BBC

News

Sports

Business

Entertainment

GhanaWeb TV

Africa

Opinions

Country

Za a yi karon batta tsakanin United da Brighton a Premier

Hoton alama

Thu, 14 Sep 2023 Source: BBC

Manchester United za ta karbi bakuncin Brighton a wasan mako na biyar ranar Asabar a Old Trafford.

United wadda ta ci wasa biyu mai maki shida tana ta 11 a teburin Premier League bayan wasa hudu, Brighton kuwa wadda ta ci karawa uku da maki tara tana ta shida.

Watakila United ta rasa 'yan wasa 10 da za su buga mata karawar, ciki har da sabon dan kwallon da ta dauka aro a bana, Sofyan Amrabat, wanda ke fama da ciwon baya.

Haka ma watakila Lisandro Martinez ba zai buga fafatawar ba, wanda ya ji rauni a wasan da Arsenal ta ci United 3-1 a Premier League a Emirates.

Haka kuma kila duk da daukar aron Sergio Reguilon daga Tottenham, Diogo Dalot zai yi tsaron baya daga gefen hagu a madadin Luke Shaw.

Antony yana Brazil, wanda ke kokarin kashe gobarar dake gabansa, bayan da ake zarginsa da cin zarafin mata biyu, ciki har da tsohuwwar budurwarsa.

Ana sa ran za a fara wasan da wanda United ta dauka a bana Rasmus Hojlund a karon farko, wanda ya shiga sauyi a karawa da Arsenal.

A bangaren Brighton kuwa Julio Enciso zai ci gaba da yin jinya, wanda ya dade baya buga tamaula.

Haka shima Jakub Moder da kyar idan zai buga wasan, bayan da yake jinya.

Za kuma a ci gaba da auna koshin lafiyar Evan Ferguson da kuma Danny Welbeck ko za su iya buga gumurzun.

Watakila Ansu Fati ya fara bugawa Brighton wasan Premier a gidan United, wanda ta dauko aronsa daga Barcelona a bana.

Wasa uku da suka buga a 2022/2023

Premier League Alhamis 4 ga watan Mayun 2023



  • Brighton 1 - 0 Man Utd


FA CUP Lahadi 23 ga watan Afirilun 2023

  • Brighton 0 - 0 Man Utd


Premier League Lahadi 7 ga watan Agustan 2022



  • Man Utd 1 - 2 Brighton


Abin da ya kamata ku sani kan wasa tsakanin kungiyoyin biyu:

Manchester United ta dan fara kakar bana da tunbube, bayan da Arsenal ta doke ta 3-1 a wasan mako na hudu duk da ita ce ta fara cin kwallo.

Ita kuwa Brighton, wadda West Ham ta doke ta har gida a fafatawar mako na uku ta ci Newcastle 3-1 a wasan mako na hudu a Premier League.

Kungiyar Brighton ce kan gaba a yawan zura kwallaye a raga, wadda ta ci 12, sai Manchester City da Tottenham da kowacce ta ci 11.

Brighton ta ci wasa uku baya a Premier League da ta fuskanci Manchester United.

Wasannin mako na biyar:

Ranar Asabar 16 ga watan Satumba



  • Wolverhampton da Liverpool
  • Aston Villa da Crystal Palace
  • FC Fulham da Luton Town
  • Manchester United da Brighton
  • Tottenham da Sheffield United
  • West Ham United da Manchester City
  • Newcastle United da Brentford


Ranar Lahadi 17 ga watan Satumba



  • Bournemouth da Chelsea
  • Everton da Arsenal
Ranar Litinin 18 ga watan Satumba



  • Nottingham Forest da Burnley


Source: BBC