BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Yaya dambarwar siyasa za ta wanye kan shugabancin majalisa ta 10 a Najeriya?

Yan takarar zama sabon shugaban majalisa

Tue, 25 Apr 2023 Source: BBC

Bayan kammala babban zaɓen Najeriya, ana iya cewa duk mazaɓun ƙasar zuwa yanzu sun san ‘yan siyasar da suka zaɓa su wakilce su. Kama daga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa har zuwa gwamnoni da ‘yan majalisun tarayya da na jihohi.

Wani muhimmin ɓangare na shugabancin ƙasar na gaba da ‘yan Najeriya ba su sani ba zuwa yanzu, kwana 34 a rantsar da Bola Ahmed Tinubu a kan karagar mulki shi ne, ɗan ƙasa na uku mafi girman muƙami da kuma na huɗu da zai yi aiki da su.

Shugabannin da za su jagoranci majalisun dokoki na tarayyar Najeriya biyu, don yin aiki da ɓangaren zartarwa.

Ana ganin cewa al’amarin, yana cikin muhimman batutuwan da zaɓaɓɓen shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyarsa ta APC za su mayar da hankali a kai, bayan dawowarsa daga hutun mako biyar da ya yi a birnin Paris.

Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu ya shaida wa BBC cewa tuni suka bayyana wa ‘yan majalisar tarayyar cewa su dakata.

“A dakata, shuwagabannin nan na jam’iyya, da shi wanda ya ci zaɓe(n shugaban ƙasa) a ba da dama. Su samu matsaya a kan me za a bai wa kowacce shiyya ta ƙasar nan. A yi haƙuri”.

Sai dai ga alama, ba lallai ne masu neman shugabancin majalisun tarayyar sun shirya yin haƙurin da APC take so su yi ba.

Su wane ne ke neman shugabancin majalisa ta 10?

Masu neman shugabancin majalisun tarayyar ƙasar sun fito ne daga dukkan ɓangarorin Najeriya na kudu da arewa, kuma akwai wakilcin manyan addinai guda biyu da ƙasar take martabawa.

Wannan, wani lamari ne, mai sarƙaƙiya da ɗaure kai ganin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar da mataimakinsa suna wakiltar addini ɗaya ne, wato Musulunci.

Hakan ya saɓa da abin da siyasar Najeriya ta saba gani a baya, inda shugaba yakan fito daga sashen addini daban da na mataimakinsa.

Ga alama, wannan na iya tsananta dambarwa da kai ruwa rana wajen fitar da shugabannin da za su ja ragamar sabuwar majalisa ta goma.

A bisa al’ada kuma, batun shugabancin majalisun tarayya shi ne ya fi tada ƙura a siyasance, bayan kammala zaɓuka.

Kuma a mafi yawan lokuta, irin shugabannin da aka zaɓa, su ne za su nuna salon yadda dangantaka za ta kasance tsakanin ɓangaren zartarwa da masu yin doka.

A baya, an ga yadda dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnatin Jonathan da majalisar wakilai lokacin da 'yan majalisar suka yi gaban kansu wajen zaɓar Aminu Waziri Tambuwal don ya jagorance su.

Haka kuma an ga irin waccan takun-saƙa tsakanin ɓangaren zartarwa a wa’adin mulkin Shugaba Buhari na farko da majalisar dattijai, lokacin da sanatoci suka yi watsi da umarnin jam’iyyar APC suka zaɓi Bukola Saraki a matsayin shugabansu.

Sai dai a wannan karo ana ganin lamarin na iya ƙara zafi saboda ban da batun ɓangare, addini ma ya shigo ciki.

Ko da yake, wasu masu neman shugabancin, na ganin addini ko ɓangare, ba su kamaci zama abubuwan la'akari wajen zaɓar mutum na uku da na huɗu mafi girman muƙamai a Najeriya ba.

Ko ba komai "majalisa, gashin kanta take ci"!

Haka zalika, samun shugaban majalisa daga addini ɗaya da shugaban ƙasa a Najeriya, in ji su, ai ba wannan karo ne, farau ba.

Majalisar Dattijai

Sanata Abdulaziz Yari

Ɗan majalisar dattijai ne mai wakiltar Zamfara ta Yamma daga Arewa maso Yamma.

