanda suka dawo da West Ham cikin hayyacinsu a Premeir Ingila, Mohammed Kudus ya zama tauraro a daya daga cikin manyan Lig ɗin Turaita hanyar cin kwallo da kware da yake nunawa.

Ya kasance cikin mutum bakwai da suka karbi kyautuka a wannan kakar, ɗan wasan na Ghana mai shekara 23 zai zama ɗaya daga cikin 'yan manyan yan kwallo da za su taka rawa a tawagar Black Star a wannan gasar.

Mohamed Salah (Egypt, 31)

Kamar yadda ya yi a wasannin ƙarshe na Afcon shekara uku baya, Mohamed Salah zai zama ɗaya daga cikin mutanen da za su ja hankali a wannan gasar.

Dan wasan Liverpool kuma wanda ya kasance cikin manyan 'yan wasanta biyar da suka fi ci mata kwallo a tarihi, wanda yake yawancin kwallo a kowanne mako, Kuma shi ne kyaftin ɗin tawagar Masar.

Ƙarƙashin jagorancinsa, Masar ta rika samun damar samun zuwa manyan gasanni.

André Onana (Cameroon, 27)

Mai tsaron ragar Kamaru da yake jan ragamar jaridu a nahiyar Turai kusan ko wanne mako, saboda abin da yake ƙoƙari ko akasin haka a ƙungiyarsa ta Manchester United.

Sai dai ana fuskantar matsalar rashin fahimtar wadda za ta iya kai wa ga hana ɗan wasan buga gasar baki ɗaya.

Source: BBC