Katafaren filin wasan Brazil mai suna Maracana zai koma amsa sunan Pele, domin martaba shi.
Wannan mataki ya biyo bayan da 'yan majalissar Rio de Janeiro suka kada kuri'ar amincewa da sauya sunan filin zuwa Edson Arantes do Nascimento - Rei Pele.
Edson Arantes do Nascimento cikakken sunan zakakurin dan wasan Brazil kennan mai shekara 80, yayin da Rei a harshen Portugal ke nufin sarki.
Sai dai kafin a sauya sunan sai gwamnatin Rio de Janeiro ta amince da wannan bukatar kafin a tabbatar.
Pele ya lashe kofin duniya uku a tawagar Brazil ya kuma ci kwallo na 1,000 a filin Maracana a 1969 a lokacin da ya buga wa Santos karawa da Vasco da Gama.
Filin wasa na Maracana ya karbi bakuncin gasar kofin duniya a 1950 da kuma 2014 da bikin wasannin Olympic a 2016.
Sama da mutum 200,000 suka kalli wasan da Uruguay ta doke Brazil ta lashe kofin duniya a 1950 a Maracana, koda yake yanzu filin yana daukar 'yan kallo 78,838.
Tun farko an bai wa filin sunan Mario Filho, wani dan jarida da ya yi ta rokon da aka gina filin a 1940, daga baya ake kiran filin da Maracana, wato wurin da aka yi ginin.