Ya taɓa zama shugaban ƙungiyar gwamnoni, kuma ya yi gwamnan jihar Zamfara wa'adi biyu. Ya ci zaɓen ɗan majalisar dattijai a shekara ta 2019, amma daga bisani kotu ta rushe zaɓukan jam'iyyarsa ta APC a jihar da ya fito, ciki har da kujerarsa.

A wani bidiyo da aka wallafa a shafin sada zumunta ranar 26 ga watan Maris, an ga Abdulaziz Yari lokacin wani jawabi ga 'ya'yan jam'iyyarsa ta APC, yana bayyana aniyarsa ta takarar shugaban majalisar dattijai.

Yari ya ce "Na yi imani, shiyyata ta yanke shawarar ta ba ni goyon baya, ba za su goyi bayan mutumin da bai dace ba.

Na yi imani sun san ƙwazona tun daga shugaban jam'iyya, zuwa ɗan majalisar wakilai har kasancewata gwamna”.

Sanata Ali Ndume

Sanata Ali Mohammed Ndume, ɗan majalisar dattijai ne mai wakiltar mazaɓar Borno ta Kudu. Kuma karo na huɗu kenan yana cin zaɓe don wakiltar al'ummar wannan yanki a majalisar dattijai.

Ya fito ne jiha ɗaya da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa Kashim Shettima.

Ya ce daga cikin dalilansa na fitowa neman kujerar mutum na uku mafi girman muƙami a Najeriya, akwai batun cewar mutane ne suka ba shi shawarar ya nema, kamar yadda ya shaida wa BBC.

"Na ɗaya, ina ɗaya daga cikin wa'yanda suka fi daɗewa a majalisar. Ga kuma cancantar da suke gani (ina da ita)," in ji shi.

Ali Ndume ya ce kasancewar ya fito jiha ɗaya da zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, ba wani shamaki ba ne, da zai hana shi wannan dama.

"Ai ba yau aka fara irin wannan abin ba," in ji shi. "A wani lokaci, an yi mataimakin shugaban ƙasa daga Northwest Namadi Sambo, kuma an yi Tambuwal a zaman kakakin majalisa".

Sanata Barau Jibril

Sanata Barau Ibrahim Jibrin, ɗan majalisar dattijai ne da ke wakiltar Kano ta Arewa.

Shi ne shugaban kwamitin kasafin kuɗi a majalisa ta tara. Yana da'awar shi ne ya fi cancantar zama shugaban majalisar dattijai ta goma da za a rantsar nan gaba a cikin watan Yuni, saboda ɗumbin ƙwarewar da yake da ita.

Karo na uku kenan yana wakiltar mazaɓar ɗan majalisar dattijai ta Kano ta Arewa.

Sanata Jibrin ya kuma ce kasancewar shiyyar da ya fito ta arewa maso yamma, ita ce ta fi bai wa jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya, ƙuri'u masu yawan da suka sanya ta nasarar da ta samu a zaɓen watan Fabrairu da na Maris, ba shi muƙamin tamkar yaba kyauta da tukwici ne ga al'ummar shiyyar.

Game da iƙirarin cewa kujerar da yake nema a yanzu ta fi dacewa, da mai bin tafarkin addinin Kirista, kasancewar Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima, duka musulmai ne, ya ce babu irin wannan tsari a majalisa.

"Kaman yadda na faɗa ƙwarewa ce. Wanda ya fi ƙwarewa, ya fi daɗewa, shi ne ake bai wa shugabanci".

Ya yi iƙirarin cewa a lokacin mulkin Goodluck Jonathan, mai bin addinin Kirista, an yi shugaban majalisar dattijai, Sanata David Mark, Kirista. "Hatta mataimakinsa Ike Ekwerenmadu, Kirista ne", in ji Barau.

Haka zalika, ya ce ko a majalisar wakilai Patricia Etteh ta yi shugabanci, duk da yake ita ma Kirista ce.

Sanata David Nweze Umahi

A watan Yuni, Sanata Dave Nweze Umahi zai ɗare kujerar ɗan majalisar dattijai mai wakiltar mazaɓar Ebonyi ta Kudu.

A ranar 22 ga watan Maris 2023 ne ya bayyana aniyarsa ta neman shugabancin majalisar dattijai ta goma a birnin Abakaliki.

Gwamnan wanda ke kammala wa'adin mulkinsa na biyu ranar 29 ga watan gobe ya yi kira ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyarsa ta APC, su yi tunanin kai muƙamin shugaban majalisar dattijai zuwa shiyyar Kudu maso Gabas.

