Menu

Yaya ƴan Najeriya suka karɓi shirin rage raɗaɗi na Tinubu?

50260094 Bola Ahmed Tinubu

Tue, 1 Aug 2023 Source: BBC

Ƴan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan shirin rage raɗaɗi na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƴan ƙasar da dama dai sun shiga cikin matsin rayuwa sakamakon janye tallafin man fetur da Shugaba Tinubu ya sanar a lokacin da yake karɓi rantsuwar kama aiki ƙarshen watan Mayu.

Baya ga cire tallafin man fetur, wani abu kuma da ya ƙara jefa ƴan Najeriya ƙuncin rayuwa shi ne na karyewar darajar naira.

A cikin jawabin talbijin da ya gabatar wa 'yan ƙasar ranar Litinin, Tinubu ya ce yana sane da halin tsadar rayuwa da ƴan ƙasar ke ciki, inda ya ce matakan da ya ɗauka su ne suka fi sauƙi, kuma da a ce akwai waɗanda suka fi su sauƙi, to da su zai ɗauka.

Cikin alƙawurran da Tinubu ya yi wa ƴan Najeriya na rage raɗaɗi a jawabinsa, sun haɗa da ƙara wa ma'aikata albashi da samar da aikin yi ta hanyar bai wa kamfanoni guda 75 rancen kuɗi naira biliyan ɗaya kowannensu a cikin wata tara.

Sauran alƙawurran akwai rabawa iyalai a jihohi 36 na fadin ƙasar tare da Abuja tan 200,000 na hatsi da kuma takin zamani da samar da motocin bas masu amfani da makamashin gas da kuma kashe biliyoyin kuɗi wajen noman shinkafa da masara da alkama da kuma rogo har kadada 400,000.

Tinubu ya ce daga lokacin da aka cire tallafin man fetur zuwa yanzu, gwamnati ta tara kuɗin da ya kai naira tiriliyan ɗaya a asusu.

Sai dai duk da irin ƙoƙari da kuma ɗaukar matakai da za su sauƙaƙa wa ƴan Najeriya da shugaban ya ce yana yi, ƙungiyar kwadagon ƙasar ta sha alwashin shiga zanga-zanga ta ƙasa baki-ɗaya a ranar Laraba.

Kungiyar ta ce cire tallafin man fetur da gwamnati ta yi, gallazawa mutane ne wanda kuma ba za ta lamunta ba.

Shugabannin ƙungiyar ƙwadago sun ce babu gudu ba ja da baya a wannan karo wajen shiga yajin aikin duk da yake a baya sun janye shi.

BBC ta duba abubuwan da 'yan Najeriya ke cewa game da irin matakan rage raɗaɗi da Shugaba Tinubu ya yi alƙawari.

Wani mai suna Akpevwe Clement ya yi tsokaci a shafin Facebook inda yake cewa "Najeriya na da manyan matsaloli guda biyu waɗanda su ya kamata a magance.

"Gwamnati ta gyara matatun man fetur, su dawo aiki yadda ya kamata, sannan na biyu kuma a shawo kan matsalar wutar lantarki, saboda tattalin arziki ba zai bunƙasa ba sai da wadataccen lantarki."



Shi ma a tsokacinsa kan jawabin da Shugaba Tinubu ya yi ranar Litinin, Sanata Shehu Sani ya yi bayani mai cike da raha inda ya kwatanta jawabin Tinubu da na magabacinsa Muhammadu Buhari.

Ya ce "Idan ka saurari jawabin Buhari, za ka buƙaci kofin shayi da zai sanya ka wartsake. Amma idan ka saurari jawabin Tinubu, za ka buƙaci fanka domin ka sha iska".

Source: BBC