BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yau Tinubu ke rantsar da sabbin ministocinsa

11283545 Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Mon, 21 Aug 2023 Source: BBC

Babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa ya fara ɗaukar harama domin rantsar da sabbin ministocin gwamnatin shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu.

A watan Afrilu ne shugaban na Najeriya ya miƙa wa Majalisar Dattijan ƙasar sunayen mutum 45 domin tantantancewa a matsayin minsitoci.

Bayan haka nan shugaban na Najeriya ya bayyana ma'aikatun da kowane minista zai riƙe gabanin ranar ta yau da ake rantsarwar.

Sai dai ko a ranar Lahadi, shugaban ya fitar da wasu sauye-sauyen da ya yi na ma'aikatu ga wasu sabbin ministocin.

Source: BBC