David Umahi ya ce kai muƙamin shiyyar Kudu maso Gabas da kuma kai shugabancin majalisar wakilai zuwa Arewa maso Gabas, zai tabbatar da rabon gaskiya da adalci da kuma daidaito.

A cewarsa kuma hakan mataki ne da zai taimaka wajen haƙurƙurtar da masu tada jijiyoyin wuya a Najeriya.

Sanata Godswill Obot Akpabio

Sanata Godswill Obot Akpabio da ke wakiltar mazaɓar Akwa Ibom ta Arewa maso Yamma, ɗan majalisar dattijai ne karo na biyu.

Ya riƙe muƙamin shugaban marasa rinjaye a shekara ta 2015, ƙarƙashin jam'iyyar PDP. Ya yi gwamna wa'adi biyu, kuma ya riƙe muƙamin ministan Neja Delta.

Sanata Akpabio yana wakiltar shiyyar Kudu maso Kudu.

Masu rajin bai wa mutumin kudancin Najeriya muƙamin kujera ta uku mafi girma, na ganin bai wa ɗan siyasa kamar Godswill Obot Akpabio matsayin shugaban majalisar dattijai, shi ne zai tabbatar da adalci da manufar raba daidai ga muƙaman siyasa na Najeriya a gwamnatin da za a kafa.

A farkon wannan wata ma, ya fitar da wata sanarwa inda yake musanta raɗe-raɗin cewa ya janye aniyarsa. Ya sake tabbatar da cewa har yanzu yana nema.

Sanata Orji Uzor Kalu

Sanata Orji Uzor Kalu, ɗan majalisar dattijai ne mai wakiltar mazaɓar Abiya ta Arewa. A yanzu haka, yana riƙe da muƙamin Mai Tsawatarwa a Majalisar Dattijai ta tara.

Tsohon gwamna ne a jihar Abiya, karo na biyu kenan kuma da yake wakiltar al'ummarsa a majalisa daga shiyyar Kudu maso Gabas.

Masu rajin bai wa Orji Uzor Kalu muƙamin shugabancin majalisar dattijai na cewa yin hakan zai tabbatar da saka kowacce ƙwarya a gurbinta.

Ganin zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bayarabe ne daga Kudu maso Yamma, mataimakinsa kuma Kanuri daga Arewa maso Gabas, Uzor Kalu zai tabbatar da wakilcin manyan ƙabilun ƙasar uku ta hanyar ba shi muƙamin a matsayin ɗan ƙabilar Igbo.

A wata hira da manema labarai da ya yi a baya-bayan nan, Uzor Kalu ya ce “Zan so jam'iyyarmu ta kai wannan kujera, zuwa shiyyarmu, kai ƙauyenmu na Igbere ma, saboda zaɓaɓɓen shugaban Najeriya yana buƙatar mutane masu nagarta da za su farfaɗo da tattalin arziƙi,.

Su yi aiki don bunƙasa rayuwar talakawa kuma su yi dokokin da za su ba shi damar bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa".

Sanata Osita B. Izunasu

Sanata Osita Izunasu, zaɓaɓɓen ɗan majalisar dattijai ne mai wakiltar Imo ta Yamma. Amma ba karon farko kenan da yake zuwa majalisar ba, don kuwa ya taɓa wakiltar al'ummar mazaɓarsa bayan zaɓen 2007.

Masu goyon bayan Izunasu a matsayin shugaban majalisar dattijai ta goma, sun ce yana da ingantaccen ilmi da kuma gogewar yin doka. Suna dai fatan jam'iyyar APC za ta kai shugabancin majalisar dattijai zuwa Kudu maso Gabas saboda a cewarsu shiyyar ce mafi koma-baya tun bayan samun 'yancin kan Najeriya a 1960

Suna iƙirarin cewa kasancewar zaɓaɓɓen shugaban ƙasar Bayarabe Musulmi da kuma shugaban ɓangaren shari'a shi ma Bayarabe Musulmi, samun wani ɗan kishin ƙasa daga al'ummar Igbo kuma Kirista, ita ce masalaha ga Najeriya.

Majalisar Wakilai

Majiyoyi sun ruwaito Shugaban Majalisar Wakilai yayin taron da ya kira masu neman kujerar da yake kai nan gaba a majalisa ta goma, yana shaida musu buƙatar su haɗa kai da nema cikin kwanciyar hankali.

