Menu

Za a kai ɗan shugaban Amurka kotu a kan mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba

Joe And Hunter Biden Hunter Biden (hagu) ɗan gidan Shugaban Amurka Joe Biden da ubansa

Thu, 22 Jun 2023 Source: BBC

Ana sa rai Hunter Biden ɗan gidan Shugaban Amurka Joe Biden zai amsa laifi a kan aikata ba daidai ba game da biyan haraji kuma zai amsa cewa ya mallaki wata bindiga ba bisa ƙa'ida ba lokacin da yake shaye-shayen ƙwaya.

Matakin na zuwa ne bayan wani bincike na tsawon shekara biyar.

Babban lauyan Amurka a Delaware ne ya gabatar da takardun bahasin da ke nuna wannan yarjejeniya da aka cimma.

Ana sa ran Hunter zai amince cewa an yi masa magani saboda matsalar shan ƙwayar da ya yi fama da ita, kuma hukumomi sun sa ido a kansa.

Mai yiwuwa ne sharuɗɗan yarjejeniyar za su ba shi damar kuɓuta daga ɗauri a gidan yari.

A kan takarda, zai iya fuskantar hukuncin ɗauri mafi tsanani na tsawon shekara ɗaya a gidan yari a kan kowacce daga cikin tuhume-tuhumen da harajin da aka yi masa da kuma ɗaurin shekara goma a gidan yari a kan tuhumar mallakar bindiga ba bisa ƙa'ida ba, in ji wata sanarwa daga ma'aikatar shari'a.

Akwai buƙatar alƙalin da ke sauraron shari'ar kuma zai yanke hukunci, sai ya amince da yarjejeniyar da aka cimma.

Ba a fayyace ƙarara ba ranar da Hunter Biden zai bayyana a kotu don amsa laifi a kan tuhume-tuhumen haraji.

Zai amsa laifi kan mallakar bindiga a wani ɓangare na "yarjejeniyar madadin shari'a" wadda ita daban ce da bahasin da ya amsa. lauyan Mista Hunter ya faɗa a cikin wata sanarwa.

"Na san cewa Hunter ya yi imani abu ne mai muhimmanci ya ɗauki alhakin waɗannan kura-kurai da ya yi a lokacin gada-gada da jarabar shaye-shaye na rayuwarsa," Mista Clark ya ƙara da cewa.

"Yana zuba ido don ganin ya ci gaba da sake gina rayuwa da kuma fuskantar gaba."

Hunter Biden, ɗan shekara 53, ya taɓa aiki a matsayin lauya a shekarun baya da kuma jami'in kamun ƙafa ciki har da a ƙasashen waje kamar China da Ukraine.

An kore shi daga Rundunar Sojin Ruwan Amurka a 2014 bayan gwaji ya nuna yana ta'ammali da kokino.

Yarjejeniyar amsa laifin ta kawo ƙarshen wani bincike da ma'aikatar shari'ar Amurka ta shafe tsawon lokaci tana gudanarwa a kan ko Hunter Biden ya ba da cikakken rahoton kuɗin shigarsa da kuma ko ya ba da bayanan ƙarya a takardun da ya yi amfani da su wajen sayen wata bindiga a 2018.

Tuhume-tuhumen harajin na da alaƙa da gazawar sa wajen biyan harajin sama da $100,000 a shekara ta 2017 da kuma a shekara ta 2018

Source: BBC