'Yan wasan Afirka sun daɗe suna taka rawar gani a gasar Premier League ta ƙasar Ingila.
Daga cikin 'yan wasan Afirka da suka kafa tarihi a gasar akwai ɗan wasan gaba na Zimbabwe da Coventry City Peter Ndlovu, da Didier Drogba da Michael Essien da Riyad Mahrez da Mohamed Salah da kuma Yaya Toure.
A gasar kakar bana ta 2023/24 ma, kamar kullum akwai sabbin fuskokin fitattun 'yan wasan Afirka ta da za su haska a gasar.
Yayin da ake fara gasar ta bana BBC ta zaƙulo 'yan wasan Afirka shida da aka saya a bana domin buga gasar, da kuma irin rawar da za su taka a wannan kakar.
Andre Onana (Manchester United daga Kamaru)
Oluwashina Okeleji, masanin wasannin ƙwallon ƙafar Afirka ne, ya kuma shaida wa BBC cewa Onana ɗan wasa ne da ke da ƙwarewa, wanda ya faro tun daga makarantar horas da 'yan ƙwallo ta Barcelona, ya kuma taka leda a ƙasashen Netherlands da Italy kafin ya je United.
"Dan wasa ne zaƙa-ƙuri da ya samu nasarori masu yawan tun lokacin da ya koma Ajax a 2016, kuma na tabbata da wannan shauƙin zai je United'', in ji Okeleji.
Onana ya taka rawar gani a Kamaru, inda ya buga gasar kofin ƙasashen Afirka, inda ya taimaka wa ƙasarsa ta ƙare a mataki na uku bayan doke Burkina Faso a wasan neman matsayi na uku.
Ya kasance ɗan wasan Kmaru da ya fi taka rawar a gasar cin Kofin Duniya da aka buga a Qatar a 2022.
A watan Disamban 2022 ne Onana ya sanar da ajiye buga wa ƙasarsa wasa, to sai dai ya nuna alamun zai koma taka wa Indomitable Lions leda.
Nicolas Jackson (Chelsea daga Senegal)
Dan wasan mai shekara 22 - da ake yi wa laƙabi da 'Neymar ɗin Senegal' - ya burge mai horas da Chelsea, Mauricio Pochettino a wasannin share fage da suka buga.
To sai dai an shawarce shi da ƙara inganta wasanninsa domin samun damar sabawa da wasannin Ingila.
Jackson na cikin tawagar 'yan wasan Senegal da suka buga gasar Kofin Duniya ta 2022 da aka yi a Qatar, inda ya fara taka wa ƙasar wasa a wasan cikin rukuni na farko da ƙasar ta ƙara da Netherlands.
Ola Aina (Nottingham Forest daga Najeriya)
Benie Traore (Sheffield United daga Ivory Coast)
Wanda ya fi kowa zura ƙwallo a babbar gasar Sweden a kakar da ta wuce, Traore mai shekara 21 ya koma Sheffield United a watan Yuli.
"Dan wasa ne da ba ya wasa da damarsa musamman ta fuskar cin ƙwallaye'', in ji Okeleji.
"Abokan wasansa ba su ji daɗin barinsa babbar gasar Sweden ba, saboda yadda yake haskawa a ƙungiyarsa''.
Marvelous Nakamba (Luton Town daga Zimbabwe )
Wasannin da ya buga wa ƙasarsa: 23
Kwantiragi: Shekara uku
Dan wasan mai shekara 29, ba baƙon Premier ba ne, kasancewar ya taɓa buga wa Aston Villa wasanni 58, bayan komarwasa ƙungiyar a 2019 daga Club Brugge.
To sai dai raunin da ya ji a watan Disamban 2021, ya janyo masa koma-baya a harkar wasan.
Lamarin da ya ƙungiyar ta bayar da aronsa zuwa Luton a farkon shekarar 2023, inda ya samu damar komawa buga gasar Premier bayan taimaka wa Luton haurowa gasar.
Nakamba ya fara buga wa babbar tawagar Zimbabwe a shekarar 2015.
Issa Kabore (Luton Town daga Burkina Faso)
Wasannin da ya buga wa ƙasarsa: 29
Aro daga Manchester City
Kwatiragi: Shekara guda
Kabore mai shekara 22, na cike da zumuɗin buga gasar Premier a lokacin da ƙungiyar Manchester City ta ɗauke shi daga KV Machelen ta Belgium a 2020.
To sai dai burin ɗan wasan bai cika ba, sakamakon bayar da shi aro da City ta yi ga ƙungiyar ta Belgium.
Kabora ya kuma buga wasanni aro a ƙungiyoyin Troyes da Marseille na Faransa, kafin ya koma Luton a watan Yuli.
Dan wasan bayan ya fara taka wa ƙasarsa, Burkina Faso wasa a matakin matashi a shekarar 2019.
Ya kuma zama matashin ɗan wasan da ya fi nuna bajinta a gasar Kofin Afirka da aka buga a 2021, inda ya taimaka wa ƙasarsa kai wa matakin wasan dab da na ƙarshe.