BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yau majalisar dattawan Najeriya za ta fara tantance ministoci

84959910 Majalisar dattawan Najeriya

Mon, 31 Jul 2023 Source: BBC

A ranar Litinin din nan ne ake sa ran majalisar dattawan Najeriya za ta fara zaman tantance mutane 28 da Shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya mika mata, domin amincewa ya nada su ministoci.

Haka kuma ana sa ran shugaban zai aika da wasu karin sunayen kasancewar, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya yi tanadi kowace jiha daga cikin 36 na kasar za ta samu akalla minista daya.

Daga sunayen da Shugaban kasar ya mika wasu jihohin suna da mutum biyu yayin da wasu ba su da ko daya.

Bisa al'ada dai majalisar kan amince da wasu mutanen salun alun, da gaisuwa kawai yayin da wasu kuma kan sha tambaya.

Sanata Mohammed Ali Ndume, babban mai tsawatarwa na majalisar dattawan ya shaida wa BBC Hausa cewa Majaisar za ta yi taza da tsifa don tabbatar da ta sauke nauyin da ke kanta yadda ya kamata.

Sai dai ya ce kamar yadda aka saba bisa al'ada, wannan karon ma ba za a bata lokaci wajen tantance duk wanda ya taba zama Sanata a cikin sunayen da aka aika musu ba, domin idan har ka taba zama Sanata, to kuwa ka cika duk wani sharadi na zama minista ma.

Ya ce kafin a kawo sunayen ma dama jami'an tsaro na gudanar da bincike a kansu, domin tabbatar da cewa babu wata matsala

Ya kara da cewa ''Ni a ganina, wannan ce za ta kasance tantancewa mafi sauki, domin shi ma shugaban kasa tsohon Sanata ne, wanda ya aiko mana sunayen tsohon kakakin Majalisar wakilai ne, dukkansu sun san me ya kamata, don haka babu wata matsala da za a samu''.

''Al'adar mu ce wannan, idan kai sanata ne a da, idan ka zo za mu gaisa ne kawai ka tafi, ban san wanene ya ce za a samu wani banbanci ba yanzu'' a cewarsa.

Ya ci gaba da cewa 'So so ne, amma ai son kai ya fi, yanzu a ce ko ni gobe idan na zo gaban 'yan uwana sanatoci su tantance ni a kan wani mukami su tozarta ni ?, ai hakan ba dai-dai bane'' inji shi.

Mutanen da za a tantance

Abubakar Momoh

Yusuf Maitama Tuggar

Ahmad Dangiwa

Hannatu Musawa

Uche Nnaji

Betta Edu

Dr. Diris Anite Uzoka

David Umahi

Ezenwo Nyesom Wike

Muhammed Badaru Abubakar

Nasir El Rufai

Ekerikpe Ekpo

Nkiru Onyejiocha

Olubunmi Ojo

Stella Okotete

Uju Kennedy Ohaneye

Bello Muhammad Goronyo

Dele Alake

Lateef Fagbemi

Mohammad Idris

Olawale Edun

Waheed Adebanwp

Iman Suleman Ibrahim

Prof Ali Pate

Prof Joseph Usev

Abubakar Kyari

John Enoh

Sani Abubakar Danladi

Source: BBC