Menu

'Yan wasa hudu ne suka ci Real da Atletico a La Liga a bana

Ferran Torres

Tue, 25 Apr 2023 Source: BBC

Ranar Talata za a ci gaba da wasannin mako na 31 a gasar La Liga, inda za a fara da fatawa uku.

Za a buga wasa hudu ranar Laraba, sannan a kammala a karawa uku ranar Alhamis a babbar gasar tamaula ta Sifaniya.

Barcelona ta doke Atletico Madrid 1-0 a wasan mako na 30 ranar 23 ga watan Afirilu a Camp Nou.

Daf da hutu ne Ferran Torres ya ci wa Barcelona kwallon da ya ba ta damar hada maki ukun da take bukata.

Dan kwallon ya zama na biyu a Barcelona da ya ci Real da Atletico a La Liga a kakar tamaula, bayan Luis Enrique da ya yi wannan bajintar 2002/03.

A kakar nan ta 2022/23 'yan wasa hudu ne suka ci Real Madrid kwallo da kuma Atletico Madrid a gasar ta La Liga.

Torres ya nuna kansa ya shiga sahun manya a cin kwallaye, inda Xavi ke saka shi wasa tare da Raphinha da Robert Lowandowski a matakin masu cin kwallaye.

Sauran 'yan wasan da suka ci Real da Atletico a kakar nan sun hada da Gerard Moreno da Yéremi Pino daga Villarreal da dan wasan Mallorca Coto Muriqi.

Kawo yanzu saura fafatawa takwas a kammala gasar La Liga ta bana, watakila a kara samun wasu da za su ci Real da Atletico a kakar nan.

Barcelona ce ta daya a teburin La Liga da maki 76, sai Real Madrid ta biyu mai maki 65 da Atletico Madrid ta uku da tazarar maki biyar tsakaninta da kungiyar Santiago Bernabeu.

Wadanda ke karshen teburi kuwa a La Liga sun hada da Valencia mai mako 30 da Espanyol mai maki 28 da Elche ta karshe mai maki 13.

Jerin 'yan wasan da ke kan gaba a cin kwallaye:

  • Robert Lewandowski Barcelona 17


  • Karim Benzema Real Madrid 14


  • Enes Unal Getafe 13


  • Borja Iglesias Real Betis 12


  • Joselu Espanyol. 12
  • Iago Aspas Celta de Vigo 12


  • Vedat Muriqi Real Mallorca 12


  • Antoine Griezmann Atletico Madrid 11


  • Alexander Sorloth Real Sociedad 10


  • Alvaro Morata Atletico Madrid 10


  • Gabriel Veiga Celta de Vigo 9


  • Martin Braithwaite Espanyol 9


  • Vinicius Junior Real Madrid 9
  • Wasanin mako na 31 a La Liga:

    Ranar Talata 25 ga watan Afirilu

  • Cadiz da Osasuna


  • Girona da Real Madrid


  • Real Betis da Real Sociedad


  • Ranar Laraba 26 ga watan Afirilu

  • Atletico Madrid da Real Mallorca


  • Getafe da Almeria
  • Celta Vigo da Elche


  • Rayo Vallecano da Barcelona


  • Ranar Alhamis 27 ga watan Afirilu

  • Valencia da Real Valladolid


  • Villarreal da Espanyol


  • Athletic Bilbao da Sevilla


  • Source: BBC