A ranar Juma'a ne za a binne tsohon shugaban Tanzania John Magufuli a mahaifarsa da ke Chato a arewa maso yammacin Tnazania.
Za a yi taron add'uoi kafin a binne gawar marigayin inda shugabar kasa Samia Suluhu Hassan za ta jagoranci al'ummar kasar.
Marigayin ya mutu ne a ranar 17 ga watan Maris yana da shekara 61 a duniya .
Mahukunta sun kuma ce ya mutu ne sanadin ciwon zuciya.
An yi masa taron addu'oi a farkon makon nan a Dodoma, babban birnin kasar kuma tun bayan wannan lokaci ake rangadin bankwana da gawarsa a sassan kasar.
Gwamnati ta ayyana zaman makoki na kwanaki 21 domin alhinin mutuwarsa kuma ta dakatar da duk wasu ayyuka na gwamnati.