Menu

Yawan ƴan Najeriyar da suka koma Birtaniya tare da iyalansu

44427199 Hoton alama

Thu, 13 Oct 2022 Source: BBC

Bayanai sun nuna cewa yawan ƴan Najeriyar da suka koma Birtaniya tare da iyalansu ya fi na sauran ƙasashe a shekarar ɗayan da ta gabata. An yi ƙiyasin ne bisa la'akari da tafiyar masu ƙaro ilimi zuwa Birtaniya ta hanyar samun bizar aiki da karatu ta kasar. Gwamnatin Birtaniya ta gano hakan ne bayan da alƙaluma suka nuna yadda ake shiga Birtaniya a wata 12 ɗin da suka gabata. Rahoton ya nuna cewa Indiya ce ta fi yawan ɗaliban da suka shiga Birtaniya, sai China mai mutum 114,837 da iyalai 401 kawai. Ɗaliban Najeriya da suka samu gurbin karatu a Birtaniya sun kai 34,000, amma sun shiga da iyalansu har 31,898. Rahoton gwamnatin Birtaniya Sharhi daga Ma'aikatar Harkokin Waje ya nuna cewa ƴan Najeriya ne suka haɗa kashi 40 cikin 100 na dukkan iyalan ɗaliban da suka shiga Birtaniyan daga bara har zuwa watan Yunin 2022. Haka kuma ɗaliban Najeriyar su ne kashi 7 cikin 100 na dukkan ɗaliban da suka shiga ƙasar daga faɗin duniya a cikin wannan tsakanin. Hakan na ƙunshe ne a cikin rahoton da ma'aikatar ke fitarwa duk bayan wata uku. "Daga bara zuwa watan Yunin 2022, mun bai wa mutum 486,868 bizar karatu, daga su har iyalansu, inda yawansu ya fi na shekarar 2019 da kashi 71 cikin 100." "Waɗanda muka bai wa bizar karatu daga bara zuwan watan Yunin 2022 shi ne mafi yawa a shekarun baya-bayan nan. Wannan shi ne lokacin da aka fi bai wa mutane bizar karatu mafi yawa daga bara zuwa watan Yunin 2022. "Mun bai wa Indiyawa 117,965 biza daga bara zuwa Yunin 2022 inda yawan ya ƙaru da mutum 80,569 (wato da kashi 215%) idan aka kwatanta da 2019.“ Ɗaliban China su ne na biyu da ak fi bai wa biza a tsakanin, inda aka bai wa mutum 115,056.“ A cikin sauran ƙasashe biyar ɗin da ke gaba-gaba, ƴan Najeriya da aka bai wa biza sun ƙaru da mutum 57,545 (wato da kashi 686%) idan aka kwatanta da na 2019. Abin da zai faru a gaba Sakatariyar ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar Suella Braverman ce ta gabatar da wannan rahoto a yayin da take magana a kan dokokin cirani na Birtaniya. Babu tabbas kan abin da gwamnati za ta yi da wannan rahoto amma labarai da ke fitowa na cewa tana shirin gabatar da wasu sabbin matakai na tsaurara bayar da biza. Baun tsaurara bayar da bizar zai shafi ɗaliban da ke neman gurbin karatu ne da ke son komawa da iyalansu. Yayin barin ƙasa Ƴan Najeriya da dama ne ke barin ƙasar - duk da dai ba sabon abu ba ne amma yawan masu tafiyar na ƙaruwa. Dalilai da yawa ke sa mutane ke barin ƙasar. Wasu neman ilimi suke tafiya wasu kuwa neman kyakkyawar rayuwa ke fitar da su. Wasu kuma rashin tsaron da ƙasarsu ke fama da ita ne ke korar su. Yawancin ƴan Najeriya sun fi komawa Birtaniya da Amurka da Canada da Australia da New Zealand da wasu ƙasashen na Turai. Wasu na barin aikinsu su sayar da ƙadarorinsu ko ma su ari kuɗi duk don barin Najeriya. "Tattalin arziki ya taɓarɓare ga wahalhalun da mutane ke sha da gazawar gwamnati sun sa sun fitar da tsammani da ƙasar," in ji Aisha Yesufu, wata mai rajin kare hakkin ɗan adam, kamar yadda ta shaida wa BBC. Amma a wasu lokutan tafiyar ba ta zuwar wa wasu da sa'a. Wani binciken BBC ya gano yadda wani kamfanin lafiya a Birtaniya ke ɗaukar ma'aikata daga Najeriya don yin aiki a asibitoci masu zaman kansu cikin yanayin da hukumar lafiyar ƙasar ba ta amince da su ba. Likitocin da ake ɗauka aikin daga matalautan ƙasashe na ƙorafi kan yadda ake ci da guminsu. Abin da ya sa ƴan Najeriya ke yin ‘japa’ 'Japa', kalma ce ta Yarbacin da ke nufin 'tserewa.' Kalmar a yanzu ta zama ruwan dare a tsakanin matasan Najeriya da suka gaji da halin da ake ciki a ƙasar. Yesufu ta ce da gaske ne mutane na barin Najeriya ne don neman rayuwa mai kyau, suna kuma taimaka wa tattalin arzikin ƙasashen da suke komawa ɗin. Mutane da dama na barin Najeriya saboda dalilai kamar; Sai dai mai rajin kare hakkin dan adam din ta ɗora alhakin hakan a kan ƙasashen da ke ƙarfafa cin hanci a Najeriya, abin da ya jawo rashin shugabanci na gari. "Duk waɗannan ƙasashen da ke barin ƴan siyasa suna kai kudin sata su ɓoye a can na ƙara munanan lamarin. Idan da ƙasashen ba sa ƙarfafa wa cin hancin da Najeriya ba ta lalace haka ba." Ba ma buƙatar tallafin kuɗi daga kowace ƙasa. "Abin da muke so shi ne kawai su daina karɓar kuɗaden satar da ak fita da su daga Najeriya suna ɓoyewa."

Source: BBC