Rahotanni sun kuma ce ya musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa yana mara baya ga ga wani a cikinsu.

Zaman dai na ranar 7 ga watan Afrilu ya samu halartar Idris Wase da Makki Yalleman da Yusuf Gagdi da Benjamin Kalu da Muktar Aliyu Betara da Sada Soli Jibia da Abdurrahman Tunji Olawuyi da Abbas Tajudeen da kuma Aminu Sani Jaji.

Rahotanni sun ce Gbajabiamila ya kira taron ne bayan wani makamancinsa da gamayyar jam'iyyun adawa ƙarƙashin jagorancin PDP suka yi ranar Talata 4 ga wannan wata.

An jiyo taron 'yan majalisar wakilan daga jam'iyyu marasa rinjaye shida na cewa sun taru ne don ƙulla ƙawance da musayar ra'ayoyi da sanin juna kafin buɗe majalisa ta goma.

A APC mai mulki, ƙarin 'yan majalisar wakilan da ke neman shugabanci sun haɗar da Alhassan Ado-Doguwa da Olaide Akinremi.

Shiyyoyin masu neman shugabancin majalisar wakilai ta 10

Arewa maso Yamma

Abbas Tajuddeen - Zariya

Makki Abubakar Yalleman - Mallam Madori/Kaugawa

Alhassan Ado Doguwa - Tudun wada/Doguwa

Aminu Sani Jaji - Ƙauran Namoda/Birnin Magaji

Sada Soli Jibiya - Kaita/Jibiya

Abbas

Arewa ta Tsakiya

Ahmed Idris Wase - Wase

Tunji Olawuyi - Ekiti/Irepodun/Isin/and Oke-Ero

Yusuf Gagdi - Pankshin/Kanke/Kanam

Kudu maso Gabas

Benjami Kalu - Bende

Princess Miriam Onuoha - Onuimo/Isiala Mbano/Okigwe

Arewa maso Gabas

Kudu maso Yamma

Wasu masharhanta dai na cewa yanzu babban aiki, ya rage wa jam'iyyar APC mai mulki ganin ko za ta raba muƙaman shugabancin Majalisun Tarayya zuwa sauran shiyyoyin Najeriya – Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya da Kudu maso Kudu da kuma Kudu maso Gabas, waɗanda zuwa yanzu suke can riƙe da ƙoƙo suna dakon rabo ya zo kansu.

An yi riga mallam masallaci - APC

Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Sanata Abdullahi Adamu dai ya ce rige-rigen neman muƙaman shugabancin majalisun tarayyar ba komai ba ne face 'riga mallam masallaci' ga 'ya'yan jam'iyyar.

Ya ce matakin na iya kawowa jam'iyyar ɓaraka a daidai lokacin da take buƙatar haɗin kai da cikakken goyon baya.

Sanata Abdullahi Adamu ya ce kamata ya yi a bar shugabannin jam'iyya su cimma matsaya kan shiyyoyin Najeriya da za a bai wa muƙaman, saboda tabbatar da adalci da daidaito.

APC na kan siratsi - Masharhanta

Masu sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya kamar Dakta Abubakar Kari na ganin cewa yadda jam'iyyar APC mai mulki za ta wanye game da rabon muƙamai a shugabancin majalisa ta goma, wani babban ƙalubale ne da ya jefa jam'iyyar kan siratsi.

"Akwai babban batu wanda dole ne ta samo bakin zaren game da shi", in ji masanin kimiyyar siyasar.

Batun daidaito tsakanin kudu da arewa da kuma daidaito tsakanin Musulmai da Kirista, muhimman batutuwa ne wajen raba muƙaman siyasa a Najeriya, ya ƙara da cewa.

A cewarsa, wani babban ƙalubale kuma shi ne Majalisar Wakilai yanzu kusan kankankan ake yi tsakanin jam'iyyar mai mulki da kuma jam'iyyun adawa, idan sun dunƙule.

"Don haka ko da APC ta fito da tsarinta na daidaito, 'yan adawa suna iya yi masa barazana, ko ma suna iya lalata shi ƙwarai da gaske," Dr. Kari ya ce.

Masanin ya ce wannan gwagwarmayar neman madafun iko, a iya cewa wata babbar gasa ce wadda yanzu ma aka fara.

"Akwai sauran kallo ƙwarai da gaske".

Source: BBC